ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 21 to 30

***

Taku ukku Naseer yayi yaji an damkoshi, baki ya bud’e zeyi ihu aka rufe bakin, d’aukarshi sukayi zuwa cikin motarsu. Kasancewar motar bakin gilashi ne yasa ba’aganin na ciki. 

Mari Lucky ya d’auke Naseer dashi yana fad’in mai ka fad’ama Alhaji Maiwada? Cikin firgici Naseer ya kallesu yana fad’in waye haka kuma? Lucky yace motar data ajeka yanzu ai shugaban kwastam ne aciki meya had’a ka dashi? Farin ciki ne ya kama Naseer jin ya aje shedarsa a inda ta dace, kuma ko zasu kashe shi bazai fad’a masu abinda ya aje ba. 

Dukan da akayi masa yasa ya dawo daga tunanin da yakeyi. Cikin wahala yace wallahi babu abinda na fad’a masa ni bamma sanshi ba kawai ragemun hanya sukayi dama wajen shugaban kwastam zanje sai kuma tsoro ya hanani k’arasawa shine na dawo sai muka had’u suka d’aukoni. 

Amsar wayarsa Lucky yayi, yana dubawa yaga abinda ya d’auka duka suna nan, waya ya kira Alhaji Marusa ya fad’a mashi, murmushi yayi yace ku gama dashi kuma ku jefar da gawarsa, banaso ku rifeta ku barta domin Iyayensa su masa sallah. 

Duk magiyar da Naseer yake masu haka suka kashe shi suka ja motar zuwa inda zasu yarda shi sukayi tafiyarsu da wayarsa bayan sun cire layin sun yona rami sun rufe. 

***

Cike da tsoro Alhaji yake kallon mutanan da suke tun karosu, Malan Sani yace Alhaji kana ganin abinda nake gani kuwa? Alhaji yace dama tunda su Moses sukace Malan Hassan ya b’ace jikina ya bani kamashi akayi, sun gano komai shine suka turo akashe mu. Abinda nakeso da kai Malan Sano ka fita da gudu kai ka tsira. 

Malan Sani yace ka daina fad’ar haka, bazan barka anan ba. Alhaji yace dole wani ya tsira acikin mu, Bilkisu da Ra’eez basu da kowa sai ni, idan suka kasheni zasu iya zuwa su kashe ta, Ra’eez zai taso cikin maraici, inaso kaje ka fitar da ita daga gidan nan, inaso ka kula mani dasu domin rayuwata suke nema ba taka ba, idan ka tsaya zasu had’a da kai. 

Kuka Malan Sani yasa yana mai rik’e da hannun Alhaji.Kamfutarsa ya miko masa yana fad’in jeka da ita, ka tabbatar ka fitar da Bilkisu, kace ta yafe mun kuma tayi hakuri da rayuwa, Allah ya albarkaci abinda zata haifa, kuma kuyi kok’arin barin garin nan kada kuzauna aciki dan Allah, ka shafa mani kan Rumaisa da Ra’eez. 

Kuka kawai Malan Sani yake haka ya fita daga motar, kasancewar bata b’angaren da suke taho yake ba hakan yasa ya gangare basu ganshi ba, wani daga cikinsu ne ya hango giccensa nan ya fad’ama Peter. 

Kafin su k’arasa ya kira Alhaji Marusa ya fad’a masa direban ya gudu hada jakar kamfuta a hannunsa. Alhaji yace nasan gidan Alhaii Maiwada zaije domin ya ceci matarsa, kuji da Alhajin zain tira su Lucky gidan yanzu, nasan zasu rigashi zuwa tunda da mota hannunsu shima zasu kasheshi. 

Fito da Alhaji sukayi, yana rok’on su amma basu saurareshi ba, wani kyalle sukasa suka nad’e mashi wuya dashi har sai da yadena numfashi. Wurgashi cikin motar sukayi suka bar wajen. 

**

Brr. Barau ne yayi kiransu Lucky ya basu umarnin kada su kashe Malan Sani su barshi sun canza shawara, kawai sujirashi agidan yazo su amso kamfutar su fito. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

1⃣5⃣

Tsayawa Malan Sani yayi yana hutawa sai dube-dube yake, hawaye kawai suke zubo masa, shikenan yanzu sun kashe Alhaji, kai duniya. Hannu yasa ya ciro wayarsa, Alhaji Mansur ya kira, yana d’auka ya sake fashewa da kuka. 

Hankali tashe Alhaji Mansur yake tambayarsa abinda yake faruwa. Tsagaita kukansa yayi ya fad’a masa abinda ya faru. Salati Alhaji Mansur yasa jikinsa yana rawa. 

Malan Sani yace yanzu haka ina hanya inaso na k’arasa can gidansa na tafi da Hajiya. Alhaji Mansur yace kaga tana d’auke ta juna biyu, kayi yanda hankalinta bazai tashi ba dan Allah, kuma shima Alhajin insha Allahu babu abinda zasuyi masa, gobe da wuri zan iso, Allah ya tsare ku gaba d’aya. 

Mota Malan Sani ya tare yana saka wayarsa aljihu. Gani yake kamar mai motar baya gudu, addu’a kawai yake Allah yasa basu yima Alhaji komai ba. 

***

Ta bayan gidan suka shiga dan Alhaji Marusa yace baya so Maigadi yasan da zuwan su saboda Brr. Barau ya had’a wani shiri ta yanda zasu fita daga zargi. 

Ummun Ra’eez tana zaune a falo sai gwada kiran wayar Alhaji take amma taki shiga, duk da tasan yana wuce haka bedawo ba amma kafin ya baro ofis sunyi waya yace ta dafa masa kwai guda ukku zaici abinci dasu. 

Gashi Ladi bata nan taje Kauyensu ana biki sai litinin ma zata dawo. Wayar ta aje tana mai jin wani irin sanyi yana shigarta, rufe ido tayi tana karanto duk addu’ar data zo mata. 

**

Madu ne ya bud’e k’ofa jin k’arar bugawa, mamaki yayi ganin Malan Sani shi kad’ai ga idanuwansa duk sun kumbura. 

Shigowa Malan Sani yayi yana fad’in Madu akwai matsala fa. Madu yace matsalar me ina Alhajin? Malan Sani yace ina zuwa bara na fito. Be jira abinda zai fad’a ba yayi gaba. Zama Madu yayi yana fad’in ikon Allah, wace matsala ce kuma wannan? Taya Malan Sani zai dawo shi kad’ai kuma, ga jaka a hannunsa kamar ta kud’i, sannan idanuwanshi duk sunyi ja kamar wanda ya shawu, ko dai Alhajin ne ya aikosa? Amma da mamaki, Redionsa ya jawo yana fad’in bari ya fito muji. 

Bayan Ummu ta bud’e k’ofar sai taji gabanta ya fad’i ganin Malan Sani d’auke da bak’ar jaka ta kamfutar Alhaji. Batayi magana ba ta shiga ciki tana fad’in shigo mana. 

Shiga yayi ba tare daya rufe k’ofar ba. Zama Ummu tayi tana fad’in Malan Sani Abbun Ra’eez ko aiki ya rik’esa ne? Duk’ar da kai yayi hawaye suna cika masa ido yace shine ya aiko ni na d’auke ki mu tafi can gidana gobe kuma zamu wuce kano. 

Zatayi magana kenan sukaji alamun motsin shigowa, dama zaman jiran Malan Sani sukeyi kuma aka ci sa’a be rufe k’ofar ba. 

Saurin mik’ewa sukayi ganin manyan mutane a cikin gidan. Hannu Ummu tasa ta dafe cikinta tana fad’in Malan Sani kace mun sun kashe Alhaji kawai, gashinan kaima kuka kakeyi, meyasa zasuyi mani haka, ina gawarsa take dan Allah? Kuka Malan Sani yasa yana kallon su yace narok’e ku da girman Allah kada ku kashe ta, ku kasheni amma kubarta ita da abinda yake cikinta. 

Zuciya ce ta ciyo Ummun Ra’eez ta rarumi flask d’in ruwan zafi da yake kusa da ita ta wurga ma Lucky, saurin kaucewa yayi cikin zafin nama ya kwad’a mata sandar da take hannunsa akai. 

K’ara Ummu ta saki ta fad’i da k’arfi saman cikinta, nan take jini ya b’alle mata. Salati Malan Sani yasa yayi kanta da sauri, kamota yayi yana jijjigata amma babu alamun rai ajikinta, ga kanta yana fitar da jini k’asanta ma jini na fita. 

Kuka yake yana fad’in baku da imani, me wannan matar tayi maku. Tsaki Lucky yayi danshi baya b’ata lokaci a aikinsa. Wata hoda ya fesama Malan Sani nan take yaji kanshi yayi nauyi, hannu yasa ya dafe kanshi yana jin yanda falon yake juya masa. 

Duk’awa Lucky yayi ya kama hannun Malan Sani ya kamo na Ummun Ra’eez, Malan Sani yana kallonsa amma jikinsa ba kwari, hannun Ummun Ra’eez yasa a wuyan Malan Sani ya karceshi da faratan ta da bata yanke ba, nan take sahu ya fito harda jini. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button