ALKALI NE Page 31 to 40

Wani abokin aikin likitan ne ya mike yana fad’in likitan yayi waya yana hanya ya taho motarsa ta samu matsala amma ya kusa k’arasowa.
Dafe kai Brr. Barau yayi, kada dai likitan bazai zo ba gashi akwai abubuwa masu muhimmanci awajensa, dole ya nemi hanyar fita yanzu ko hutu ne ya nema.
Risnawa yayi yana fad’in ya mai shari’a ina rokon wannan kotu data bada izinin hutu ko na rabin sa’a ne domin akwai abinda za’a kawo mai muhimmanci wanda ya shafi wannan shari’ar.
Alkali yace muje ga sheda ta gaba kafin likita ya k’araso. Risnawa Brr. Barau ya sakeyi yana fad’in ina neman alfarmar kotu ta bada wannan hutu saboda wani uzuri daya taso mani yanzu.
Jinjina kai Alkali yayi yana fad’in kotu zataje hutun mintuna ashirin, idan be iso ba zamu cigaba da gabatar da shari’a. Buga tebur yayi.
Girgiza kai Alhaji Mansur yayi hawaye suka zubo masa, har cikin ranshi yana zargin wannan *ALKALIN*. Tashi yayi ya fita zuciyarsa na zafi, ga tunanin Ra’eez wanda har yanzu besan Mahaifinsa ya rasu ba, tsoro yake kada wani ya fad’a masa tunda Alhaji babban mutum ne mutuwarsa bazata b’oyu ba, dole gobe idan suka koma yaje ya d’aukoshi.
Ur’s.
Nabeelert Lady????*Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣8⃣
A waya Brr. Barau ya kira likita, hak’uri ya bashi yace gashinan zuwa. Sosai Brr. Barau ya sake nana ta masa abinda zaice kafin ya kashe wayar.
**
Bayan an dawo hutu Alkali ya bada izinin acigaba da gabatar da shari’a, tambaya yayi idan likitan ya iso? Tashi Brr. Barau yayi yana fad’in ya iso ya mai shari’a, inaso nayi masa tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama, likita ya fito gaban kotu.
*Brr. Barau*… Kotu zata so taji sunan ka da kuma bayanin binciken da kayi.
*Sunana Aliyu Sani*, nine likitan da yayi binciken gawar Alhaji Maiwada, a binciken da nayi mun samu shatin hannu wanda akayi amfani dashi wajen shak’e Alhaji kafin aka masa wannan allurar da ‘yan sanda suka kawo mana wacce aka samu a motarsa, ita dai wannan allura tana da had’ari sosai, domin tana kisa a cikin lokaci kad’an, Alhaji yaci matuk’ar wahala alokacin da akayi masa allurar, domin alokacin da aka kawosa tuni ya dad’e da rasuwa, haka wuyansa ya kumbura kuma yayi ja, gaba d’aya rahoton dana rubuta yana wajen Inspector Bello na had’a masa.
*Brr. Barau*… Jinjina kai yayi yana fad’in ko allurar da aka samu a cikin jakar da take d’akinsa tayi dai-dai da wadda aka samu a motarsa?
*Likita*… Kwarai kuwa, dukkansu iri d’aya ne.
*Brr. Barau*… Mungode likita zaka iya tafiya. Ina so zanyi tambaya ta k’arshe ga likitan da yake kula da Matar Alhaji Maiwada idan kotu ta bani izini. Kotu ta baka dama.
*Brr. Barau*.. Kotu tana so taji sunan ka da kuma bayanin binciken daka gudanar akan matar Alhaji.
*Sunana Saddik Mansur*, nine likitan da nake kula da Hajiya Bilkisu matar Alhaji Maiwada, bayan da ‘yan sanda suka kawo ta sai muka gano cikin da yake jikinta ya zube sakamakon fad’uwar da tayi asamanshi da k’arfi, haka kuma a rahoton da aka bada na cewar fyad’e ne yayi silar zubewar cikinta maganar gaskiya babu alamun wani fyad’e, sanadiyar bugun da akayi mata akai yasa ta faad’i saman cikin wanda ya jawo zubewarsa, sannan taji abinda ya firgita ta, sannan sakamakon bugun da akayi mata akai ya jawo ta samu tab’in hankali wanda yanzu haka tana kwance tana karb’ar taimako daga gare mu, sai bincike na k’arshe shine mun samu jini a cikin farcenta, bayan da muka auna muka gano sakamakon duk na had’a na bama ‘yan sanda. Wannan shine abinda na sani.
*Brr. Barau*… Likita mungode zaka iya tafiya.
Murmushi yayi yana fad’in ya mai shari’a Malan Sani yayi nasarar kashe Alhaji Maiwada ne ta hanyar daya shirya, tun daga kisan da yayima Alhaji ya tabbatar mana cewar ya dad’e yana shirya yanda hakan zata kasance, domin a daren juma’a bayan sun taso daga wajen aiki sai Malan Sani yayi dabara ya canza masu hanyar da zata sadasu zuwa gida, yayi amfani da faci ya tsayar da motar domin ya fita ya duba, da haka ne ya shiga bayan mota da niyar d’aukar wani abu kasancewar Alhaji baya zama a baya sai gaban mota, ta baya ya shakoshi kafin ya caka masa allura a wuyansa kafin ya d’auki jakar kud’in Alhaji yayi saurin barin wajen.
Yayin da yayi kok’arin hayk’ema Matar Alhaji sunyi kokowa da ita domin an samu shatin faratan ta a wuyansa, sannan jinin jikin farcenta yayi dai-dai da jinin Malan Sani, sannan an samu hoton hannunsa a nata, ganin zata tona masa asiri sai ya buga mata abu akai, ganin ta suma ya d’auka mutuwa tayi shiyasa yayi saurin barin wajen yana tunanin ya gama da ita.
Wad’annan sune sakamakon da aka samu a wajen likita da duk wata sheda da zata tabbatar ma kotu Malan Sani shine ya aikata wad’an nan laifukan da ake zarginsa dashi. Ina rokon wannan kotu mai albarka da tayi amfani da wad’annan hujjoji domin ta yanke ma Malan Sani hukuncin da yayi dai-dai dashi. Nagode.
Gaba d’aya kotu ta d’auki kus-kus kowa da abinda yake fad’a. Brr. Kamal gaba d’aya jikinsa yayi sanyi domin yasan sun fad’i, duk wata sheda Brr. Barau ya gabatar da ita, kuma ko waye dole ya yarda da abinda aka gabatar saboda sheda ce tabbatacciya, amma dole ya tashi yayi wani abu ko dan kada aga gazawarsa.
Bubbuga tebur Alkali yayi, bayan anyi shiru Alkali yace Baristan da yake kare wanda ake k’ara ko kana da abinda zaka fad’ama kotu? Tashi Brr. Kamal yayi cike da kwarin guiwa yace ina dashi ya mai shari’a, ina so nayi ma Maigadin gidan Alhaji tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama maigadi ya fito.
*Brr. Kamal*… Madu a cikin bayanin daka bayar naji kace lokacin da Malan Sani ya shigo gidan ya fad’a maka akwai matsala, sannan kace kaga idanuwansa sunyi ja, sannan kaga bak’ar jaka a wajensa, shin ko waccan jakar da aka gabatar tayi dai-dai da wadda ka gani? Sannan daya shigo kaga yanayin maye atare dashi? Sannan alokacin da kace kaji ihu meyasa bakayi saurin shiga ciki ba amatsayinka na wanda yake kula da mutanan gidan? Kace Malan Sani ya fito da jini a jikinsa, sannan ka ganshi acikin yanayi na maye, amatsayinka na maigadi ya akayi ka barshi har ya fita daga gidan ba tare da ka rik’esa ba?
*Madu*…. E to gaskiya lokacin daya shigo babu yanayin Maye a tare dashi, kawai dai baya cikin natsuwarsa, alamu sun nuna kamar yana cikin tashin hankali domin jan da idanuwansa sukayi sun nuna alamun kamar wanda yayi kuka. A lokacin da naji ihu kuma dalilin da yasa ban shigaba saboda nasan Malan Sani yana ciki, kuma nasan amintaccen gidan ne, alokacin da ya fito kuma nayi kok’arin tareshi amma sai ya ture ni, kuma tabbas da yanayin maye ya fito, sai dai kafin na tashi ya fice, saboda gaskiya jikina ne yayi sanyi saboda ganin abinda ban tab’a zato ba, hakan yasa na kasa yunkurin rikeshi da kyau. Sannan kuma wannan jakar tabbas irin tace na gani a hannunsa, kuma nasan ta Alhaji ce domin koni nasha d’aukarta idan ya fito zai fita domin nasan jakarsa ce da yake saka kamfutarsa.