ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Sunana *Malan Sani*, kuma sana’ata shine tukin mota. 

*Brr. Barau*… Malan Sani meye alak’ar ka da Alhaji Maiwada? 

*Malan Sani*… Bamu da wata alak’a ta jini tsakanin mu, sai dai ina masa aikin tuki, nine direbansa tun farkon daya fara aiki a garin nan. 

*Brr. Barau*… Zaku kai shekara nawa tare? 

*Malan Sani*… E to gaskiya mun dad’e dashi, a kalla zamuyi shekara sama da biyar atare. 

*Brr. Barau*… Idan na fahimceka kun dad’e sosai har kun zama ‘yan uwan saboda sabo? 

*Malan Sani*… Maganar gaskiya Alhaji ba Ubangidana bane kad’ai, ina jinsa tamkar Yayana da muka fito ciki d’aya, domin Alhaji ya gama mani komai arayuwa. 

*Brr. Barau*… Malan Sani, kotu taji irin yanda ka d’auki Alhaji Maiwada, sai kuma gashi duk irin alkhairin da yayi maka hakan bai hanaka kashe shi ba kuma ka keta ma Iyalinsa haddi… 

Ina da ja ya mai shari’a, ya kamata abokin aikina ya kula da maganar da yake jifar Malan Sani da ita, har yanzu ba’a tabbatar shine ya aikata kisan ba zarginsa akeyi, be kamata yarik’a masa irin wannan tambayar ba. Nagode. 

*Alkali*… Brr. Barau ka kiyaye. Risnawa Brr. Barau yayi yana fad’in za’a kiyaye. 

*Brr. Barau*… Malan Sani aranar juma’a da misalin k’arfe bakwai da ‘yan mintuna kana ina? 

*Malan Sani*… Ina tare da Alhaji a wannan lokacin muna kan hanyar mu ta zuwa gida. 

*Brr. Barau*… Ko Malan Sani zai fad’ama kotu abinda ya faru a wannan lokacin da suke kan hanyar gida? 

*Malan Sani*… E to muna cikin tafiya sai tayar motar mu tayi faci, muna kok’arin fita sai ga wasu mutane kamar daga sama, kafin suzo wajen mu sai Alhaji yace na tafi gidansa na tafi ta matarsa gidana saboda yana tsoron wani abu ya faru da ita, shine na tafi ashe kashe shi zasuyi. 

*Brr. Barau*… Murmushi yayi yana fad’in, Malan Sani kamar yanda ka fada, kace kuna hanyar ku ta zuwa gida ne, wanda mun san cewar Alhaji Maiwada yana zaune a unguwar Apapa ne, sai gashi kun taso daga wajen aikinsa kun canza hanyar da zata sada ku da gida, ko zaka fad’a mana dalilin da yasa bakubi hanyar da kuka saba bi ba. 

*Brr. Kamal*…. Ina da ja ya mai shari’a, wannan tambayar bata da alak’a da wannan shari’ar, domin kowa yana da ikon bin inda yakeso domin zuwa gida. 

*Alkali*….. Korafi bai karb’u ba, dole zai amsa wannan tambayar domin tana da alak’a da wannan shari’ar. Brr. Barau kacigaba. 

*Brr. Barau*…. Risnawa yayi kafin yace kotu tana sauraron ka. 

*Malan Sani*… Haka ne, bayan fitowar mu daga wajen aiki sai muka had’u da wani yaro yana neman taimako, sai Alhaji yace mu d’aukeshi, bayan ya fad’a mana unguwar da zaije muka tafi, sai dai da muka isa a bakin hanya muka ajeshi saboda nasan layin beda kyau, bayan mun juya zamu koma hanyar mu ta zuwa gida shine mukayi faci har wannan abun ya faru. 

*Brr. Barau*… Girgiza kai yayi yana fad’in bayan ka isa gida ya akayi ka fito ba tare da Matar Alhajin ba? 

*Malan sani*…. Bayan na shiga gidan muka gaisa da Madu mai gadin gidan, anan nake fad’a masa zanshiga ciki, bayan na shiga ciki mun gaisa da Hajiya, ina kok’arin na fad’a mata abinda Alhaji yace sai kawai mukaga wasu mutane sun shigo fuskarsu a rufe, Hajiya tana kok’arin magana sai kawai wani ya kwad’a mata sanda, nan take ta fad’i sai ganin jini nayi yana fita daga k’afarta, kafin nayi wani yunku’ri suka hura mani wani abu, tun daga lokacin ban sake sanin abinda yake faruwa ba, domin kaina yayi nauyi, ina kallo suka sa hannunta a wuyana suka yakusheni da farcenta, sai suka turoni waje, bayan na fito wajen gida suka sani a mota muka tafi, suna ajeni k’ofar gidana suka tafi, iya abinda na sani kenan amma wallahi ba nine na kashe Alhaji ba, haka kuma banyima Hajiya abinda ake zargina dashi ba. 

*Brr. Barau*… Malan Sani zaka iya tafiya. Ya mai shari’a inaso nayima Maigadin gidan Alhaji wasu tambayoyi. Kotu ta baka. 

*Brr. Barau*… Kotu zata so taji sunan ka da aikin ka. 

*Sunana Amadu wanda akafi sani da Madu*, kuma aikina shine gadi agidan Alhaji. 

*Brr. Barau*… Ka kai shekara nawa agidan Alhaji kana masa aiki? 

*Madu*…. Zanyi shekaru kusan sama da shidda tare dashi. 

*Brr. Barau*….. Ko akwai wata matsala da kasani wadda take faruwa atsakanin Malan Sani da Alhaji a zaman su? 

*Madu*… Gaskiya tun had’uwar Alhaji da Malan Sani basu tab’a samun sab’ani ba, asalima Alhaji yana kyautata masa sosai, domin hatta da karatun d’iyarsa shine ya d’auki nauyi, gidan da yake ciki ma Alhaji ne ya cika masa ya sayeshi, gaskiya ban tab’a ganin sun samu matsala ba. 

*Brr. Barau*…. Aranar juma’a a wane yanayi Malan Sani yashigo gida? 

*Madu*…. E to gaskiya yashigo ba’a yanayin dana saba ganinsa ba, ina zaune ya buga mani k’ofa, bayan na bud’e sai na ganshi wani iri idanuwansa sunyi ja hannunsa rik’e da wata bak’ar jaka wanda bansan meye aciki ba, sai na tambayeshi ina Alhaji sai yace mani akwai matsala bara ya fito daga ciki, ban tsaya tambayarsa ba na barshi yashiga kasancewar nasan amintaccen Alhaji ne, ina zaune sai naji kamar ihun Hajiya, amma sanin Malan Sani yana ciki sai banyi yunkurin shiga ba, ba’a dad’e ba sai naga Malan Sani ya fito jikinsa duk jini yana tafiya kamar a buge, dana tareshi ina tambayarsa sai kawai ya ture ni har sai da na faad’i, kafin na tashi ya fice, ina lek’awa sai dai kurar mota na iske babu shi, sai nayi saurin shiga ciki, Hajiya na iske a kwance cikin jini hakan yasa nayi saurin fitowa domin na sanar da mutane. Iya abinda na sani kenan. 

*Brr. Barau*…. Madu mungode zaka iya tafiya. Ina so zanyima Inspector Bello tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. 

*Brr. Barau*…. Kotu zata so taji sunnanka kuma kayi mata bayanin binciken da kukayi. 

*Sunana Bello Kabir*, nine d’an sandan da yake kula da case d’in mutuwar Alhaji Maiwada. A ranar juma’a mun samu waya daga wasu daga cikin ma’aikatan mu da suka fito aiki cewar sun samu motar Alhaji Maiwada tare da gawarsa aciki, bamu b’ata lokaci ba mukaje wajen, bayan an d’auke gawarsa daga motar sai muka binciki motar, mun samu sirinji da kwalbar wata allura a ciki, haka muka had’a komai muka nufi asibiti da gawar domin likitoci suyi bincike akai.

Bayan munje mun kama Malan Sani sai na koma asibiti, bayanin da likita yamun akan mutuwar Alhaji yasa a jiya na koma gidan Malan Sani domin yin wani bincike, a binciken da mukayi mun samu wata bak’ar jaka b’oye a d’akinsa acan k’asan gado wacce take d’auke da muk’udan kud’i a kalla zasu kai milliyan biyar, a cikin jakar muka samu irin kwalbar allurar da muka samu a motar Alhaji. Wannan sune takardun binciken da akayi ga kuma jakar. 

Cusa kai Halima tayi cikin k’afafuwanta tare da sake sakin wani irin kuka, tunda ‘yan sanda suka zo jiya suka gano wannan jaka a d’akin Malan Sani take cikin tashin hankali, bata san lokacin da aka aje jakar ba, ta tabbata Malan Sani ba zai aje wannan jaka ba, kuma ita tunda aka tafi da Malan Sani bata sake shiga d’akinsa ba sai kawai jiya da aka zo bincike taga an fito da jaka ashe wannan abun ne aciki, shikenan tasan babu wanda zai fitar da Malan Sani sai Allah. 

*Brr. Barau*… Mungode zaka iya tafiya. Ina so zanyima likitan da yayi binciken gawar Alhaji tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. Likita ya fito gaban kotu. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button