ALKALI NE Page 21 to 30

Adebayo yace Yanzu wannan motar kad’ai ta rage mani acikin kud’in da aka bamu na sallama, kason Mr. Kallah dana Brr. Barau sunfi yawa gashinan har yanzu suna cin abunsu.
Umar yace baka san kason wanda yake da yawa ba, Mr. Kallah da Brr. Barau ba sune masu kaso mai yawa ba, Babban Yallab’ai nashi yafi nasu yawa ai, domin kasan shi baya wahala amma ana bashi kasonshi a duk lokacin da akayi irin wannan harkar. Adebayo yace wai Alhaji Marusa kake nufi? Umar yace bashi ba, wannan ai shine Oga kwata-kwata, babban Yallab’ai nake nufi.
Dariya Adebayo yayi yana fad’in wallayi Umar baka da kyau, har na manta dashi ai, kasan shi baya son asan dashi sai dai yaji kud’i kawai. Umar yace gaskiya muje mu samu Alhaji Marusa ya k’ara mana wani abu asusuna yayi k’asa, kaga dai yanzu bama samun cin hanci. Adebayo yace idan aka d’auki kayan kawai muje.
Hannu Alhaji Maiwada yasa yana goge zufar da ta zuba masa,
***
canza wata d’aukar Moses yayi sai ga Adebayo zaune a mota yana waya da Mr. Kallah….
Yallab’ai wallayi Alhaji Marusa ne yace a fad’a maka anjima kayansa zasu iso kuma wannan karon yace rabin kayan ba wanda ya saba kawowa bane, gashi ta bodar mu yace ashigo dasu kuma yau Sir, yana ofis gashi Abubakar ne yake da aiki yau, d’azu yakira baka d’auka ba shine yace idan na sameka na fad’a maka saboda kayan wannan karon masu tsada ne sosai kuma za’a samu riba, shine yace ka d’auke Abubakar daga wajen shida Sir, hakan ne zaisa a tafi da kayan ba tare da an duba ba…. E, yauwa, sauran ma’aikatan nasan basu da matsala. Toshikenan mun gode.
Murmushin takaici Alhaji Maiwada yayi domin ya tuna ranar da Mr. Kallah yayi masa waya akan suje Abuja shida Abubakar akwai abinda zasuyi, ashe dama wannan harkar zasuyi. Runtse ido yayi yana jin takaici da kayan suka samu wucewa, ya tabbata yanzu sun gama rabar dasu ga dilolinsu.
***
‘Dayan d’aukar Moses ya kunna wadda take a gidan Alhaji Marusa. Fitowar farko Alhaji Marusa ne da Brr. Barau, Mr. Kallah sai wani babban mutum wanda ya juya baya ba’a ganin fuskarsa. Zaune suke a saman kujeru gabansu cike da kayan motsa baki.
Yanda yaga suna nutsuwa suna nuna ladabi ga wannan babban mutumin ya tabbatar masa koma waye mai babban matsayi ne.
Muryar Alhaji Marusa sukaji yana fad’in Brr. Ina kara maka godiya akan kok’arin da kayi mana a wancan karon na shari’ata da Alhaji Maiwada, wannan karon ma akwai wata shari’a nida wani abokin kasuwancina, kayansa na cinye kuma ya biyani, to nawa ne bansan ya akayi suka salwanta ba shine naji bazan iya biyansa kud’insa ba sai kawai nace ai rabin kud’in ya bani yace idan na bashi kaya zai cika mani, shine yanzu yake fad’in zai shigar da k’ara, kuma gaskiya kud’in da yawa, ina dasu kawai bana jin zan iya biyansa shiyasa nake son a juya maganar, domin jiya na bashi rabin kud’in kuma na d’auka lokacin da nake bashi.
Muryar babban mutumin sukaji yana fad’in wannan ba wani abu bane na tada hankali, nasan Brr. Barau zai iya da wannan matsalar kawai ka bar masa komai. Brr. Barau yace Yallab’ai duk abinda kace angama ai.
Mr. Kallah yace Alhaji Marusa baka da kyau akan kud’i. Alhaji Marusa yace kud’i ai dole muso su, nifa duk yawan kud’ina banki su linka so goma ba, shiyasa nake so ka d’auke mana wancan jarababben Maiwadan ko harka zata k’ara bud’ewa. Mr. Kallah yace kwantar da hankalin ka k’arshen shekarar nan zan canza masa wajen aiki, gara ya dawo kusa dani kaga hankalin mu zai kwanta. Dariya sukasa gaba d’aya.
***
Wuce wajen Moses yayi, sauran d’aukar duk bata da amfani, wucewa yayi tayi har yazo wani waje, sai kawai sukaga wani babban mutum da ganinsa mai gadin Alhaji Marusa ne, tsaye yake a wajen yana ta dube-dube yana kallon agogon hannunsa wanda suke jin k’arar harbawarsa, da alama wani abu yake nunawa, can kuma sukaji yana fad’in kemera kuma anan? Nasan dai ba Alhaji bane yasata domin da ya sanar dani, hannu sukaga yasa a wajen sai kawai sukaga hoton ya d’auke.
Hannu Moses ya tafa yana fad’in kassh! Wannan banzan ya lalata mana. Zama yayi yana cije baki. Abubakar yace bakomai mun samu abinda muke so, domin ko wannan kad’ai ya ishe mu sheda.
Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad’in kwashe su duka ka had’a mani a (Flash) in tafi dasu akwai abinda nakeso nayi, dole sai ancire abubuwa marasa amfani abar masu amfani kafin mu gabatar dasu, bana so na bar maka kayi aikin kada tsautsayi yasa wani ya gani, amma idan naje dashi gida nasan acan yafi tsaro domin ni kad’ai ne zanyi aikin.
Moses yace yanzu kuwa Sir, nima bana son su zauna a wajena saboda wallayi tsoro nakeji, zan turasu duka sai na goge komai. Dariya Abubakar yayi yana fad’in kai dama ai sarkin tsoro ne.
Kallonsu Alhaji yayi yana fad’in muryar wannan babban mutumin tayi mun kama da ta wani, naso an d’auko fuskarsa domin koma waye babba ne a k’asar nan, lallai duniya babu gaskiya, amma koma waye idan aka mik’asu kotu zasu fad’esa.
Tabbas na tuna shari’ar da Alhaji Marusa yayi da abokin kasuwancinsa har akace shine yayi nasara, ashe dai shine beda gaskiya, lallai Brr. Barau mutumin banza ne, insha Allahu k’arshen su yazo.
Bayan Moses ya gama ya mik’a ma Alhaji sannan ya goge komai, haka suka fito, sallama yayi masu Malan Sani ya tuk’a suka nufi gida, a hanya Alhaji yake bashi labarin abubuwan da suka faru, sosai Malan Sani yayi mamakin abinda Alhaji ya fad’a masa, dama shi yana zargin Mr. Kallah kawai Alhaji ne ya yarda dashi. haka suka nufi gida Malan Sani yana bashi shawara akan abinda ya kamata.
**** ***
A cikin wani d’aki mai duhu aka jefa Malan Hassan, Alhaji Marusa yace ka barsa nan zuwa safiya zamu bincikesa, wannan babban al’amari ne, yanzu zanyi waya dasu Brr. Barau dole suzo asan abunyi domin ina da tabbacin Alhaji Maiwada ne ya aikosa, kuma tabbas ya kalli wannan d’aukar, idan har ya fito da ita ya gama damu, zan iya yin komai domin na kare mutuncin kai na koda ya had’a da wani ya rasa ransa ne.
Rufe k’ofar da Malan Hassan yake ciki akayi da makulli kafin Alhaji Marusa ya wuce ciki hankali atashe yana neman wayar Mr. Kallah.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣4⃣
A daren wannan rana Alhaji Maiwada bai samu bacci ba, sai da ya gyara komai ya had’ashi kamar a lokaci guda akayi komai, bayan daya gama ya b’oye wani a cikin kamfutarsa dan guda biyu yayi saboda tsaro, cire flash d’in yayi wanda shine zai kai a kotu, k’asan gadonshi ya b’oyeshi saboda washe gari juma’a yafiso sai litinin sannan yashigar da k’ara kotu dan Brr. Kamal yakeso gobe ya samu suyi maganar kafin litinin.
**
Malan Hassan kuwa gaba d’aya ya tsure, hankalinsa a tashe yake dan yasan halin Alhaji Marusa, akan dukiyarsa babu abinda bazai iya ba, haka ya zauna yana ta fargabar wayewar safiya dan yana tsoron abinda zai faru, babban tashin hankalinsa Iyalinsa, duk da d’azu yayi masu sallama amma besani ba ko zai koma garesu da rai. Haka yayi ta tunani har barci b’arawo yayi gaba dashi.