ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Hannu tasa ta goge idonta tana fad’in shikenan Ladi nagode. Amsar kunun tayi ta fara sha tana kwalla. 

Da wayar shugaban ma’aikatan gidan yari tayi magana da Malan Sani, sosai yaji dad’i haka yayi ta lallashinta kuma yace mata zai zo insha Allahu. Bayan sun gama waya shugaban ma’aikatan yace masa zai kaishi yaje yayi ma yaron hud’u ba. Sosai Malan Sani yaji dad’i yayi ta masa godiya. 

Sai da dare suka je, alokacin Rumaisa ma tayi bacci. Haka yayi ma yaron hud’uba da *Abdallah*, yaso yasa sunan Alhaji Hamza amma sai ya tuna da maganar Alhaji Hamza da yake fad’a masa.. *idan Ummun Ra’eez ta haihu idan mace ce zai saka sunan mahaifiyarsa, idan kuma namiji ne zaisa sunan mahaifinsa Abdallah, saboda beyi amfani da sunansa a jikin takardunsa ba, sai yayi amfani da sunan da ake kiransa dashi a cikin ‘yan uwa wato MAIWADA, hakan yasa yake son yasa sunanshi na gaskiya*. Wannan dalilin ne yasa Malan Sani ya cika ma Alhaji Maiwada burinsa. Ya dad’e yana kallonshi, wajen Rumaisa yaje yayi mata addu’a, sai da yaci abinci shida shugaban sannan suka tafi yana ta yima Madu godiya. 

***

Dubu hamsin Alhaji Mansur ya aiko mata asayi rago ayi siyayyar kayan yaro. Godiya tayi masa. Haka akayi hidimar suna cike da rufin asiri tamkar Malan Sani yana nan. 

****

Bayan da Ra’eez ya zana jarabawarsa suka baro su Labiba amakaranta, satinsa biyu a Kano ya taho Lagos yayi hutu kafin jarabawarsu ta fito. Sosai Rumaisa da Halima sukaji dad’in zuwanshi. 

**** ****

Bayan da jarabawarsu ta fito haka aka kammala masa komai, cikin sa’a ya samu gurbin shiga makarantar koyon aikin lauya da take Landon, cike da farin ciki yaje yayi ma Ummunsa sallama, sai dariya takeyi kamar tasan abinda yake fad’a. Haka yayi ma kowa sallama ya tafi cike da fatan nasara. 

*** ***

*Bayan shekaru da dama*,  

Abubuwa da yawa sun faru, aciki hada kaddamar da Brr. Barau a matsayin sabon Alkali na babbar kotu bayan da tsohon Alkali ya aje aiki, sosai yayi farin ciki da wannan al’amari dan ya dad’e yana jiran wannan rana. 

Mr. Kallah ma ya dawo Lagos da zama saboda ya aje aiki, gaba d’ayansu girma ya kama su, sai dai naira ta hana aga tsufansu, har zuwa wannan lokaci Alhaji Marusa yana shigo da haramtattun kaya, sai dai yanzu abun nashi na zamani yakeyi dan an samu cigaba. 

Ummun Ra’eez tana kan amsar magani, zuwa yanzu jikinta da sauki sosai, sai dai bata da yawan magana, idan ka ganta tamkar mai hankali amma bata magana, a koda yaushe maganarta d’aya Abbun Ra’eez sai kuma d’anta. 

Su Alhaji Mansur suna yawan kawo masu ziyara, haka wajen Malan Sani suna zuwa wajensa. Komai yana tafiya yanda ya kamata. 

A yanzu haka Rumaisa an girma tana aji ukku a babbar makaranta. Sosai kyanta ya k’ara fitowa, ga natsuwa ga kok’ari, sosai take maida hankali a karatun ta. Abdallah ma yashiga fimare, sosai suke waya da Ra’eez. 

Labiba kuwa tuni ta kammala makarantar ta, inda tayi karatu a FCE kano har ta kammala dan shekara ukku ne, yanzu haka ana shirin bikinta. 

****

Bayan da Ra’eez ya kammala karatunsa haka ya dawo gida cike da nasara dan ya fita da first class, sosai Alhaji Mansur yaji dad’in haka. 

Bayan dawowarsa yaje yaga Ummunsa kafin ya dawo kano, haka Alhaji Mansur ya nema masa (Bar school) da take abuja. Sai da akayi bikin Labiba kafin ya tafi. 

Shekara d’aya yayi kafin ya kammala, bayan ya dawo yayi service shekara d’aya, alokacin Rumaisa zata jana jarabawar fita daga makaranta. 

Yana kammala service d’insa ya samu aiki a babbar kotu da take kano. Kasancewar Ra’eez mai natsuwa da hazaka, cikin lokaci kad’an ya saye zuciyar mutane, dan duk abinda yasa agaba sai yaga bayansa, haka duk shari’ar da zaiyi sai yayi nasara, danshi baya amsar shari’ar da yasan babu gaskiya a cikinta, shiyasa mutane suke masa lak’abi da Mai gaskiya. 

Sai da yayi shekara d’aya a kano kafin Alhaji Mansur yayi nasara aka canza ma Ra’eez wajen aiki zuwa babbar kotu da take lagos. Ranar da takardarsa ta fito sosai sukaji dad’i, haka Alhaji Mansur yayi ta masa nasiha yana bashi shawarar yanda zai tafiyar da komai musamman da yasan cewar Brr. Barau shine Alkali a kotun da Ra’eez zaiyi aiki, kuma yaja kunnansa akan ya b’oye komai nashi, dan baya so kowa yasan yana da alak’a da Alhaji Maiwada har sai komai ya kammala. 

Cike da d’oki ya shirya ya tafi Lagos yana mai farin cikin zai koma kusa da abun sonshi Rumaisa, dan ya girma ne da soyayyarta, sannan zai koma kusa da Mahaifiyarsa. 

Sai da sukayi kwana ukku suna gyaren tsohon gidansu dan Alhaji Mansur yace ya zauna acan, alokacin tuni an sake maigadi kusan ukku bayan wancan, haka aka gyara komai kamar alokacin aka zuba su. 

A d’akin Abbunsa yace zai zauna. Haka ya shirya komai nashi. Yaso Maman Rumaisa su dawo gidan amma tace yayi zamansa tafi son ta zauna acan, duk yanda yayi haka ya hak’ura dan sai da Alhaji Mansur ya shiga maganar sannan. 

*Wannan shine asalin labarin Alhaji Hamza Maiwada*

Ajiyar zuciya Kawu yayi yana goge hawayen da suka zubo masa. Ra’eez kuwa kuka yake sosai kamar k’aramin yaro. Hannunsa Kawu ya kamo yana fad’in kada ka barsu Ra’eez, sun cutar dani sama da shekaru da dama, nayi kuka har na gaji, nayi dauriya har sai da hak’urina ya kusa k’arewa, sun lalata mani rayuwa, sun b’ata mani suna, sunci mutuncin Mahaifiyarka, ta kwashe shekaru tana cikin hali na rashin lafiya. 

Girgiza kai Ra’eez yayi yana fad’in kada ka damu Kawu, na girma da shirin d’aukar fansa, zan b’ullo masu ata yanda basuyi zato ba, insha Allahu sai asirin su ya tonu, sai Allah ya kawo mani hujja gamshashshiya, kamar yanda sukayi amfani da kwakkwarar hujja suka kada ka nima sai Allah ya bani wannan damar, kacigaba da tayani addu’a Kawu. 

Murmushi Malan Sani yayi yana fad’in ina kan yi Ra’eez, kaine keda nasara a wannan karon, sai sunyi nadamar abinda suka aikata. Allah yayi maka albarka. 

Ra’eez yace amin Kawu, zan zo na koma ka k’ara hak’uri Kawu. Malan Sani yace yanzu kam acikin farin ciki nake, fatana Allah ya barni da raina domin nasha kallo. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in amin. Sallama yayi masa ya tafi cike da damuwa aransa. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

2⃣2⃣

Yana kan hanyarsa ta komawa wajen aiki wayarsa tayi k’ara, yana dubawa yaga *Alkali ne*, saurin d’auka yayi, yana d’agawa ya fara tambayarsa ina yaje? Ra’eez yace na d’an fita na siyo magani ne ganinan dawowa. Kashe wayar akayi. 

Tsaki Ra’eez yayi yana jin wani b’acin rai, sosai yake jin hushin Alkali Barau, tunda yasan irin muguntar da sukayi ma Abbunsa da Ummunsa ya k’ara tsanarsa. Gudun motar ya k’ara dan yayi sauri ya isa. 

Inda ake aje motoci ya aje kafin ya fito, kai tsaye ofis d’in Alkali Barau yawuce, sai da ya fara kwankwasawa aka bashi zini kafin yashiga da sallama. 

Kallonshi Alkali yayi yana fad’in baka jin dad’i ne? Kai Ra’eez ya d’aga yana fad’in kaina ne yake ciwo amma nasha magani yayi sauki. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button