ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

**

Bayan ya kama d’aki suka shiga, wanka ya farayi kafin yayi sallah yasa aka kawo masu abinci sukaci. Tashi yayi yana fad’in ta kulle zaije ya dawo. Addu’a tayi masa kafin ya nufi wajen Mr. Kallah. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

2⃣0⃣

Gaba d’aya kunya ce ta rufe Mr. Kallah, ji yake kamar Alhaji Mansur zai gano su, da kyar yasa jarumta aranshi. Canza fuska yayi zuwa kalar tausayi yace yanzu shikenan fa, har yanzu na kasa mantawa da mutuwar Alhaji Maiwada, shiyasa muka tsaya sai da aka yanke ma direbansa hukunci domin munyi zaman amana da Alhaji. 

Alhaji Mansur yace an dai yanke hukunci, amma wad’an da suke da laifi ai sun san kansu dan wata shari’ar sai alahira.

 K’warewa Mr. Kallah yayi da sauri ya d’auki ruwa yasha. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad’in sannu. Kai Mr. Kallah ya d’aga yana fad’in yanzu meke tafe da kai? Alhaji Mansur yace akan maganar kud’in Alhaji Maiwada ne. 

Jawo takarda Mr. Kallah yayi yana fad’in wannan baka da damuwa, Alhaji Maiwada na mu ne, dole mu tsaya komai nashi ya fito. Yanzu ka bani lambarka kome kenan zamuyi magana, amma ina tabbatar maka kud’inshi bazasu dad’e ba nayi maka alk’awari.

Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad’in nagode sosai, kawo wayar taka nasa maka lambartawa. Bayan ya gama saka masa yayi masa sallama, har bakin mota Mr. Kallah ya rakoshi. 

Yana tafiya ya saki ajiyar zuciya. Ciki ya koma yana lalaubar lambar Alhaji Marusa. Yana d’agawa Mr. Kallah ya fad’a masa yanda sukayi da Alhaji Mansur. 

Alhaji Marusa yace abokina kasan yanda zakayi komai ya fito cikin lokaci, bana son asake tada maganar Alhaji Maiwada, gara a sallamesu nasan bazai sake zuwa garin nan ba. 

Mr. Kallah yace amma ina tsoron matarsa ta warke ta tona mana asiri. Alhaji Marusa yace ai babu abinda ta sani, iyaka tace Malan Sani beyi mata abinda aka fad’a ba, amma bazata k’aryata kisan da muka d’ora masa ba, idan kuma kana ganin akwai matsala itama tabi bayan mijinta kawai. 

Da sauri Mr. Kallah yace haba Alhaji, wai wace irin zuciya kake da ita ne haka? Kai kisa baya maka wahala, kada kamanta rayuwaka biyu muka kashe fa, dan Allah kabar wannan maganar, shikenan bani da wata damuwa akan matarsa abarshi ahaka gobe ma zan koma abuja daga can zanje waje nayo sati biyu dan na samu natsuwa. 

Dariya Alhaji Marusa yasa yana fd’in abokina kacika tsoro, nifa akan dukiyata babu abinda bazan iya ba, dan haka kadena sako mani maganar wata matsala. Mr. Kallah yace shikenan na dena. Sallama sukayi Alhaji Marusa yana ta tsokanarsa. 

****

Wai Maman Naseer baza kici abincin ba, haba dan Allah, ya kike so nayi ne, ga rashin Naseer ke kuma kina so ki jefa kanki cikin damuwa. 

Hannu tasa ta goge idonta tana fad’in yanzu shikenan haka zamu bar wad’an da suka kashe Naseer susha banza kenan Baffan Naseer, kana gani wanda aka kashe su a rana d’aya har an yankema makashin hukunci amma mun kasa tab’uka komai sai kace an kashe mana karan gida. 

Hannunta ya kamo yana fad’in Hajiya Zainabu Abu kenan, wani lokacin mata k’aramin tunani gare ku, shi wanda aka yanke ma hukuncin kinsan irin hujjojin da aka gabatar ma kotu kuwa? To bari kiji, duk da banje kotu ba a labarai naji yanda shari’ar ta kasance, hatta da lauyen da ya tsayama Alhaji Maiwada sai da aka bashi lambar yabo domin ya gabatar da shedu kwarara wanda a kowace kotu akaje dole ta amshe su, kinga kuwa bazamu had’a kanmu da su ba. 

Ni na barma Allah akan mutuwar Naseer, domin nasan zamusha wahala ne kawai idan mukace zamu nemo wad’an da suka kashe shi, domin babu wata alama da aka bari a mutuwar Naseer, ko Waye ya kashe Naseer ba k’aramin makashi ba ne, abinda nake so da ke kema ki barma Allah sai ya saka mana. 

Jinjina kai tayi tana fad’in shikenan Baffan Naseer tunda ka fad’i haka, insha Allahu bazan sake d’aga maganar ba, dama su biyu Allah ya bamu koma waye ya aikata hakan zan cigaba da addu’a Allah ya tona asirinsa. 

Baffa yace amin Zainabu. Murmushi tayi tana goge fuskarta. Sallamar Yayan Naseer ce tasa suka kalli k’ofar tare da amsawa. Zama yayi yana fad’in sannun ku da gida. Baffa yace yauwa sannu *RAFIK*. 

Maman Naseer tace ga abincinka a kicin ka d’auko kaci ina kaje haka ne? Kallonta yayi yana fad’in Mama kinci naki ko? Baffa yace ina fa taci, yanzu nake mata magana kasan yanda tasa damuwa akan rashin gano wanda ya kashe Naseer aranta. 

Maman Naseer tace baka bani amsata ba. Rafik yace naje wajen Junaidu ne nayi masa gaisuwa kinsan makarantar mu d’aya shima k’aninsa ne aka tsinci gawarsa an kashe shi da wuk’a kuma d’an makarantar su Naseer ne, shine naje nayi masa gaisuwa kinsa abokina ne abu iri d’aya muke karantawa ma. 

Baffa yace ikon Allah, dama fa naji ana sanarwa a masallaci an kashe d’an makarantar su Naseer har nake cewa nazo gida naji ko Naseer yasan shi ashe nima bazan iske nawa d’an ba, ya Allah ka tona asirin ko suwa suke aikata wannan mugun abun, ace duk lokaci guda akashe mutum ukku. 

Maman Naseer tace shiyasa nake damuwa da mutuwar Naseer, ina ma akwai wata sheda da mun shiga kotu. Rafik yace haba Mama mu barshi da Allah kawai, wahala zamusha idan mukace zamu shigar da k’ara domin babu sheda, Allah yajik’an Naseer ya bamu ikon jure rashinsa kawai, gashi yau har anyi sadakar ukku ma. 

Baffa yace amin dai. Yaushe zaka koma makaranta? Rafik yace sai anyi kwana bakwai sannan, shima saboda mun kusa fara jarabawa ne. Baffa yace wannan karatu naku akwai wahala ko? Rafik yace da sauki Baffa, idan muka dawo sai munyi (IT) kafin mu koma. 

Baffa yace lallai kace zaka fara karanto labarai. Rafik yace da saura dai, ai yanzu muka fara baza’a bamu karanta labarai ba, zamu dai je muga yanda akeyi. 

Mama tace ina ruwan Rafik d’an jarida. Dariya sukayi Baffa yace zamusha tambaya dai. Rafik yace Baffa ai sai a wajen aiki ake surutu amma agida wazan ma tambaya. Baffa yace Allah dai ya taimaka ya cika maka burinka ka zama cikekken d’an jarida. Gaba d’aya suka amsa da amin. 

**** ****

Washe gari tunda wuri suka bar kano cike da kewar su Alhaji Maiwada. Alhaji Mansur sai da yayi kwalla lokacin da jirginsu ya tashi saboda tunowa da amininsa kuma d’an uwansa. 

***

Koda Halima ta gama abincin safe sai ta zuba ma Madu ta bama Rumaisa ta kai masa. Da fara’a Madu ya amsa gaisuwarta yana fad’in hada abinci haka, to kice mata nagode sosai. 

Bayan ta koma taci abincinta Halima tace Rumaisa ki maida hankali akarantun ki kinji, kinga Babanki yace idan baki karatu zaku b’ata. Rumaisa tace Mama yaushe Baba zai dawo to? Halima tace Babanki yayi tafiya shida Abbun Ra’eez zuwa wata k’asa bazasu dawo ba sai kunyi girma. 

Dariya Rumaisa tasa tana fad’in zasu kawo mana tsara ko? Halima tace sosai kuwa, ke dai ki maida hankali kiyi karatu, babu ruwanki da k’awa kiyi rayuwarki ke kad’ai domin k’awaye gori garesu, ko tashi akayi kada ki tsaya kowa kiyi tahowarki kinji. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button