ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Alkali yace ko dai ka tafi gida kila bacci ne. Ra’eez yace da sauki zan iya zama. Murmushi Alkali yayi yana fad’in shikenan, dama nace idan an tashi ko zaka bini gidana nasa ayi abinci da kai amatsayin ka na sabon ma’aikacina mai kwazo, ina so na gabatar da kai a wajen Iyalina. 

Kau da kai Ra’eez yayi yana fad’in badamuwa nagode Allah ya kaimu atashi. Alkali yace amin, kuma naji dad’i, dan haka idan an tashi zan maka magana sai mutafi. Ra’eez yace to. Juyawa yayi ya fita. 

Zaune yake a ofis suna fira shida Brr. Jabeer, sauran ma’aikatan ne suka iso suna ma Ra’eez sannu da zuwa. Da murmushi ya amsa yana basu hannu suna gaisawa. 

Bayan sun gama Ra’eez ya kalli Jabeer yana fad’in gaskiya naji dad’in zuwa wannan kotun, domin mutanan cikinta suna da kirki musamman ‘Yallab’ai. 

Murmushi Jabeer yayi yana fad’in wai Alhaji Barau kake nufi? Ra’eez yace shi nake nufi. Murmushi Jabeer yayi yana fad’in kayi a hankali dai, domin kura ce rufe da fatar akuya. 

Ra’eez yace bangane ba? Jabeer yace bakomai manta kawai. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in tunda nazo muka gaisa da kai sai nake jin kamar kaine kafi cancan ta nayi abota dashi a wajen nan duba da yanayin ka, sai gashi nazo kai kuma kana so ka b’oye mani wani abu, kyakkyawar alak’a ana kullata ne da kyakkyawar zuciya, amma kila ni d’in ne banyi maka da zama aboki ba. 

Hannunsa Jabeer ya kamo yana fad’in wallahi ba haka bane, kasan ba’a son mutum yarik’a saurin fad’ar mugun abu ga wanda yazo waje amatsayinsa na sabon zuwa, ban sani ba kilama ‘yallab’ai d’an uwanka ne haka kawai nayi sara akan gab’a. 

Ra’eez yace amma na fad’a maka ba’anan nake ba, bani da kowa nan aiki ne ya kawo ni. Jinjina kai Jabeer yayi yana fad’in nima ai ban dad’e anan ba, kawai nasan labarinsa ne a wajen Kawuna, domin sunyi aiki tare dashi alokacin yana lauya, yanzu haka Kawuna yana Babbar Kotu da take garin Abuja, da tare suke anan, sai Kawu na yaje ya k’aro karatu, sukayi wani taro na k’asa da k’asa akan yanda za’a kawo cigaba akan shari’ar k’asarnan, Kawuna ya bada gudummuwa sosai, hakan yasa aka maidashi babbar camber da take abuja, kaji dalilin da yasa yabar wannan kotun domin yanzu yana saman Alhaji Barau. 

Ra’eez yace lallai ashe dai gadon aikin shari’a kayi. Jabeer yace wallahi kuwa, domin acikin ‘ya’yansa ma akwai lauya amma shi yana Jos acan yake aiki, a cikin dangin mu kusan mu biyar ne muke aiki a wannan fannin, da anan garin kake kila da ka san Kawuna, sunansa *Kamal S. Buzu*, alokacin da yake aiki tare da Alhaji Barau yasha wahala, domin bakinsu d’aya da manyan masu kud’i, gashi ya iya tsara magana, shiyasa duk yawancin shari’a shine yake nasara musamman ta masu kud’i, yasan yanda zai maida gaskiya ta koma k’arya, ta yanda babu wanda zai iya ganowa. 

Ra’eez yace lallai kace yanzu sai ya raina kanshi tunda Kawun ka ne samansa. Jabeer yace ai yanzu yayi sauki sosai, kasan dama idan kaga mutum yana yanda yaso ba’a bashi shugabanci bane, ai tamkar ka d’auki ajiya ne ka bama b’arawo, kaga dole idan kazo amsa ya baka, shiyasa wasu suke ganin da zama da munafuki gara zama da b’arawo. 

Dariya Ra’eez yayi yana fad’in wallahi Jabeer kana da abun dariya, gashi ka iya karin magana kamar wanda tsofaffi suka yaye, to ni dai ban fahimci abinda kake nufi ba. 

Murmushi Jabeer yayi yana fad’in ina nufin yanzu shine shugaba, dole abinda lauyoyi suka fad’a shi zaibi, domin yanzu kotu ce take tafiyar dashi ba shine yake tafiyar da kotu ba, kasan duk abinda lauya ya fad’a dashi kotu take zama ta duba kafin ta yanke hukunci, shiyasa nace maka yanzu yayi sauki, dole yake yanke hukuncin gaskiya, shiyasa yanzu mutane suke sara masa, gani suke shid’in mai gaskiya ne, musamman koda yana lauya ba’a tab’a kamashi da laifin cin amanar aikinsa ba, shiyasa yanzu duk inda kaje zakaji ana fad’in Alkalin babbar kotu yafi kowa iya aiki, dan haka mutane suke son kawo k’ara a wannan kotu, damma ana soke wasu amaida su k’ananan kotu. 

Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in lallai irin wad’an nan mutanan wahalar sha’ani garesu, domin sun riga sun gama saye zuk’atan mutane, duk yanda wani yaso ya fad’i wani aibunsu mutane bazasu yarda ba har sai an gabatar masu da babbar hujja akansu. 

Jabeer yace shiyasa ka zuba masu ido yafi, domin fad’a da aljani ba kyau, ko kace zakayi ma kaine a k’asa, domin zaka sa mutane su tsaneka ne kawai, shiyasa duk da nasan shid’in ba mai gaskiya bane dole na had’iye abuna nake binsa a yanda kowa yake kallonsa kafin ranar da Allah zai kamashi, wata kila a duniya wata kila kuma sai anje can. 

Ra’eez yace irin wad’an nan mutanan asirinsu ya tonu aduniya yafi dad’i, domin mutanan da suka basu gaskiya zasu ga komai da idanuwansu, sannan masu aikata makamancin laifinsu zasu hankalta, idan suna da rabon shiriya sai kaga sun shiryu, amma abarsu sai anje lahira ai sun bar baya da k’ura. 

Jabeer yace kai da kasan haka kenan, addu’ata d’aya Allah ya bayyana gaskiya, domin Kawuna yasha fad’a mani wata shari’a da sukayi wacce har yanzu bata wuce a zuciyar Kawu ba, saboda tare sukayi ta kuma shine yayi nasara, saboda irin hujjar daya gabatar ma kotu dole ne ta yanke hukunci, kuma Kawu yace ba hujjar gaskiya bace, sai dai shima bai da ikon k’aryatawa, domin an gabatar da ita ne amatsayin ta gaskiya, sune kad’ai suka san cewar ba ta gaskiya bace. 

Ra’eez yace shari’ar waye haka? Jabeer yace an dad’e fa, shari’ar wani marigayi daya rik’e shugaban Kwastam a garin nan, kaga na manta sunansa wallahi, amma dai naji Kawu na yana fad’in har yanzu direbansa da aka k’ullama sharrin yana nan a gidan yari, kai wallahi wata shari’ar sai alahira kaji, amma mutanan da suke zaune agidan yari masu gaskiya suna da yawa. 

Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in Allah ya kyauta, mu kuma ya bamu ikon tabbatar da gaskiya, amma aikin mu yana da had’ari sosai, idan mutum yaso zai nemi lahira dashi, idan kuma yaso sai ya tara abun duniya dashi. Jabeer yace wannan haka yake, muje muyi sallah naji an fara kira.

***

Bayan da suka tashi Ra’eez yayi sallama da Jabeer, bakin motarsa ya tsaya yana jiran fitowar Alkali. Yana nan tsaye sai gashi ya fito shida Brr. Bajinta suna tafe suna magana sai dariya sukeyi. 

Da wani irin kallo Ra’eez ya bishi yana jin wani zafi aranshi. K’arasowa sukayi Alkali yana fad’in Ra’eez yi hak’uri na tsayar da kai. Ra’eez yace ai bakomai. 

Brr. Bajinta yace ‘yallab’ai yau kana da babban bako kenan? Alkali yace wallahi kuwa, bara muje sai Allah ya kaimu. Brr. Bajinta yace Allah ya kaimu. Alkali yace Ra’eez bara na shiga gaba sai ka biyoni abaya ko. 

***

Tunda suka shiga unguwar Surelere idanuwan Ra’eez suka canza kala, gaba d’aya jijiyoyin kansa suka tashi, shigowarsu unguwar sai ya tuna masa da rayuwar Iyayensa. Runtse ido yayi lokaci guda suka kawo ruwa. 

Tunaninsa ya tsaya ne alokacin da yaga Alhaji Barau ya tsaya a k’ofar gidan da yake tunanin ya tab’a rayuwa acikinsa a shekarun baya, tabbas ko ba’a fad’a masa ba yasan wannan gidan Abbunsa ne daya gina da kud’insa wanda Abbu yayi masa wayau akan baya sonshi hakan yasa ya koma Apapa. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button