ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 21 to 30

***

Kasancewar akwai band’aki a cikin d’akin hakan yasa yashiga yayi alwalar asuba, bayan yayi sallah ya zauna yana ta addu’a. 

K’arar bud’e k’ofa yaji hakan yasa cikinsa ya d’auki k’ara, ga yunwa dama yanaji dan ko abincin dare beci ba. Alhaji Marusa, Brr. Barau, sai wasu majiya k’arfi guda biyu ne suka shigo d’akin. 

Da sauri Malan Hassan yaja da baya yana cira ido, k’ofar suka jawo sannan Alhaji Marusa ya kunna wuta hakan yasa haske ya gauraye d’akin. Waje suka samu shida Brr. Barau suka zauna, sauran mazan kuma suna tsaye sun hard’e hannuwa akirji. 

Brr. Barau ne yace yanzu kai tsoho da kai amma ka iya munafurci, da Lucky be gano abinda kayi ba shikenan a jiya kake tunanin d’auke abinda kasa kaje ka kai masu ko? Lallai tsoho ka kira mutuwar ka, dan wallahi bazamu bari ka tarwatsa tamu rayuwar ba tun lokacin mu beyi ba. 

Cikin rawar murya Malan Hassan yace na roke ku kuyi mani rai, wallahi ina da iyali, basu da kowa sai ni, idan kuka kasheni zasu shiga matsala. 

Alhaji Marusa yace bakasan darajarsu ba shiyasa ka jefa kanka a cikin matsala, mu da kake shirin tona mana asiri ai bamu da Iyali ko? Wallahi kaji na rantse maka ko Matata na samu da irin wannan laifin sai na kasheta, arayuwata bana had’a dukiyata da komai, kana tunanin idan aka mik’amu kotu bazan rasa komai ba? Dan haka inaso ka fad’a mani *WAYE NE*(Tsohon littafina), ya saka wannan aikin? Shiru Malan Hassan yayi jikinsa na rawa. 

Brr. Barau yace Alhaji bamu da lokaci, na tabbata wannan abun da sukasa sun riga sun ganshi a can, domin had’awa akeyi, duk abinda yake faruwa anan zasu ganshi a wajensu, muyi abinda yake gaban mu domin muje garesu tun kafin su fitar dashi domin nasan yanzu suna jiran Malan Hassan ya kai masu wannan su had’a dashi. 

Alhaji Marusa yace Mr. Kallah yana hanya dan munyi waya dashi, kallon Malan Hassan yayi yana fad’in bazaka fad’a ba? Jiki a sanyaye Malan Hassan yace su Abubakar ne da abokinsa Moses, sunyi ne dan su taimaki Alhaji Maiwada, dan Allah kubarni wallahi nayi maku alk’awari zan kwashe Iyalina mu koma garin mu har abada bazan sake dawowa nan ba. 

Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad’in daga baya kenan, kallon Lucky yayi yana fad’in bana son aji labarin gawarsa. Ficewa sukayi shida Brr. Barau. Malan Hassan duk rokon da yake masu sai da suka kashe shi, nad’eshi sukayi suka d’aukeshi zuwa mota suka nufi bayan gari suka binneshi. 

***

Abbun Ra’eez ka tasa abinci kana kallo ka kasa ci, kuma na tambayeka kayi mani shiru, anya babu abinda yake faruwa kuwa? Ajiyar zuciya ya saki yana fad’in Bilkisu dole na bar wannan aikin, dole mubar garin nan ina aje aikina, wallahi aikin Kwastam ya fice mani, nayi danasanin fara yinsa. 

Matsowa tayi tana fad’in haba Abbun Ra’eez ya zaka fad’i haka, tun jiya dama nake ganin ka wani iri, dan Allah ka fad’a mani abinda yake faruwa kila ina da abinda zan taimaka maka dashi. 

Beyi magana ba ya fara cin abincinsa, sai da yaci rabi sannan ya aje, hannunta ya kama suka nufi d’aki. Bayan sun zauna ya kalleta yana fad’in Bilkisu kicigaba da tayani addu’a domin Allah ya fara haska mani wad’an da suke bibiyata da sharri. Murmushi ta saki tana fad’in kai amma naji dad’i, meya faru? Wayarsa ce tayi k’ara hakan yasa yayi shiru ya d’auka. 

Alhaji Mansur ne, bayan sun gaisa yake tambayar Alhaji k’arin bayani akan sakon daya tura masa jiya? Gyara zama Alhaji Maiwada yayi yana fad’in wallahi jiya na gama aiki naji bazan iya kwanciya batare dana fad’a maka abun farin cikin da nake ciki ba…….. 

Labarin komai ya fad’ama Alhaji Mansur Ummu tana gefe tayi tagumi tana jin abun al’ajabi. Bayan ya gama Alhaji Mansur yace Allah mungode maka, lallai Allah shine abin godiya, abinda nakeso da kai kada ka bari wannan maganar ta fita, Malan Sani nasanshi beda matsala, sannan kayi magana da Brr. Kamal zuwa litinin zan biyo jirgi domin ayi komai ina nan, wallahi kaji na rantse bazamu yarda ba sai an bi maka hakkin ka, wannan gidan daya anshe maka sai ya maidoshi, sai a maida masa kud’insa. 

Alhaji yace insha Allahu zanyi yanda kace, Allah ya kaimu litinin d’in. Alhaji yace amin. Sallama sukayi yana fad’in sai ya sake kira. Hannunshi Ummu ta kamo tana fad’in yanzu kam na goyi bayanka akan maganar aje aiki, ana kammala shari’ar nan ka aje masu aikinsu, wannan gidan ma kasayar dashi mu koma Kano da zama, Malan Sani ma nasan zai bimu kawai mutafi dasu bazamu sake waiwayar Lagos ba. 

Murmushi Alhaji yayi yana fad’in insha Allahu aikina yazo k’arshe, abinda na tara ya ishe ni, Allah ya albarkaci abinda zan samu anan gaba. Ummu tace amin. 

**** ****

Zaune suke su Ukku, Brr. Barau, Mr. Kallah da Alhaji Marusa, magana suke akan yanda zasu b’ulloma wannan abun. Alhaji Marusa ne yace abinda nake gani kawai mu kawar da Alhaji Maiwada. Zaro ido Mr. Kallah yayi yana fad’in kasan abinda kake fad’a kuwa? Brr. Barau yace wannan itace mafita, dole ya mutu kuma mu anshe shedar da take wajensa, hatta da wannan direban nasa bazamu bari ba saboda yasan komai. 

Girgiza kai Mr. Kallah yayi yana fad’in maganar gaskiya bazan iya aikata kisan kai ba, duk son kud’ina bai kai nayi kisan kai ba, ina laifin mu saceshi tare da matarsa har sai ya kawo mana duk wata sheda da yake da ita. 

Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad’in Mr. Kallah ka manta waye ni, to Malan Hassan ma da aka ba aikin tuni ya tsufa arami. A zabure Mr. Kallah ya mik’e yana fad’in haba Alhaji Marusa, duk da ban kasance musulmi ba nasan kisa ba abu bane mai kyau, me yayi mana? Sheda ce yake da ita kuma muna da hanyar da zamu karb’eta. 

Tashi Alhaji Marusa yayi fuska a d’aure yana fad’in Mr. Kallah bana so mu fara haka da kai, kasan yanda muka dad’e da kai muna harka, bana so saboda wannan k’aramun abun mu samu matsala, kasan dai tunda muka san sirrin juna dole mucigaba da tarayya, dan haka ka amince da abinda muka fad’a. 

Murmushi Mr. Kallah ya saki ya kamo hannun Alhaji Marusa yana fad’in haba abokina ai wannan abun bazai lalata tarayyar mu ta shekara da shekaru ba, ka sani nima bazanso asirin mu ya tonu ba, shikenan ayi abinda kukace. 

Murmushi Alhaji Marusa ya saki yana fad’in ko kai fa abokina, wannan hanyar ita kad’ai zamubi mu rufe wannan maganar, domin Allah kad’ai yasan iya abinda suka samu akan mu. 

Brr. Barau yace amma ya zamuyi dasu Abubakar da Moses? Alhaji Marusa yace zasubi wanda sukasa aikin ne. Mr. Kallah yace kisan zaiyi yawa fa, kasan yanda jini yake zai iya binmu, abinda zaifi zanyi masu canjin wajen aiki, kuma zamusa su Lucky suyi masu barazana akan abinda sukayi. 

Brr. Barau yace shikenan ayi hakan na yarda da kai. Alhaji Marusa yace duk ranar da wani abu ya faru babu ruwana. Mr. Kallah yace babu abinda zai faru ma. 

Wayar Brr. Barau ce tayi k’ara, yana dubawa ya kallesu yana fad’in babban ‘yallab’ai ne bara naji abinda zai fad’a kunsan kiransa samu ne. 

Saurin tashi yayi yana fad’in shikenan ‘Yallab’ai ka kwantar da hankalin ka zanji da wannan abun, wanda ya fishi ma muna rufewa bare kuma yau ya had’o da kai, shikenan zamuzo anjima akwai wata magana da zamuyi dama. 

Kashe wayar yayi ya zauna yana fad’in wata sabuwa. Alhaji Marusa yace meya faru kuma? Brr. Barau yace kunsan akwai Yaron wajen ‘Yallab’ai na biyu mai suna Fawwaz ko? Kai suka jinjina. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button