ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Kai ta d’aga tana fad’in ai babu ruwana da kowa idan akayi break ma ni kad’ai nake zama naci abincina, kuma kinga Auntyn mu tace saura sati biyu muyi hutu da mun dawo zamu shiga aji biyar ai kinga mun kusa gamawa. 

Halima tace sosai ma kuwa, shikenan sai atafi wata makarantar. Rumaisa tace to Mama zan tafi kada amun duka. Halima tace Allah ya ba da sa’a kiyi addu’ar fita daga gida kinji, kuma duk wanda ya tare ki yana maki tambaya akan Babanki ko kallonsa kada kiyi, kome zaice kitafi kada kitsaya duk karya sukeyi kinji. Rumaisa tace to bazan tsaya ba. 

Bayan Halima ta gama karyawa sai ga Sister Hassana tashigo dan su gaisa. Zama tayi suka gaisa, bayan sun gama gaisawa tace Maman Rumaisa ashe haka abu ya kasance kuma? Duk’ar da kai Halima tayi tana kok’arin maida kwallar data taho mata. 

Sister Hassana tace Allah ya kyauta gaba, dan Allah Maman Rumaisa kada kisa damuwa aranki, wallahi har cikin raina ban yarda da abinda akace Malan ya aikata ba, kinsan dama haka aikin Kwastam yake, matuk’ar zakayishi da gaskiya dole ka samu makiya musamnan masu kud’i, dan haka kicigaba dayi masa addu’a wata rana gaskiya zata fito, Allah ya baki ikon jurewa. 

Halima tace amin nagode Sister Allah ya bar zumunci. Sister Hassana tace amin. Ina so duk abinda kike da buk’ata kiyi mani magana matuk’ar befi k’arfina ba zanyi maki, ina fatan kina shan maganin ki? Halima tace ina sha, sister tace yauwa, idan yashiga watan fara zuwa awo sai ki fara insha Allahu babu abinda zai gagara. 

Halima tace nagode sosai. Dubu biyu Sister Hassana ta aje mata tana fad’in zan wuce sai na dawo. Halima tace nagode sister Allah ya saka da alkhairi tace amin. 

Har ta juya ta dawo tana fad’in yauwa wannan mutumin da nagani a shagon k’ofar gida kamar ina ganinsa yana zuwa wajen Malan ko? Kai Halima ta d’aga mata kafin ta bata labarin yanda akayi. 

Murmushi Sister Hassana tayi tana fad’in amma gaskiya ya kyauta, irin wad’annan mutanan ba’a barinsu domin suna da amana, kuma nima naji dad’in zamanshi anan domin kariya ce, a jiya har Dadyn ‘yan biyu yana mani magana ko a samo maki maigadi saboda tsaro, to sai kuma daya dawo da dare yake fad’a mani yaga wani mutum a shagon gidan idan nashigo na tambayeki ashe ma na gida ne. 

Halima tace wallahi kuwa. Sister Hassana tace to Allah ya k’ara tsarewa, ita kuma Allah ya bata lafiya. Halima tace amin. Sallama tayi mata ta fita. 

Madu ne yayi sallama ya tsaya a zaure. Hijabi Halima ta d’auka ta lek’a. Bayan sun gaisa ya k’ara jajanta mana kafin yace dama kasuwa zaije yayo sarin kaya shine ya leko ko tana da sako. 

Halima tace ina da sako kuwa, bari na rubuto maka abubuwan da za’a siyo mani, tunda zaka bud’e shago sai na canza wasu abubuwan da nake saidawa a gida. 

Madu yace baza’ayi haka ba, ki rubuto mani abubuwan da kike saidawa sai asiyo maki a zubasu ashago sai na rik’a saida maki, sauran abinda baza’a aje a shago ba kuma sai ki ajeshi a cikin gida. 

Murmushi Halima tayi tana fad’in nagode sosai Madu. Yace haba ai bakomai, zan samo littafi sai arik’a rubuta komai. Halima tace haba meye na wani rubutu. Madu yace ko musulunci ya yarda da rubutu ai, dan haka babu komai. Halima tace nagode sosai.

**** ****

A washe garin ranar da suka dawo Alhaji Mansur ya nufi makarantar su Ra’eez, bayan sun gama gaisawa da shugaban makarantar ya fad’a masa abinda yake faruwa. Shugaban makarantar yace Allah sarki, ashe Alhaji Maiwada yana da yaro a makarantar nan? Alhaji Mansur yace wallahi kuwa, da yake nine na ke zuwa wajensa shiyasa. 

Jajanta masa yayi kafin yace yanzu jarabawa sukeyi saura sati d’aya suyi hutu, ranar juma’ar nan suke gamawa kaga yau saura kwana biyu kenan tunda yau muna laraba, me zai hana kayi hak’uri zuwa ranar juma’a sai kazo ka tafi dashi. 

Alhaji Mnsur yace haka ne kuma, idan yasan Mahaifinsa ya rasu zai shiga damuwa wata kilama ya kasa rubuta jarabawar, shikenan, dama ina jin tsoron kada yasan labarin daga sama ne, amma tunda sun kusa gamawa ranar juma’ar zan dawo. Shugaban makarantar yace bakomai Allah yajikansa. Alhaji yace amin. Sallama yayi masa ya tafi. 

***

A ranar juma’a yazo ya d’auki Ra’eez, duk hankalin Ra’eez ya tashi ganin anzo d’aukarsa ba’ayi butu ba, duk da Alhaji Mansur yace masa bakomai amma hankalinsa yaki kwanciya, saboda sunsha ganin ana zuwa d’aukar wasu idan iyayensu suka rasu. 

Tun amota Ra’eez ya fara kuka, Alhaji Mansur sai lallashinsa yakeyi shima hawayen suna shirin zubo masa, ganin Ra’eez sai ya sake dawo masa da mutuwar sabuwa. 

Haka suka isa gida ba tare daya fad’a masa komai ba. Maman Labiba ma tana ganin Ra’eez ta fashe da kuka, saurin juyawa Alhaji Mansur yayi saboda hawayen da suka zubo mashi. 

Zama Ra’eez yayi yana sakin wani kukan. Ya jima ahaka kafin Alhaji Mansur yafito. Abinci yasa Maman Labiba ta kawo masa, sai dai duk yanda sukayi yaci kinci yayi. 

Gyara zama Alhaji Mansur yayi ya jawo Ra’eez, cikin kwantar da hankali ya fara bashi labarin abinda ya faru…… 

Ra’eez yasha kuka bana wasa ba, wanda kukan da yakeyi ya sakar masa zazzafan zazzab’i lokaci guda. Gaba d’ayansu suma kukan sukeyi, jin jikinshi yayi zafi sosai yasa Alhaji Mansur ya kaishi d’akinsa, rigarsa ya cire ya kawo ruwa ya fara goge masa jikinsa. 

Ya dad’e yana masa haka har sai da jikin yayi sauki, magani yasa Maman Labiba ta kawo masa, tadashi yayi yasha sannan ya kwanta, cikin lokaci kad’an bacci yayi gaba dashi. 

Fitowa sukayi Maman Labiba tana fad’in irin wannan ranar nake tsoro, dole Ra’eez yashiga damuwa, domin yasan komai akan Iyayensa, Allah ne kawai zai saka masa, bawan Allah gashi dai yaro amma yana da halin manya. 

Alhaji Mansur yace bazan bari sai nan da shekara biyu kafin ya gama makaranta ba, tunda yana da kok’arinsa idan sun koma makaranta aji biyar zai shiga, zanyi magana da shugaban mkarantar asa sunanshi cikin ‘yan aji shidda domin ya zana jarabawa acikinsu, kinga zuwa shekara mai zuwa sune zasu gama sai kawai yaje ya fara karatunshi. 

Maman Labiba tace hakan yayi dai-dai, Allah ya saka masa kok’ari da hazak’a ya kuma bashi ikon cimma wannan burin da muka d’auka. Alhaji Mansur yace amin. 

**** ****

Tun daga wannan lokacin Ra’eez ya koma shiru-shiru, hatta wasan da sukeyi da Labiba tamkar abokan wasa yanzu sai dai yayi murmushi, gaba d’aya baya dariya sai ta kama dole, a islamiyarsu kuwa sosai yake maida hankali, yanda kasan an bud’e masa kwakwalwa yanzu haka yake karatu, duk abinda ya d’auka sai ya iyashi. 

Kasancewar dogon hutu ne na canjin aji yasa suka dad’e agida, ana saura sati biyu su koma ya roki Alhaji Mansur akan suje Lagos yaga Ummunsa. Babu b’ata lokaci Alhaji Mansur ya amince, dama saboda kada ya tada masa hankali yasa bece suje ba. Haka suka shirya suka tafi su biyu dan ta jirgi suka bi. 

**** ***

Halima tana zaune tsakar gida ita da Rumaisa suna gyara alaiyahun da zata zuba amiya, sai sauri sukeyi dan Alhaji Mansur yayi mata waya tun jiya yace zasu zo. Rumaisa sai murna take Yayanta zai zo. 

Bayan ta gama komai suna zaman jiransu sai sallama sukaji, hakan yasa Rumaisa tayi saurin tashi tana murna. Amsa sallamar Halima tayi ta sako hijabi tana fad’in bismilla sannun ku da zuwa. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button