ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Tsayawa yayi har yaga motar Alhaji Barau ta shige ciki, tunani yayi ko dai ya tafi, dan bazai iya shiga gidan ba. Wata zuciyar ta bashi shawara daya daure yashiga, dole ya b’oye komai matuk’ar yana son gano gaskiya. 

Cike da gamsuwa da shawarar da zuciyarsa ta bashi ya kutsa kan motar cikin gidan, yayin da yake kok’arin saita kanshi. Alhaji Barau ya fito yana jiran fitowar Ra’eez. 

Sai da ya rufe motar kafin ya nufo wajen Alhaji Barau. Murmushi kwance a fuskarsa ya kalli Ra’eez yana fad’in bsimilla muje. Haka yabi bayansa yana kallon gefen gidan wanda Abbunsa yace b’angarensa ne zai gina idan yayi aure su zauna, tuni an gama gina wajen da alama b’angaren baki ne ko na yaransa maza. Girgiza kai Ra’eez yayi aranshi yana fad’in fenti kawai aka sake ma gidan amma komai nashi yana nan. 

Tunaninsa ya dawo alokacin da Alhaji Barau yake gaisawa da mai aikin gidan. Risnawa Ra’eez yayi yana gaishe da mai aikin daya fito daga gidan. 

Har ciki suka shiga bakinsa d’auke da sallama, sai dai babu kowa afalon sai TV da takeyi ita kad’ai. Kallonsa Alhaji Barau yayi yana fad’in zauna Ra’eez bara nayima mutanan gidan magana. 

Zama yayi yana k’are ma gidan kallo. Da sauri yasa hannu ya goge kwallar data zubo masa, duk yanda yaso ya tsaidata kasawa yayi dole sai da suka zubo, hakan yasa yayi saurin goge su. 

Motsin da yaji ne yasa shi kallon matattakalar benen, wata mata ce ya gani sun jero da Alhaji Barau sai murmushi take suna magana. Tana k’arasowa falon ta kalli Ra’eez tana fad’in lallai Alhaji yau muna da babban bako, ka kyauta daka kawo manishi, dan tunda ka bani labarin yanda ya tafiyar da shari’ar su Amina naji ya burgeni, sannu da zuwa Ra’eez. 

Zamewa Ra’eez yayi yana gaisheta. Zama tayi tana amsawa. Alhaji Barau yace ai Ra’eez yana da kirki, jinsa nake tamkar d’ana. Hajiya Hauwa tace nima haka kawai naji ya kwanta mani, shiyasa nace maka naji dad’i daka kawo manashi. 

Alhaji Barau yace ina *Raheenatu* take? Hajiya tace tana ciki, bara na kirata ta kawo masa abunsha. Ra’eez yace Hajiya kibarshi akoshe nake tafiya ma zanyi. Alhaji Barau yace ai ba haka mukayi da kai ba, dole kaci abinci ko kad’an ne. 

Duk’ar da kai Ra’eez yayi bece komai ba. Wucewa Hajiya tayi tana fad’in ina ma za’ayi haka ai har abinci sai kaci. Bayan ta kira Raheena ta wuce kicin. 

Suna zaune Raheena ta fito, tun kafin ta k’arasa shigowa falon k’amshin turarenta ya bud’e falon, a hankali Ra’eez ya d’ago kanshi domin yaga wanda yashigo da k’amshin. 

Ido suka had’a da Raheena alokacin da ta fito sai kwarkwasa takeyi, wata doguwar rigace ajikinta mai kyan gaske, d’inkin yayi kyau domin tabi jikinta, kanta d’aure da d’ankwali fuskarta tasha kwalliya, sosai kayan suka matseta sai yanga takeyi tana taubar cingam ko mayafi babu. 

Kicin ta wuce, ta jima kafin ta fito hannunta d’auke da faranti babba. Ra’eez kuwa tunda ya kalleta ya d’auke kai. Alhaji Barau ne ya tashi yana murmushi yace bara nashiga daga ciki ka saki jikinka kaci abinci nan ma gidan ku ne, yanzu zan fito, Raheena ki tayashi fira. 

‘Daga kai tayi tana murmushi. A tare da Hajiya Hauwa suka haura sama. Zama Raheena tayi tana fad’in barka da zuwa da fatan kazo lafiya? Ra’eez yace lafiya lau. 

Lemu ta zuba masa ta mik’a masa tana fad’in bismillah. Amsa yayi yana fad’in nagode. Matsowa tayi kusa dashi tana fad’in naji labarin shari’ar daka gudanar gaskiya kayi kok’ari, sosai naji dad’i fa. 

Ra’eez yace nagode. Shiru tayi ta tsura masa ido, tunda take arayuwarta bata tab’a ganin namiji mai kyansa ba, haka tunda Dadynta yace mata tayi kwalliya zai zo da bako take jin farin ciki, ashe wanda zai zo had’ad’d’an gaye ne, gaskiya dole ma Dady ya aura mata shi don ayanzu kad’ai jitake bazata iya rabuwa dashi ba, idan ko yaki amincewa da ita. zata iya shiga wani hali. 

Gyaran murya Ra’eez yayi ganin irin kallon da take masa, da sauri ta d’auke idonta tana murmushi. Ra’eez yace zaki iya tafiya nagode. Raheena tace haba Yayana baka son na taya ka firar? Kauda kai yayi yana fad’in kaina yana mani ciwo ne. 

Murmushi tayi tana fad’in bara na kawo maka magani. Kai ya girgiza yana fad’in bana shan maganin ciwon kai kawai surutu ne bana so. Tashi tayi tana fad’in nayi shiru bara na zauna acan, kallon ka ya fiye mani surutun ma. 

Zama tayi a saman kujera tana binshi da kallo. Kauda kai yayi yana jan tsaki a zuciyarsa dan har itama haushinta yakeji gashi bata da kamun kai. 

Fitowar Alhaji Barau ce tasa ya d’an saki fuska. Alhaji Barau yace Ra’eez har ka sha ruwan ko? Ra’eez yace nasha tafiya ma zanyi. Hajiya Hauwa da ta sauko take fad’in ga abinci fa zamuci. 

Mik’ewa Ra’eez yayi yana fad’in nagode Hajiya ana jirana a gida ne. Da sauri Raheena tace kana da aure ne? Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad’in beda aure kila dai abokinsa ne yake jiransa. 

Ajiyar zuciya ta saki tana fad’in har naji dad’i Dady. Hajiya Hauwa tace Oh! ni Hauwa’u, wallahi Raheena baki da kunya. Alhaji Barau yace nagode Ra’eez, amma wata rana zaka zo muci abinci tare. 

Ra’eez yace insha Allah. Sallama yayi masu sai godiya suke masa. Alhaji Barau ne ya kalli Raheena yana fad’in bazaki rakasa mota ba. Da sauri tayi gaba tana fad’in na d’auka kai zaka rakashi ai Dady. Hajiya Hauwa tace waye k’arami anan ai dole kece zaki rakashi. 

Har bakin mota ta rakashi, bayan ya zauna zai rufe tayi saurin rik’e murfin, langwab’ar da kai tayi tana fad’in Yayana sai yaushe kuma? Kau da kai yayi yana fad’in nima ban sani ba. 

Shagwab’e fuska tayi hada dira k’afa tace kai dan Allah Yayana! Murmushi yayi dan ta basi dariya. Kallonta yayi yana fad’in shikenan zan samu lokaci nazo. Murmushi ta saki tana fad’in nagode Allah ya kaimun kai gida lafiya. 

Ra’eez yace amin nagode. Rufe masa k’ofar tayi. Sai da ya fita daga gidan kafin ta shige ciki. A mota Ra’eez sai jan tsaki yakeyi akan abinda Raheena takeyi, sai kace ba mace ba, wai nan har karatu tayi. Murmushi yayi yana shafa fuskarsa, a hankali ya furta Alhaji Barau zan bar maka tabo biyu kuwa. 

***

Da tsalle tashiga gidan ta rungume Hajiya Hauwa tana dariya. Alhaji Barau yace ikon Allah lafiyar ki kuwa? Hajiya Hauwa tace da alama anyi nasara. 

Alhaji Barau yace ai tunda na ganshi nayi ma Raheena sha’awarsa, domin nasan shine irin zab’inta. Hajiya Hauwa tace wallahi nima ya kwanta mani, yaro sai kace jinin larabawa, jikinsa na hutu ne, da gani kasan ya fito daga babban gida, dan ya tsumu a cikin daula. 

Raheena tace wallahi Dady ina matuk’ar sonshi dan Allah ka aura mani shi zan iya shiga wani hali idan na rasashi. Saurin rufe mata baki Hajiya Hauwa tayi tana fad’in haba shalele, kima daina fad’ar haka, ke d’aya muke da ita mace, sannan kece ta gaban goshin mu, dole ma ki auresa. Sake rungumeta tayi tana fad’in nagode Momy nah. 

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button