ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Alhaji Mansur yace bara mu rakata ta tafi hakan zaifi, dama tace tana son zuwa shiyasa muka taho da ita. Malan Sani yace akwai kud’i a inda nake ajewa kiyi amfani dasu, tunda kina sana’ar cikin gida ki k’ara jari nasan Allah bazai tozarta ki ba. Kai kawai ta d’aga tayi waje da sauri. 

***

Bayan kowa ya dawo Alkali yashigo, nan kowa ya natsu. Zama yayi yana gyara takardu. Kotu tayi tsit tana jiran abinda Alkali zai yanke. 

*Alkali*… ‘Dago kai yayi yana fad’in bayan dogon bincike da kwararan hujjoji da aka gabatar agaban wannan kotu, kotu tayi dogon nazari akansu kuma ta tabbatar da ingancin su, domin duk abinda aka gabatar mata babu wanda yake na bogi, an tabbatar cewar an samu allurar da akayima Alhaji Maiwada agidan Malan Sani, sannan an tabbatar da hoton hannun jikin wuyan Alhaji yayi dai-dai dana Malan Sani, haka zalika an tabbatar da hoton jikin hannun matar Alhaji yayi dai-dai dana Malan Sani, sannan jinin da yake jikin farcenta yayi dai-dai dana Malan Sani, bayan haka Malan Sani ya gaza kawo ma kotu wata hujja da zata tabbatar da abinda ya fad’a gaskiya ne, dan haka kotu zata yanke hukunci. 

*A k’arkashin penal code sashe na 302,da 201,da 180, da 340 sashen kisa amfani da makami ko wani abu, bisa la’akari da wannan sashe na kundin tsarin mulki na k’asa penal code, wannan kotu ta yanke ma Malan Sani hukuncin d’aurin rai da rai agidan yari, sannan zai biya tarar naira dubu d’ari biyar ga Iyalan Alhaji amatsayin cin zarafinta da yayi na yunk’urin haike mata, haka zalika zai biya diyya ga Iyalan Alhaji idan suna da buk’atar hakan. Kottttt!!!!.* 

Gaba d’aya mutanan kotun suka mike kowa da abinda yake fad’a, wasu suna yabama Alkali da Brr. Barau abisa kok’arin da sukayi, yayin da wasu suke ganin gaskiyar Malan Sani. Haka kowa ya fita ‘yan sanda suka taso Malan Sani wanda hawayen idanshi suka k’afe ya koma yin kukan zuci. 

Alhaji Mansur kasa motsi yayi daga inda yake, gaba d’aya jiyake kamar amafarki abubuwan suke faruwa. Maman Labiba kuwa kuka kawai takeyi. 

Alhaji Musa ne da Alhaji Usman suka k’araso wajen Alhaji Mansur, kamoshi Alhaji Musa yayi suka fito waje. Jingina sukayi da mota Alhaji Musa yana fad’in sai hak’uri Alhaji, Allah kad’ai yasan gaskiyar wannan al’amarin, domin har cikin zuciyata na kasa yarda da abinda ya faru, na jima da sanin Malan Sani haka kawai nake jin bazai iya aikata abinda akace yayi ba. 

Alhaji Usman yace wallahi kaji na rantse maka banyarda da abinda aka gabatar ma kotu ba, kawai babu yanda zamuyi ne, koda zamuje kotun da tafi wannan iya hukuncin da za’a zartar kenan, saboda ko waye aka bama wannan shedun dole ya amince dasu, mu da mukasan hakan bazai yuwu ba mu kad’ai zamu iya k’aryatawa, amma an cutar da Malan Sani, domin nasan waye Alhaji Marusa, zai iya komai akan kud’i, tunda naji sun fara takun sak’a da Alhaji Maiwada nasan ba zai barshi haka ba, domin duk wani ma’aikacin kwastam da za’a kawo nan matuk’ar mai gaskiya ne Alhaji Marusa shine yake silar barinsa garin nan, saboda aminin Mr. Kallah ne shugaban Kwastam na k’asa. 

Alhaji Musa yace wallahi tunda Malan Sani ya fara bada labarin dalilin da yasa aka kashe Alhaji naji na yarda da abinda ya fad’a, ko Brr. Barau beda gaskiya, domin a lokacin naga yanda yanayinsa ya canza, sai dai kawai mu barma Allah amma sun cutar da Malan Sani. 

Alhaji Usman yace kasan abinda yafi bani mamaki? Brr. Barau lauyen Alhaji Marusa ne, sai gashi ana fad’in wannan abu ya fito da wuri amatsayin wanda zai kare Alhaji Maiwada, a tunanina Brr. Kamal shine lauyen daya tsayama Alhaji a wancan karon, amma sai gashi an juya abun, tun daga lokacin nasan akwai wani abu. 

Ajiyar zuciya Alhaji Mansur yayi yana fad’in duk abinda zan fad’a maku bazai canza komai ba, amma kusa aranku Brr. Barau, Mr. kallah, ‘Yallab’ai da Alhaji Marusa duk a rumfa d’aya suke, nasan mutane ukku d’ayan ne ban sani ba, amma wallahi su dukansu munafukai ne, babu yanda zamuyi ne dole mu barma Allah, zanje na biya tarar da akasa ma Malan Sani, sannan amatsayina na dangin Alhaji da Matarsa mun yafe diyyar da aka fad’a, kuma insha Allahu yau zamu wuce Kano, kome kenan zamuyi waya saboda Bilkisu. 

Alhaji Usman yace wannan ba matsala bane, insha Allahu zata samu kulawa kamar tana kusa da ku, su kuma ka barsu, wata rana Allah zai nuna su a lokacin da basuyi zato ba, zasuji kunya tun aduniya, ina rok’on Allah ya k’ara masu tsawon kwana ko dan su girbi abinda suka shuka. Gaba d’aya suka amsa da amin. 

K’arasawa sukayi wajen Brr. Kamal, anan sukayi masa godiya. Brr. Kamal kam hak’uri yayi ta basu zuciyarsa cike da damuwa. Alhaji Mansur yace haba wallahi bakomai, mun bar ma Allah. 

Kafin a tafi da Malan Sani Alhaji Mansur ya rok’esu alfarmar su bashi mintuna biyar. Matsawa sukayi daga wajen suna fad’in yayi sauri. 

Dafa kafad’ar Malan Sani yayi yana fad’in kasa Allah aranka, kuma kacigaba da addu’a Allah maji roko ne, sannan yana saurin amsa addu’ar wanda aka zalunta yayi hak’uri, insha Allahu wata rana zakaga sakamakon hak’urin da kayi, kuma ina tabbatar maka zaka fita daga wajen nan, ta silar Alhaji Maiwada kashigo wajen nan, domin kana aiki a k’asanshi akayi amfani da wannan aka kulla maka wannan abun, insha Allahu jinin Alhaji shine zai kwato maka hakkin ka, da izinin Allah sai Ra’eez ya zama lauya, domin tun yanzu zan fad’a masa irin zaluncin da akayi ma mahaifinsa da kai, zai tashi da burin d’aukar fansa, ta haka ne zai dage ya cimma burinsa. 

Kai Malan Sani ya jinjina yana fad’in zan so naga wannan ranar, ka dage Alhaji Ra’eez yayi karatu, kada ka barshi a k’asar nan, domin har yanzu acikin makiyan Alhaji babu wanda yasan yana da ‘Dah, insha Allahu sai Ra’eez ya basu mamaki. 

Ayanzu da kayi wannan maganar sai naji wani haske ya ziyarci zuciyata, kuncin da nakeji yayi sauki, inajin zan shiga gidan yari hankali kwance, kuma zan zauna ba tare da wata damuwa ba, domin bazan bari damuwa ta kamani ta kassara lafiyata ba, zan roki Allah ya ara mani rana domin naga wannan rana da kake fad’i, nagode sosai Alhaji. 

Alhaji Mansur yace haka nake son ji Malan Sani, ayanzu kasa zuciyata tayi dad’i, domin damuwakar zata sa naji babu dad’i, amma ayanzu nasa burin d’aukar fansa, zan tsaya ma Ra’eez har ya kai matsayin da zai tsaya mana, kuma insh Allahu zan kula da matarka da d’iyar ka, Allah ya k’ara maka hak’uri.

 Malan Sani yace amin. Haka aka tasa Malan Sani suka shiga mota mutane sai kallonshi akeyi, shi ko gaba d’aya yaji damuwarsa ta ragu sosai, haka suka bar kotu. 

***

Hannu Halima tasa ta goge idonta bayan ta gama jin abinda ya faru, sannan Alhaji Mansur ya fad’a mata yanda sukayi da Malan Sani. 

Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tana fad’in daga yau nima zanyi yaki da damuwar da take zuciyata, dole nayi irin ta Malan matuk’ar ina so naga wannan rana, haka idan ina so na raini yaran mu dole na cire komai araina, zan toshe kunnuwana daga jin surutun mutane, zan bama kowa mamaki domin zan kasance jarumar mace wadda tafi wasu mazan, Allah ya shige mana gaba. 

Alhaji Mansur yace amin Halimatu, hakika kin k’ara sanyaya mani zuciyata da kalamanki, kamar yanda kika d’auki wannan k’addarar ina tabbatar maki Allah bazai barki haka ba, zan tsaya akan al’amuran ku, duk wata matsala bana so ki b’oye mani, ki d’auke ni amatsayin Yayanki, ga Maman Labiba nan ki d’auketa amatsayin ‘Yar uwarki, insha Allahu babu abinda zai gagara. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button