ALKALI NE Page 21 to 30

Brr. Barau yace wallahi wani tsautsayi ne ya faru dashi, yaron yana makarantar *King’s collage* ne, kunsan yaran zamani akwai wauta, tsautsayi yasa sukayi fad’a da wani abokinsa akan mace shine fa ya yankeshi da wuk’a a wuya ajali yana kusa yaron ya mutu, ‘Yallab’ai yace agaban mutum biyu akayi abun yanzu haka sun wurgar da gawar a wani waje, to sauran mutum biyun manyan abokansa ne nasan bazasu tab’a tona masa asiri ba, to amma d’aya daga cikinsu yace yaga wani d’an ajinsu kamar yana d’aukarsu alokacin da akayi abun, domin yaga lokacin daya fito ya ruga, shine hankalin ‘Yallab’ai ya tashi, domin idan wannan maganar ta fito zai rasa kimarsa, toshine yace naje yana nemana.
Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad’in lallai wannan babbar magana ce, abinda ya sameshi ai ya same mu ne, dan haka kutashi muje yanzu sai mu gama komai kawai.
**** ***
*Naseer* ne ya fito daga gidansu hankali atashe, ya rasa wanda zai nuna ma wannan abun daya d’auka, haka Allah yayishi da tsoro gashi yaje ya gano abinda yafi k’arfinsa har ya d’auko saboda ya nuna sheda, domin yaron da aka kashe abokinsa ne suna gaisawa.
Kallon wayarsa yayi yana tunanin wanda ya kamata ya nuna ma wannan abun, ko a gidansu babu wanda yasani, shiyasa ya fito kada Mamansa ta ganoshi. Tunani yayi ko dai ya kaima Baban Fawwaz tunda babban mutum ne yasan dole ya d’auki mataki akanshi.
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa, wayarsa yasa aljihu yana fad’in bara yayi sallah yaje ya kaimasa shima ya huta. (Allah sarki Naseer yarinta ta hana ka gane tsakanin Uba da ‘Dahsai Allah????????♀) .
***
Lokacin da yaje gidansu Fawwaz Maigadin gidan ya samu, bayan sun gaisa ya fad’a masa d’an makarantar su Fawwaz ne malaminsu ya aikoshi wajen Babansu. Murmushi maigadi yayi yace aikuwa Alhajin yayi baki suna lambu suna ganawa, amma tunda sako zaka bayar kaje ka fad’a masa kada na tsaida ka bansan lokacin da zasu gama ba.
Godiya Naseer yayi masa yashiga, babu wanda ya ganshi har ya d’auki hanyar lambu, yana dab da zai isa wajensu yaji muryar Brr. Barau yana fad’in ‘Yallab’ai ba ance sunan yaron daya d’auki kisan Naseer ba? Abinda zaifi anemoshi a daren yau a kashe shi kawai.
Hannu Naseer yasa ya dafe kirjinsa jin abinda aka fad’a, har ya juya zai gudu sai kuma jarumta tazo masa, wayarsa ya d’auko ya kamo wajen ya matsa kusa dasu yanda zai d’auka da kyau ya b’oye yana d’aukar su.
Mr. Kallah yace wai Brr. Barau meyasa fad’in kisa baya maka wahala ne, kace akashe Alhaji Maiwada, sannan kuma k’aramin yaro kace akashe shi Allah fa zai kama ka.
Alhaji Marusa yace Mr. Kallah yanzu idan yaron ka ne aka ce ya aikata haka zaka bari a yanke masa hukuncin kisa bayan be gama more rayuwarsa ba? Brr. Barau yace Fawwaz shekararsa 19 ya isa ya d’auki kowane hukunci, tunda aji shidda yake yanzu gab suke da gamawa domin jarabawa suke zanawa, Mr. Kallah kayi tunani mana, mu da ‘Yallab’ai mun saba tonawa mu rufe domin zaman lafiyar mu, idan asirin wani ya tonu acikin mu gaba d’ayan mu ya shafa.
Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad’in haka ne, yanzu ya kuke gani za’ayi? Alhaji Marusa yace ayau za’a kashe su duka, Abubakar da Moses na tura su Lucky tun d’azu ina da tabbacin sun kamasu yanzu, zanyi magana da Peter ‘Yallab’ai ka tambayar mana kwatancen gidan su Naseer zaije ya d’aukoshi za’a shafe babinsa, shi kuma Alhaji Maiwada su Lucky zasu kaddamar masa anjima bayan ya taso daga wajen aiki.
Dariya Brr. Barau yasa yana fad’in shugaban kwastam ake fad’a maka, daga yau bamu da sauran tashin hankali, Alhaji zaka cigaba da tafiyar da kasuwancinka yanda kakeso, muma zamu k’ara hannun jari domin ya bunk’asa.
‘Yallab’ai yace wannan haka yake, dama dole kasa rigar mutunci ka b’oye zahirin ka idan kana so ka zauna lafiya da mutane, domin yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, nafi son mutuncina so dubu.
Mr. Kallah yace amma akwai abokan Fawwaz da kace sun san komai, baka tunanin yanayi yasa su tona? Brr. Barau yace bazasu iya tona komai ba, kawai zanyi magana dasu akan su manta da komai, ‘Yallab’ai dole a fitar da Fawwaz waje yayi karatu hakan zaisa hankalinsa ya kwanta.
Jinjina kai ‘Yallab’ai yayi yana fad’in nagode sosai, kuma zanyi hakan, abinda nakeso mu k’ara rik’e sirrin junan mu, Brr. Barau kayi mani alkhairi da yawa arayuwa, abu d’aya zanyi maka wanda zan saka maka, kaine zaka zamto *ALKALIN GOBE* na babbar kotun ku. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad’in nagode Allah ya saka, ashe zan kai wannan matsayin.
Jiki na rawa Naseer ya baro wajen, gaba d’aya zufa ta gama rufeshi, ko takan Maigadi bebi ba yayi hanyar waje, Maigadi yana tambayarsa ya bada sakon amma be saurareshi ba yayi waje da gudu.
Kai tsaye d’akinsa ya shige ya saki kuka, ya dad’e yana kuka kafin ya d’auko Flash ya jona da wayarsa, gaba d’aya abinda ya d’auka ya tura, kayan jikinsa ya canza ya b’oye Flash d’in a aljihu ya fito.
Mamansa ce ta kalleshi tana fad’in Naseer wai yau lafiyar ka kuwa? Murmushi yayi yana fad’in lafiya lau Mama. Dama zanje gidansu Mannir na amso littafina saboda muna da jarabawa da safe ranar litinin a makaranta na mantoshi a ajakarsa.
Jinjina kai tayi tana fad’in yanzu za’ayi kiran sallar magriba ka biya masallaci kayi sallah kafin ka wuce, kuma kasan yanda unguwarsu take da ka bari ma sai da safe. Naseer yace bazan dad’e ba Mama. Murmushi tayi tace shikenan kaje kayi sallah. Naseer yace to Mama yanzu zanyi. Har ya kai bakin k’ofa Mamansa ta kirashi, dawowa yayi yana fad’in gani.
Ido ta tsura masa kafin tace Naseer kamar akwai abinda kake b’oye mani ko? Saurin girgiza kai yayi yana fad’in bakomai Mama. Murmushi tayi tana fad’in shikenan ai nasan baka mani k’arya, Allah ya tsare ka gaishe da Mannir d’in.
***
Risnawa Maigadi yayi yana fad’in barkan ku da fitowa, hannu Alhaji Marusa yasa aljihu ya ciro kud’i yana fad’in ga wannan anci goro ko. Amsa yayi yana masa godiya. Har sun kai bakin k’ofa Maigadi yace ‘Yallab’ai wannan yaron ya samu ganin ka kuwa? Cak suka tsaya jin abinda yace.
‘Yallab’ai yace wane yaro kenan? Maigadi yace d’azu wani yaro yazo yace yana nemanka shine nace kana da baki, sai yace sako zai baka inji malaminsu, shine nace kuna lambu yaje ya sameka, to bayan wani lokaci ina zaune sai kawai naga yaron ya fito a firgice, yanayin yanda naganshi yasa na taso ina tambayarsa ya ganka, amma be tsaya saurarata ba yayi waje a guje, to da yake bansan yanda kukayi ba shiyasa na kyaleshi na zauna.
Gaba d’ayansu hankalinsu ne ya tashi jin binda Maigadi ya fad’a. Brr. Barau ne yace a ina Yaron yace maka yake? Maigadi yace ni dai yace mun d’an ajinsu Fawwaz ne. Dam… Gabansu ya sake fad’uwa.
Da sauri suka fita waje hankali tashe. Da kallon mamaki Maigadi ya bisu ganin yanda hankalinsu ya tashi.
Dafe kai ‘Yallab’ai yayi yana fad’in duk yanda akayi wannan yaron turoshi akayi. Brr. Barau yace ba lallai turosa akayi ba, nafi tunanin yazo wajenka domin ya fad’a maka abinda ya faru, sai kuma yaci sa’ar sauraron abinda muke tattaunawa wanda ya tada hankalinsa ya kasa ganinka ya fita da sauri, abin tambayar anan shine, ya d’auki abinda muke tattaunawa akai ko kuwa saurara kawai yayi? Alhaji Marusa yace koma menene bazamu barshi ba, dole anemoshi kuma a amso wannan shedar daya d’auka.