ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Jinjina kai Halima tayi tana masu godiya. Alhaji Mansur yace zamuje can gidan domin a kulleshi, zan aiko da duk wasu kayan abinci da suke gidan saboda idan an barsu zasu lalace, nasan hakkin Ra’eez ne da Bilkisu, kuma zan masa bayani nasan bazai hana a baku ba, ita kuma Bilkisu ga halin da take ciki, saboda haka babu wata matsala dan an baku abinci, sauran kayanta zan aikama Likita dasu saboda arika kula da tsaftar ta, idan akwai wad’an da ya kamata abayar zan fad’a masa ya aika dasu gidan marayu, haka kayan Alhaji duk zan tafi dasu, idan Ra’eez ya d’auki wanda yake so sauran za’a bada sadakarsu dan banga amfanin ajesu ba, sauran abinda yake da amfani duk zamu tafi dasu, kaya masu nauyi ne kawai zamu bari nasan babu abinda zai samesu, domin munyi magana da Alhaji Musa yace zai kawo maigadin da zai zauna agidan sai na rik’a biyanshi saboda Madu yace bazai iya zama ba. 

Halima tace mungode sosai, Allah ya biyaka da alkhairinsa, kuma insha Allahu zan rik’a zuwa duba Ummun Ra’eez sai ka fad’a mani sunan asibitin. 

Alhaji Mansur yace sai dai muje tare domin likitan ya ganki, dan na fad’a masa kada ya yarda da kowa, tunda gaki ke kad’aice wadda zata rik’a zuwa wajenta dan ina jin tsoron a illata ta. Maman Labiba tace wannan haka yake. 

Tashi yayi yana fad’in bara muje mu fara da wuri dole ma sai gobe zamu tafi saboda mu gama komai, tunda ga mota Alhaji Musa ya bani nayi zirga-zirga da ita gara na gama, idan zamu kawo kayan abincin sai ki shirya muje can asibitin. Halima tace shikenan sai kunzo. 

**

Duk wani abu mai muhimmanci na takardun Alhaji sai da suka had’asu a cikin akwati, kayansa kaf sun had’a, dama shi Alhaji Maiwada baya tara sutura, da yayi d’inki yake bayar da wasu dan baya son tara kaya. 

Haka kayan Ummu duk sun had’a mata, sai kayan abinci suka had’a komai sukasa amota. Madu sai kuka yakeyi. Suna cikin had’a kaya sai sukaji sallamar Ladi. 

Bayan tashigo sai tayi turus, kada dai abinda takeji gaskiya ne? Tunda ta shigo Lagos a mota take jin ana wani labari, sai dai bata gazgata ba. Ganin Madu yana kuka yasa tayi saurin matsowa tana tambayarsa.

**

Kuka kawai Ladi takeyi bayan da ta gama jin komai. Maman Labiba tace sai hak’uri Ladi, haka Allah ya tsara bamu da hanyar kaucewa. Ladi tace ikon Allah, wannan abu da me yayi kama? Da zan tafi dubu ashirin Alhaji ya bani kud’in gudummuwa Hajiya ta k’ara mani goma ashe shikenan rabuwar kenan, ya Allah kajik’an Alhaji, itama kuma Hajiya Allah ya bata lafiya, Malan Sani kuma Allah ya saka mashi. 

Gaba d’aya suka amsa da amin. Ladi tace dan Allah kuje dani na gano Hajiya, shikenan yanzu dole na koma gidana amma insha Allahu bazan manta da alkhairinsu ba. Alhaji Mansur yace shikenan bara mu k’arasa sai mu tafi. 

Ladi tana kuka haka ta tayasu had’a kaya, sun bata wasu kayan abincin hada wasu kayan Ummu Maman Labiba ta bata. Alhaji Mansur yace zaije ya ciri kud’i sai ya basu na sallamarsu. Haka suka rufe ko ina bayan sun zare mahad’ar wutar gidan, dama kuma wutar kati ce. 

Bayan sun fito suka rufe gate d’in gidan suka tafi hada Madu, Alhaji Mansur yace idan ya dawo anjima sai ya bama Alhaji Musa mukullin gate d’in da motarsa tunda a hotel zasu kwana saboda da wuri zasu tafi. 

Sai da suka aje kayan sannan suka d’auki Halima suka nufi asibiti. A mota sai jajanta ma Halima Ladi takeyi tana fad’in tunda unguwarsu babu nisa bazata yarda zumunci ba. 

***

Kallon su kawai Ummu takeyi, domin tunda ta farka bata magana sai kallon mutane. Ganin su Halima da Ladi suna kuka yasa itama ta fashe da kuka. Girgiza kai Dr. Saddik yayi yana fad’in abinda takeyi kenan tunda ta farka, idan ta gama kallon mutum sai kawai ta fashe da kuka. 

Alhaji Mansur yace yaushe ne za’a maidata can? Dr. Saddik yace nan da kwana biyu idan ta k’arasa warwarewa.

 Alhaji Mansur yace ga Halima nan itace Matar Malan Sani, idan ba ita ba kada abar kowa yazo wajenta. Dr. Saddik yace wannan ba damuwa, zan amshi lambarta kome kenan zan rik’a mata bayani. Alhaji Mansur yace mungode likita. 

Haka suka gama ganinta ba tare da tace masu komai ba suka tashi zasu tafi bayan sun aje akwatin kayanta. Har sun kai k’ofa sukaji muryarta tana fad’in Abbun Ra’eez sun kashe shi, akira mani Ra’eez kada su kashe mani shi. Saurin juyowa sukayi gaba d’aya. 

Shiru tayi sai kuma ta fashe da kuka tana fad’in duk saina kashe su da wuk’ar makka. Hatta da Alhaji Mansur sai da kwalla ta cika masa ido, jiki a sanyaye suka bar d’akin. Dr. Saddik yace kada ku damu, dama fatana ta fara magana, tunda ta fara sai mugodema Allah, insha Allahu zata samu lafiya. Alhaji Mansur yace mungode sosai. Haka sukayi mashi sallama suka tafi. 

**

Bayan Alhaji Mansur ya ciro kud’i yayi masu sallama mai tsok’a, godiya sukayi mashi Madu yace zai tafi. Alhaji Mansur yace wai Madu yanzu ina zakaje? Madu yace zanje na nemi wajen da zan zauna kuma. 

Da sauri Halima tace idan zaka yarda ka zauna a shagon waje na gidan mu hakan zai zamar mana tsaro musamman yanzu da babu namiji agidan dan Allah. 

Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad’in maganar ki gaskiyace, abinda zuciyata take tunani kenan. Dan Allah Madu ka zauna hakan zai zame masu kariya, kaga akwai Rumaisa, kuma kana da amana ka zama tamkar d’an uwa agaremu, duk da wanda ya had’amu baya raye be kamata mubar abinda ya had’a ya lalace haka ba. 

Jinjina kai Madu yayi yana fad’in shikenan zan zauna sai na rik’a biyan kud’in haya. Halima tace wallahi bazamu amsa ba, kayi zamanka har mutuwa ta raba babu wani abu, dama mutanan unguwar sun saba ganinka agidan, dan ka dawo ba wani abu bane, tunda shagunan biyu ne sai ka bud’e shagon saida abubuwa a d’ayan dama Malan Sani yana so ya bada hayarsa, tunda ga yanda komai ya kasance sai kawai kayi amfani dashi saboda kada ka zauna haka, akwai band’aki a cikin d’ayan shagon sai ka d’aukeshi a d’akin ka. 

Alhaji Mansur yace wannan haka yake, kuma bana so kace a’a. Madu yace shikenan nagode da wannan abu da kukayi mani, wallahi da zan iya zama agidan Alhaji da bazan bari wani ya zauna ba, kawai idan na zauna hankalina bazai kwanta ba, amma nine yafi cancanta na zauna na rik’e amanar gidan, amma duk da haka zan rik’a kula da gidan bazan bari wani abu ya sameshi ba, saboda wanda za’a ba gadin gidan abokina ne agidan Alhaji Musa yake gadi su biyu ne. 

Alhaji Mansur yace bakomai Madu na fahimceka, kunyi sabo sosai da Alhaii, dama nasan bazaka iya zama agidan ba, hakan ma da zakayi yayi, dan haka zan fad’ama Alhaji Musa kaine zaka rik’a kula da gidan. Madu yace nagode. 

Bayan sun aje su aka bud’ema Madu shagunan domin ya gyara, katifarsa daya d’auko da kayansa ya shigar dasu ciki kafin ya gama gyara. Ladi kuwa sallama tayi masu tana godiya kafin ta sake zagayowa saboda basu da nisa. 

Kud’i Alhaji Mansur ya bama Halima masu yawa yana fad’in idan zaiyi aike zai turoma Dr. Saddik sai yarik’a bata tunda bata da account. Godiya tayi masa kafin suka fita. 

A mota yake fad’ama Maman Labiba zasuje ya kama d’aki sai ya barta ta huta yana so yaje yaga Mr. Kallah yasan gobe zai koma abuja, duk da sune suka kashe Alhaji amma shine shugabansu ta hanyarsa za’a samu kud’in Alhaji su fito cikin sauki, kuma idan yaga yaje wajensa da maganar zaifi maida hankali kodan su fita daga zargi. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button