ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

*Brr. Kamal*…. Kace jakar kamfutarsa ce, kenan lokacin da Malan Sani ya shigo da ita kamfutarce aciki? sannan kace ya fito cikin yanayin maye, shin ya fito da jakar ko kuma be fito da ita ba? 

*Brr. Barau*… Ina da ja ya mai shari’a, duk da Madu yace yaga Malan Sani ya shigo da jaka ta kamfutar Alhaji ai be zama dole ace kamfutar bace aciki tunda alokacin be bud’a masa ba, ya kamata abokin aikina yasan irin tambayar da zaiyima mai bada sheda. Nagode. 

*Alkali*… Brr. Kamal ka gyara yanayin tambayarka. Risnawa yayi yana fad’in zan kiyaye. 

*Brr. Kamal*… Madu kotu tana sauraronka shin kaga Malan Sani ya fito da wannan jakar? 

*Madu*…. A gaskiya ban lura da hannunsa ba, saboda yana fitowa naga jini a jikinsa sai hankalina ya tashi hakan yasa bazan iya cewa ya fito da jaka ba. Iya kar abinda na sani kenan. 

*Brr. Kamal*.. Jinjina kai yayi yana fad’in mungode zaka iya tafiya. Ina so nayima Malan Sani wasu tambayoyi idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. 

*Brr. Kamal*… Malan Sani kace alokacin da aka tare ku Alhaji yace ka tafi domin kaje ka tafi da iyalinshi gidan ka, shin ko zaka fad’ama kotu abinda kuka tattauna da yasa yace kaje ka tafi da matarsa. 

*Malan Sani*… Tabbas Alhaji shine yace naje na tafi da Hajiya, sannan ya bani jakar kamfutarsa yace na tafi da ita saboda mutanan da suka taremu kada su ansheta dan akwai abubuwa masu muhimmanci aciki. 

Hannu Brr. Barau yasa yana gyara zaman gilashinsa jin abinda Malan Sani ya fad’a, kada fa aje allura ta tono galma, kada ace Malan Sani ya b’oye wata shedar da zata tabbatar da abinda sukayi. 

*Brr. Kamal*…. Malan Sani kace akwai abubuwa masu muhimmanci acikin kamfutar Alhaji hakan yasa ya baka ka tafi da ita, shin ko zaka fad’a mana wani abu wanda ka sani idan Alhaji ya sanar da kai. 

*Malan Sani*… Tabbas akwai masu neman rayuwar Alhaji, kuma hakan ya faru ne saboda sun gano yasan wani sirri nasu akan abubuwan da sukayi mashi, kuma ya shirya komai yana jiran litinin tayi domin ya shigar da k’ara saboda ya samu duk wata sheda da zata tabbatar da abinda sukayi domin shedar bidiyo ce da maganganunsu aciki, wanda suka san duk abinda yayi hakan yasa suka shirya kashe shi. Wannan dalilin ne yasa ya bani kamfutar yace na tafi da ita. 

*Brr. Kamal*… Ko zaka iya fad’a mana su waye suke kokarin kashe shi? 

*Malan Sani*… E to wad’an da aka turo ban san su ba, amma mutanan da suke cikin kamfutar ‘yan tawagar Alhaji Marusa ne kuma shine babban su domin shine abokin takun sak’ar Alhaji. 

A zabure Brr. Barau ya tashi yana fad’in ya mai sharia wannan magana da Malan Sani yake fad’a ba gaskiya bane, yariga da yasan komai na Alhaji hakan yasa zeyi amfani da wannan damar ya kare kanshi domin ya ga beda wata hanyar tsira, Malan Sani yasan duk wani sirri na Alhaji, yasan cewar sun samu sab’ani da Alhaji Marusa alokacin baya, hakan yasa zaiyi amfani da wannan damar ya sako Alhaji Marusa a cikin wannan shari’ar, ina so kotu tayi watsi da wannan gurguwar hujjar ta Malan Sani tayi duba da hujjar zahiri da aka gabatar mata domin ta yanke masa hukunci, domin Malan Sani zai b’atama kotu lokaci ne kawai, kuma idan beyi hankali ba Alhaji Marusa yana da damar neman hakkinsa akan b’ata masa suna da yake kok’arin yi. Nagode. 

*Brr. Kamal*… Ya mai shari’a maganar Malan Sani tana kan hanya, babu wanda besan alak’ar da take tsakanin Alhaji Marusa da Alhaji Maiwada ba, kuma tabbas hakan zata iya kasancewa domin Alhaji Marusa yana takun sak’a da Alhaji Maiwada. Inaso wannan kotu da tayi duba da maganar Malan Sani, kada tayi saurin yanke hukunci, abashi dama domin ya tabbatar da abinda ya fad’a. Nagode ya mai shari’a. 

Hayaniya ce ta cika kotun. Bubbuga tebur Alkali yayi kafin akayi shiru. Kallon Malan Sani yayi yana fad’in Malan Sani ko kana da shedar da zaka tabbatar ma kotu abinda ka fad’a gaskiya ne? Duk’ar da kai Malan Sani yayi hawaye suna zubo masa yace bani da sheda ya mai shari’a domin mutanan da suka shiga gidan Alhaji sune suka amshe kamfutar da shedar take ciki. 

Ajiyar zuciya Brr. Barau ya saki jin abinda Malan Sani ya fad’a. 

Girgiza kai Alkali yayi yana fad’in kowa ce kotu tana amfani ne da kwakkwarar hujja kafin ta yanke hukunci, dan haka wannan kotu baza tayi amfani da abinda ka fad’a ba amatsayin hujja. Brr. Kamal idan kana da sauran tambaya kotu tana sauraronka. 

Jiki a sanyaye Brr. Kamal yace bani da ita ya mai shari’a. Komawa yayi ya zauna yana jin d’aci aranshi, tabbas yasan akwai munakisa acikin wannan shari’ar, amma saboda basu da hujja dole suyi hakuri Allah zai saka masu. 

*Alkali*… Brr. Barau kana da sauran abinda zaka fad’ama kotu? Tashi yayi yana fad’in bani da sauran abun fad’a, ina so wannan kotu da tayi gaggawar yanke ma Malan Sani hukunci saboda zaluncin daya aikata. Nagode. 

Rubutu Alkali yayi kafin yace kotu zataje hutu na rabin sa’a. Bubbuga tebur yayi kowa ya tashi. 

Zamewa k’asa Malan Sani yayi yana sakin kuka mai tsuma zuciya. Da sauri Alhaji Mansur da su Halima sukayo wajensa.

Ur’s. 

Nabeelert Lady[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

1⃣9⃣

Hannu Alhaji Mansur yasa ya kamo Malan Sani yana fad’in kayi hak’uri Malan Sani, Allah yana tare da kai, koda sunyi nasara akan ka yanzu wallahi baza suyi nasara akan ka ba ranar lahira, Allah yasan komai, kuma yana kallon su, shine kad’ai zai saka maka, zuciyata tana mani wani tunani akan wannan Alkalin, sai dai bana so nayi zarginsa kada Allah ya kama ni da laifi, a gaskiya daga farko yanda naga yana yawan goyon bayan Brr. Barau sai nake tunanin ko an bashi cin hanci ne, amma daga baya sai na gano ko wane Alkali hakan zaiyi, domin kotu da sheda take amfani, da yawan Alkalai suna yanke hukunci bisa hujjar da aka gabatar masu, ko da hujjar ta k’aryace matuk’ar aka aminta da ita suna amfani da ita, dan haka kayi hak’uri Allah zai saka maka. 

Hannu Malan Sani yasa ya goge ido shi yana fad’in bakomai Alhaji, wallahi tun ba yau ba na sadak’as, nasan dole irin wannan hukuncin ya hau kaina, shiyasa tunda farko ban tsaya b’atama kaina lokaci wajen fad’ama Brr. Barau komai ba daya tambaye ni, ai kunga alokacin banyi maganar dalilin da yasa Alhaji ya bani kamfutarsa ba, ban kawo komai na abinda nasan sunyima Alhaji ba, saboda nasan kona kawo bani da hujjar tabbatar da hakan, saboda Brr. Kamal ne yasa na bud’e baki nayi magana, shima bana so yaga yana mani kok’ari amma naki bashi had’in kai, amma kaga yanzu da yasan babu hujja zai hak’ura, wallahi na d’auki k’addarata, fatana Allah ya bani ikon cinyeta. 

Cike da tausayi Alhaji Mansur yace amin Malan Sani. Cikin kuka Halima tace nikam Malan zan tafi gida, bazan iya tsayawa a yanke maka hukunci ba, ina tsoron binda zai faru dani, bana so muyi asarar abinda yake ciki na. 

Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad’in tunda na ganki naji rashin dad’in zuwanki, kinsan baki da lafiya, kuma nasan matuk’ar aka yanke mani hukunci wani abun zai iya faruwa da ke, dan Allah ki koma gida, kinga an kusa tashin su Rumaisa idan ta koma gida zata iske babu kowa, ki kwantar mata da hankali, bana so tasan abinda yake faruwa har sai ta k’ara hankali. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button