ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 21 to 30

Waya ya ciro yana fad’in bara nakira Lucky. Bayan ya d’auka Alhaji Marusa ya bashi umarnin su nemo Naseer a duk inda yake, su kashe shi kuma su amso wayarsa. 

Peter ya kira anan yake fad’a masa ya baza yaranshi su jiran Alhaji Maiwada ya fito su k’addamar masa. Godiya yayi masu ya kashe wayar.

Fawwaz ne yazo wucewa shida abokansa, risnawa sukayi suka gayar dasu Alhaji, duk sai Fawwaz ya tsargu ganin fuskokinsu d’auke da damuwa. Dadynsa ne yayi kiransa, bayan yazo ya tambayesa unguwar su Naseer. Fad’a masa yayi, Brr. Barau yace baka da hotonsa? Fawwaz yace akwai, wayarsa ya d’auko ya nuna masu, amsa Alhaji Marusa yayi nan take ya tura awayarsa, bayan sun shiga Alhaji Marusa ya turama Lucky had’e da kwatancen unguwar. 

Brr. Barau yace zamu wuce ‘Yallab’ai ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru, anjima zan dawo domin in gana da abokan Fawwaz hada shima. Godiya yayi masu yana fad’in ab’atar da duk wata sheda. Alhaji Marusa yace wannan ba matsala bane nasan yarana. 

****

Bayan an gama sallar magriba kafin Naseer ya fito yaji ana sanarwar mutuwar abokinsa wanda aka tsinci gawarsa a cikin daji saboda unguwarsu d’aya. Runtse ido Naseer yayi hawaye suka zubo masa, da sauri yazo fita sai yaji an dafashi, yana juyowa yaga wani abokinsa ne makwafcinsu. 

Hannu yasa ya goge idonshi yana fad’in Saddik ya gidan? Saddik yace lafiya lau Naseer, naji wanda aka fad’a ya rasu a makarantar ku yake ko? Kai Naseer ya jinjina masa. Saddik yace Allah yajik’ansa, cike da k’osawa Naseer yace amin kafin ya fice. 

Wayarsa ya d’auka ya kirawo abokinsa Mannir, yana d’auka Naseer yace Mannir kana gida? Mannir yace ina gida lafiya naji muryarka wani iri? Naseer yace akwai wata magana da nakeso na fad’a maka akan mutuwar abokin mu amma ka jirani agida yanzu zanzo. Mannir yace shikenan sai kazo. 

Mota ya tare ya hau yana fad’in dan Allah Malan ofis d’in shugaban kwastam zaka kaini, jiyowa mai motar yayi yana fad’in sai dai na ajeka bakin titi domin bana son harka da kwastam. Naseer yace bakomai muje. 

Tafiya suke sai mai motar yaga kamar ana binsu, kallon Naseer yayi yana fad’in nifa jikina yana bani wani abu, sai nake ganin kamar ana binka, kodai ka d’auko wasu kud’i ne? Naseer yace ba wasu kud’i kawai ka tsargu ne. 

Lucky ne ya kira Alhaji Marusa ya fad’a masa sun samu yaron mma sunga kamar ya d’auki hanyar ofis d’in Kwastam. Alhaji Marusa yace kuyi a hankali kunga dai dare beyi ba sosai, bana so kuzo ba tare da kungama komai ba. 

Tsayawa direban yayi yana fad’in iya nan zan tsaya sai ka k’arasa. Kud’i Naseer ya bashi yana fad’in nagode. Tafiya ya fara gabanshi yana fad’uwa, yanaso yaje ya tambaya a nuna masa shugaban Kwastam dan shine yaji su Alhaji suna maganar za’a kashe, gara yaje ya fad’a masa yasan kila shima ya samu kariya, gashi ko ganinshi bai tab’ayi ba ballantana ya ganeshi, dole sai yayi tambaya. 

***

Alhaji Maiwada bayan ya gama aikinsa ya fito, sallama sukayi da Malan Bala yana fad’in gobe bazan shigo aiki ba sai litinin, a gyara ofis d’in da kyau. Malan Bala yace insha Allahu. Kud’i Alhaji ya ciro ya mik’a masa yana fad’in gashi kayi kud’in mota kayi cefane naga wata ya raba tsakiya. Godiya sosai Malan Bala yayi masa, har bakin mota ya rakoshi. 

Ganin su Abubakar da Moses yasa ya tsaya, k’arasowa sukayi suna fad’in har yanzu basu samu wayar Malan Hassan ba, kuma agidanshi ance bai koma ba. Moses yace ina tunanin wani abu, ko dai sun kamashi ne suka kulle? Alhaji yace insha Allahu babu abinda zasuyi masa, gobe zamuje can gidanshi muji. Godiya saukayi tare da masu sallama yashiga mota Malan Sani yaja suka tafi. 

Su Moses suna barin wajen kasancewar a motar Abubakar suke, bayan sunyi nisa yaran Peter suka tare su, nan take suka shiga motar suka bar wajen dasu bayan sun watsa masu wata hoda. 

**

 A hanya Alhaji yana gyara wasu aiyuka a cikin kamfutarsa yake fad’ama Malan Sani yanda sukayi da Alhaji Mansur. Malan Sani yace Alhaji ni har wannan kamfutar ma da kadena fitowa da ita kasan akwai abu mai muhimmanci aciki. Alhaji yace ai babu wanda yasan yanda ake bud’eta, kuma natura shedar a Flash saboda tsaro. Malan Sani yace hakan dai yafi. 

***

Jikin Naseer ne ya fara rawa ganin kamar ana binsa, nan take tsoro ya kamashi sai ya baza da gudu yana tunanin ya koma gida kada garin neman shugaban kwastam akamashi, haka kawai ma yaje garin tambaya wani yace shine sai ya fad’a masa gaskiya a kamashi tunda duniyar babu gaskiya, gudu yake aranshi yana fad’in babu wanda zan tambaya gara naje na fara saninshi a hoto kafin naje wajensa. 

***

Birki Malan Sani ya taka da sauri ganin mutum ya faad’o masa. Alhaji yace lafiya dai Malan Sani? Bud’e motar Naseer yayi ya shige sai haki yake yana fad’in dan Allah ku taimaka mani wasu ne suka biyo ni. 

Alhaji yace ikon Allah! Kai ko yaro meya had’aka dasu? Naseer yace kawai ‘yan iskan gari ne. Malan Sani yace ka tabbata abinda ka fad’a gaskiya ne? Naseer yace wallahi da gaske nakeyi. Alhaji yace tuk’a muje. 

Malan Sani yace Alhaji… Hannu ya d’aga mashi hakan yasa yaja suka tafi. Naseer yayi masu kwatancen unguwar su Mannir, kasancewar hanyar gidansu bata da kyau Malan Sani yace sai dai mu ajeka bakin hanya dan yasan unguwar bata da kyau. Naseer yace hakan ma yayi nagode. 

***

Waya Lucky yakira Alhaji Marusa yana fad’a masa yaron yashiga motar su Alhaji Maiwada. A firgice Alhaji Marusa ya mik’e yana fad’in mene? Wallahi idan kuka bari ya sha sai na kashe ku, inaso kushiga gabansu yaron yana fita ku gama dashi, shima Alhaji bazai sha ba yana barin wajen su Peter zasu k’addamar masa.

**

Malan Sani ne yace Alhaji kaji labarin wani yaro da aka kashe ko? Alhaji yace wallahi d’azu nakejin labari, kai zamanin nan ran mutum ba abakin komai yake ba. Naseer yace ai abokin mu ne makarantar mu d’aya. Alhaji yace Allah sarki, Allah yajikansa ya tona asirin wad’an da suka kashe shi. Naseer yace amin. Yana so ya fad’a masu gaskiya yana jin tsoro hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru. 

Suna zuwa bakin hanya Malan Sani ya tsaya yana fad’in kayi sauri ka wuce kasan dai wannan hanyar bata da kyau. Godiya Naseer yayi masu, jiyowa yayi yana fad’in Abba nagode. Murmushi Alhaji yayi masa yace bakomai ka kiyaye ka daina kaiwa dare a waje kaji. Kud’i ya bashi yana fad’in ga wannan kasa kati. 

Godiya Naseer yayi masa, haka kawai yaji ya yarda da mutumin, sai yayi tunanin ya b’oye Flash d’in amotarsa yasan zai gani, idan ya gani zai taimaka. Hannu yasa ya zaro Flash d’in, a hankali ya turashi k’asan kujerar baya ya fita. 

Kan motar Malan Sani ya juya yana fad’in wallahi shiyasa nake jin dad’i da Ra’eez baya zama agarin nan, kallifa ko isha’i ba’ayi ba amma an fara bin mutane. Alhaji yace kai dai sai addu’a, shiyasa nace maka muna gama wannan shari’ar zan aje aikina na bar garin nan. Malan Sani yace ai k’afarka k’afata Alhaji, domin bazanji dad’in zaman garin nan ba idan bakanan. 

Alhaji zaiyi magana kenan sukaji motarsu tana rawa alamun taya ta samu matsala. Malan Sani yace kila kuwa mun taka k’usa, Alhaji yace tsaya mugani. Malan Sani yace gara mu tuk’ata ahaka wajen nan beda kyau kuma babu mutane. Alhaji yace Malan Sani kaci ka tsoro, dare fa beyi ba gara mu canza wata tayar zaifi. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button