ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 31 to 40

Shigowa sukayi Ra’eez yana goge idonshi, dan tunda suka sauka a Lagos yake kuka. Idanuwan Halima ne suka cika da kwalla ganin Ra’eez. Bayan Rumaisa tayi masu shimfid’a suka zauna. 

Bayan sun gama gaisawa Halima ta kamo Ra’eez tana shafa kanshi sai hak’uri take bashi. Zama Rumaisa tayi tana fad’in Yayana kadena kuka mana, ai Mama tace da Baba da Abbu sunje unguwa sai na girma zasu dawo kaima kadena kuka kaji. 

Murmushi Ra’eez ya saki hawaye suna zubo masa jin shirmen Rumaisa. Dad’i Alhaji Mansur yaji ganin Rumaisa tasa Ra’eez murmushi. 

Tashi Halima tayi zata kawo masu abinci Alhaji yace Halima bar abincin nan sai anjima, yanzu ina so muje wajen Bilkisu ne, ina Madu ko baya nan ne? Halima tace yanzu ya leko yace mun zaije can gidansu Alhaji ya dawo. 

Alhaji Mansur yace Allah sarki, ya zaman naku yake babu wata matsala ko? Halima tace babu komai wallahi, ai Madu ya zame mani tamkar d’an uwana, dole Alhaji yake rik’eshi, domin mutum ne mai gaskiya da amana, babu abinda bayayi mana, cefane duk bayan kwana biyu sai yayo mana, haka Rumaisa shine yake bata kud’in tara, sannan ya amshi kayan da nake sayarwa anan yasa ashago yana tara mani ribar, gaskiya babu abinda zance sai Allah yasa albarka, amma Alhaji ya tafi ya barmu da masu kula damu, Allah yajik’ansa. 

Alhaji Mansur yace amin, ai gaskiya Madu mutumin kirki ne, Allah ya saka masa da alkhairi, ina Ladi fa? Halima tace jiya ma tazo nan mun wuni sai yamma ta tafi, gaskiya ta rike alkawari tana zuwa wallahi, gaskiya bana cikin damuwa sai ta rashin Malan, amma Allah ya had’ani da mutanan arziki, ga Sister Hassana da mijinta babu abinda basa mani, wancan satin ma naje naga M….. 

Shiru tayi ganin Rumaisa tana wajen. Alhaji yace na gane, yana lafiya ko? Halima tace lafiya lau, dan naji dad’in ganinsa a haka, shine ma yasa hankalina ya k’ara kwanciya dan shima ya kwantar da nashi hankalin. 

Alhaji Mansur yace idan kin gama muje asibitin sai muwuce wajensa, Rumaisa kije gidan Sister ki zauna zamuje mudawo kinji. Kai ta d’aga tana fad’in Yayana taho muje. 

Alhaji Mansur yace asibiti za’a kaishi yanzu zamu dawo. Rumaisa tace wayyo sannu kaji, idan anyi maka allura da zafi ka fad’a mani zan rama maka. 

Dariya Ra’eez yasa yana kallonta. Da mamaki Alhaji Mansur yake kallonshi ganin yayi dariya. Gyara wajen Halima tayi suka fita. 

***

Kasancewar an mayar da Ummu asibitin Mahaukata yasa suka nufi can. Suna zuwa shima Dr. Saddik ya isa dan sunyi waya dashi. Bayan sun biya mai mota kud’insa suka k’arasa ciki. 

Da fara’a Dr. Saddik ya tarbe su, bayan sun gama gaisawa suka shiga ciki. Ofis d’in *Dr. Najib* suka nufa. Bayan sun gama gaisawa Alhaji yayi masa godiya akan kok’arin da yakeyi. Dr. Najib yace haba bakomai wallahi, ai jikinta da sauki sai dai acigaba da addu’a. 

Alhaji yace mungode fa. Dr. Saddik yace muje su gaisa ga yaronta nan. Dr. Najib yace ikon Allah, sannu kaji sai hak’uri. Kai kawai Ra’eez ya d’aga yana maida kwallar data taho masa. 

Suna tura k’ofar d’akin da take Ra’eez yayi saurin shigewa, jikinsa har rawa yakeyi yana so yaga Ummunsa. Kwance take idanuwanta a rufe kamar me bacci. 

K’arasawa Ra’eez yayi ya kamo hannunta hawaye suna zubo masa, a hankali ya furta Ummunah! Da sauri ta mik’e tsaye, ganin Ra’eez agabanta yasa ta kwala k’ara tana fad’in Ra’eez sun kashe shi, wallahi sun kashe shi, ka samo mani wuk’ar Makka sai na kashe su dukansu. 

Tashi Ra’eez yayi yana kuka ganin yanda Ummunsa ta koma, su kansu sai da jikinsu yayi sanyi ganin yanda tsigar jikinta ta tashi sai rawa jikinta yakeyi. Hannu tasa ta rik’e kanta tana wani k’ara. 

Da sauri Dr. Najib yayo kanta, kafin ya k’araso ta tafi zata faad’i, aguje ya tareta ta fad’a jikinsa a sume. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

2⃣1⃣

Sai da aka yi mata allurar bacci kafin suka samu kanta, gaba d’aya yau jikinta ya rikice zuwan Ra’eez. Bayan ta samu bacci Dr. Najib yace suje ofis. 

Kallon su yayi yana fad’in ayau naga wani canji atare da ita ganin d’anta da tayi, alamu sun nuna bata mance dashi ba, kuma ina ganin idan tana ganinshi zata iya tunawa da wani abun, tunda kace karatu yakeyi mai zai hana duk hutu yarik’a zuwa yana ganinta kila ta haka zamu samu shawo kanta. 

Gyara zama Alhaji Mansur yayi yana fad’in likita zuwan Ra’eez bazai yuwu ba, domin zai shiga aji shidda, kuma kaga zasu fara karatu mai zurfi ga islamiyya yanayi hakan nema yasa koda Mahaifansa suna nan baya zuwa wajensu, bayan nan kuma gaskiya waje nakeso yayi karatu, akwai wata makaranta *Queen Mary*, law school ce a Landon, tunda nasa ma raina inaso ya karanci fannin shari’a na fara duba makarantu masu kyau, hakan yasa na zab’a masa wannan makarantar, kuma bana so idan ya tafi ya rik’a dawowa, amma tunda akwai wannan lalurar zanyi kok’ari yarik’a zuwa ko so d’aya a shekara ne. 

Jinjina kai Dr. Najib yayi yana fad’in kaima da naka uzurin, bakomai, tunda zai rik’a zuwa hakan ma yayi, dama bana so ace kwata-kwata bazai rik’a zuwa ba domin yin hakan zai maida mu baya. 

Alhaji yace insha Allahu zai zo, Allah ya bata lafiya. Gaba d’aya suka amsa da amin. Tashi sukayi suka masa godiya. Ra’eez yace abarsa a wajenta. Alhaji Mansur yace Ra’eez kaga ciwonta yana tashi kana so tarik’a shan wahala? Kai ya grigiza yana goge hawayen idonshi. 

Alhaji Mansur yace kayi hak’uri zan barka a gidan Maman ku kayi sati d’aya kaga idan zata zo ganin Ummunka sai kuzo tare kaji. Kai ya jinjina. 

Murmushi Dr. Najib yayi yana fad’in gara kasa juriya azuciyarka hakan zaisa kayi karatu sosai, idan kasa damuwa aranka bazaka gama karatu da wuri kazo ka kwato maku hakkin ku ba. 

Godiya sukayi masa suka tafi. Dr. Saddik yaso ya kaisu amma Alhaji Mansur yace ya barshi, baya son arik’a ganinsu tare. Haka suka wuce gidan yari wajen Malan Sani. 

***

Malan Sani yasha kuka, ganin Ra’eez sai ya dawo masa da mutuwar sabuwa, shima Ra’eez d’in kuka yakeyi, duk dauriyar da Halima takeyi sai da tayi kuka, da kyar Alhaji Mansur ya basu hak’uri. 

Kamo Ra’eez Malan Sani yayi yana fad’in wallahi sharri sukayi mani Ra’eez, ban kashe Alhaji ba, haka kuma ban…. Rufe masa baki Ra’eez yayi yana girgiza kai. 

Zame hannunsa yayi yana fad’in Kawu kadena fad’ar haka, duk da k’arancin shekaruna nasan abinda zakayi da wanda baza kayi ba, tunda Abbah ya bani labarin abinda ya faru nasan cewar ba gaskiya bane sharri akayi maka, zanje nayi karatu insha Allahu wata rana sai ka fita daga nan, kuma sai gaskiya ta tabbata. 

Gaba d’ayansu tsayawa sukayi suna kallon Ra’eez jin yanda yake sako magana mai cike da hankali da nutsuwa sai kace wani babba, alokacin gaba d’aya shekarunsa bazasu wuce 17 ba amma yana maganar masu shekaru da yawa. 

Murmushi Alhaji Mansur yayi aranshi yana fad’in Allah mai iko, Allah mai shirya yanda yaso, gashi dai ya hukunta wannan abun sai kuma ya kawo Ra’eez, yasa masa natsuwa da zurfin tunani. Ya Allah ka tabbatar da ikon ka akan wannan bawan naka. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button