ALKALI NE Page 31 to 40

Sun dad’e a wajen Malan Sani suna fira, lokacin da zasu tafi Alhaji Mansur ya samu shugaban ma’aikatan suka gaisa, alheri yayi masa yana rok’onsa akan ya kula da Malan Sani. Murmushi yayi yana fad’in bakomai Alhaji, babu abinda zamuce da wannan k’asa tamu sai addu’a, amma wata shari’ar sai a lahira. Godiya Alhaji Mansur yayi masa suka tafi.
***
Bayan sun gama cin abinci sukayi sallah. Zama sukayi da Madu suna ta fira. Madu yake fad’a masa komai lafiya na gidan Alhaji, dan Maigadin yana kula da komai, motar Alhaji ma an rufeta da tampol, sai dai yana ganin gara a cire tayoyin a d’ageta zaifi.
Kallon Ra’eez Alhaji Mansur yayi yana fad’in Ra’eez ko dai asiyar da motar asaka maka kud’in a banki tunda nan gaba yayinta zai wuce? Kallonsa Ra’eez yayi yana fad’in Abbah idan aka barta har na girma akwai abinda zai sameta? Kai ya girgiza masa.
Ra’eez yace dan Allah Abbah abarta, ina so idan na girma na tuk’ata domin narik’a tunawa da Abbu kaji. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad’in angama Ra’eez, insha Allahu baza’a sai da ta ba, kuma sai ka tuk’ata da izinin Allah, sai dai ina ganin zamu tafi da ita can kano kaga akwai gareji sai sata ciki kawai.
Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in yauwa Abbah. Madu yace shikenan ma, nima hankalina zaifi kwanciya idan aka tafi da ita, domin za’a iya d’auketa, amma idan aka tafi da ita ya rage sai gida kawai shiko babu wanda zai d’aukeshi, shima dan kace abarshi amma da an sayar dashi hankalin kowa ya kwanta.
Alhaji Mansur yace akwai dalilin da yasa nace baza’a siyar dashi ba, wata rana Ra’eez zai zo yayi aiki agarin nan, kuma bana so ya zauna a wani waje, dan haka ka barshi babu abinda zai sameshi da izinin Allah, idan ma Maigadin ya gaji sai asamo wani. Madu yace begaji ba, shikenan ayi yanda kace.
Rumaisa ce ta shigo tana fad’in Yaya kazo muje kaga takarduna to. Murmushi yayi yana fad’in kilama duk ziro kikaci. Rumaisa tace wallahi duk na cinye, kok’ari fa gareni, kusan kullum sai an bani kyauta a aji. Ra’eez yace to muje na gani.
Dariya sukayi Alhaji yana fad’in ina ruwan Ra’eez, tunda yasan mutuwar mahaifinsa ban sake ganinsa cikin annashuwa ba sai da mukazo yaga Rumaisa, shiyasa na yanke shawarar barinsa yayi sati d’aya idan yaso sai ya taho ta jirgi, ni kuma sai na tafi da motar dan bana son na tafi dashi amota kasan hanyar Lagos. Madu yace haka ne, Allah ya tsare mana kai. Alhaji yace amin.
**** ****
Wshe gari tunda asuba Alhaji Mansur ya tafi bayan ya cika Halima da kud’i ita da Madu. Ra’eez da Rumaisa sai dad’i sukeji zai zauna yayi sati.
Sosai Halima take jin dad’in zaman Ra’eez domin koda yaushe yana koyama Rumaisa karatu, haka idan tayi ba dai-dai ba yana tsawatar mata, sai take ji ina ma abar matashi kodan Rumaisa.
Tunda sukaje asibiti basu sake komawa ba sai ana saura kwana biyu Ra’eez ya tafi, a wannan rana jikin Ummu bai tashi ba, haka Ra’eez ya wuni a wajenta dan Halima acan ta barosa, duk da ita kad’ai take shirmenta amma shi d’auka yake fira sukeyi, dan ita labarin Abbu kawai take bashi, hakan yasa shima yayita bata labarin Abbun.
Idan ka gansu sai ka d’auka mai hankali ce, gaba d’aya masu kula da ita aranar sunyi farin ciki domin kowa yasan Ra’eez yazo, duk wanda yaje sai ta fad’a masa ga Ra’eez shine zaije makka yasiyo mata wuk’ar da zata kashe wad’an da suk kashe mata Abbun Ra’eez, gaba d’aya aranar kowa sai da ya gaji da jin sunan Abbun Ra’eez.
Sai da yamma sosai Madu yazo tafiya da Ra’eez, anan fa Ummu tace bata san maganar ba, kuka da ihu tashiga yi za’a sace mata Ra’eez, haka ta rik’eshi tana kuka duk ta yakushe shi, sosai Ra’eez ya tsorata da yanayinta, duk yanda aka so akwace Ra’eez abun ya faskara domin wani irin k’arfi ne yazo mata, ta jima mutane da yawa ciwo hakan yasa dole suka kira Dr. Najib.
Koda yazo shima yasha fama, sai da yayi ta maza ya rik’eta da k’arfi akayi mata allura kafin tayi shiru, har bacci ya d’auketa hannunta yana rik’e dana Ra’eez, a hankali aka cireshi daga jikinta. Ra’eez yana waigenta har suka fita daga d’akin suka wuce gida sai kuka yakeyi.
A ranar haka ya wuni da kyar Rumaisa tasa yaci abinci. Bayan kwana biyu aka gama mashi komai na tafiya Madu ya d’aukeshi domin ya kaishi inda zai hau jirgi. Daga Rumaisa har Halima sai da sukayi kuka da zai tafi, shima kukan yakeyi da kyar suka rabu.
*** ***
Lokacin daya sauka Alhaji Mansur hada Labiba sukaje d’aukoshi, Labiba sai murna takeyi abokin firarta ya dawo. Haka suka nufi gida.
***
Lokacin da hutunsu ya k’are haka Alhaji Mansur ya had’a masu komai, d’aki yaja Ra’eez ya fad’a masa kud’in mahaifinsa sun fito, kuma ya saka masa abankin da Alhaji Maiwada ya bud’e masa ya saya masa hannun jari domin arik’a juya kud’in. Ra’eez yace Abbah bana so kace bazaka tab’a kud’ina ba, kaga a waje zanyi karatu ina so nayi karatu da kud’in Abbu domin ina so nayi amfani da guminsa nayi karatun da zan kwato masa hakkinsa.
Murmushi Alhaji Mansur yayi yace Ra’eez kenan, ko sisi baza’a tab’a maka ba, nine nayi niyar sai kayi karatu a waje kuma zakayi shi komin tsadarsa. Ra’eez yace dan Allah Abbah. Alhaji Mansur yace naji yanzu dai muje kada muyi dare, kuma bana so kasa damuwa aranka idan ba haka ba baza kaje karatun aikin lauya ba kaji. Ra’eez yace zan dage.
Haka suka fito suka yima Maman su sallama suka tafi cike da kewar gida, Labiba sai haushi takeji an canza ma Ra’eez aji yanzu saiya rigata gamawa, itama taso amayar da ita ajinsu amma Alhaji Mansur yace bazai maida ta ba dole ta hak’ura.
***
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, wasu suna jin dad’i wasu suna cikin wahala, tuni Halima ta fawwalama Allah al’amuranta, ta rungumi k’addararta da hannu biyu, cikin ikon Allah take tafiyar da rayuwarta babu abinda ta nema ta rasa, Madu yana kokari akansu sosai, ga Sister Hassana da mijinta.
Cikinta sai girma yakeyi tana zuwa awo ba tare da wata matsala ba, damuwarta d’aya idan taje ganin Malan Sani, ganin yanda take damuwa yasa Malan Sani yace ta dena zuwa kawai tacigaba da kulawa da kanta.
Su Brr. Barau kuwa rayuwa tayi masu dad’i, domin arzik’in yanzu ya wuce na baya, sun had’a hannu da Alhaji Marusa suna shigo da kaya wad’an da suke so, domin Adebayo shine aka ba kujerar Alhaji Maiwada dama kuma alk’awari aka masa matuk’ar komai yayi dai-dai shi za’a ba yayin da aka bama Umar matsayinsa. Wannan dalilin ne yasa suke cin karen su babu babbaka dan yanzu mutane suna kuka da yanda ake amsar masu kudi.
****
Lokacin da cikin Halima ya isa haihuwa safiyar juma’a ta tashi da nakuda, alokacin Rumaisa tayi shirin zuwa makaranta sai fasawa tayi, da gudu taje ta kira Sister Hassana, haka suka d’auketa suka nufi asibiti.
Cikin ikon Allah ta haifi d’anta namiji. Bayan an gama komai suka koma gida. Bayan da ta gama gyara jikinta Ladi tayima yaro wanka, kunu ta kawo mata da d’umamen tuwo, kasa ci tayi sai kuka takeyi.
Zama Ladi tayi tana fad’in haba Halima, godiya ya kamata kiyima Allah daya sauke ki lafiya, nasan kina tunanin rashin Malan Sani, ki sani bazaiji dad’i ba idan yaji kina cikin damuwa, kinsan yanzu ba’a son kina saka damuwa aranki, ki daure kici abinci dan Allah.