ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Tashi Mama tayi tana fad’in mutafi tunda ta samu bacci, Ra’eez kada ka sake yin maganar wad’an nan azzaluman agabanta, nima mantawa nayi har na tambayeka. 

Kai ya d’aga ya tashi yana mai sake kallon Ummunsa, sosai ya k’ara jin kiyayyar su Alhaji Barau. Haka yayi ma ma’aikatan alkhairi da wannan matar kafin suka tafi, a waya ya fad’ama Dr. Saddek halin da take ciki. 

Dr.. Sadeek yace insha Allahu Ummunka ta kusa samun sauki, tunda har take jin haushin mutanan da take zargi tabbas alamun sauki sun fara bayyana, gobe zan shiga dan a d’auki hoton kwakwalwarta. 

Godiya Ra’eez yayi mashi ya kashe wayar. Mama tace idan ka ajemu sai kaje kaji kiran da yake maka. Ra’eez yace bazanje ba sai dai mu had’u a ofis gobe. Mama tace a’a, idan bakaje ba zaiyi tunanin wani abu. 

A fusace Ra’eez yace wallahi bazanje ba, saboda sunanshi kad’ai komai na Ummu ya hargitse, muna firar mu daga jin sunanshi komai ya tsaya, idan naje wallahi zan iya yin wani abu da zaisa na b’ata masa. 

Jinjina kai Mama tayi tace shikenan ka fad’a masa wani uzuri to. Kai ya d’aga yana goge idonshi. 

Bayan ya ajesu Mama tace yashigo yaci abincin dare. Ra’eez yace akoshe nake ai munci a asibiti gida zan tafi kaina yana mun ciwo. Mama tace idan kaje kasha magani, kuma bana so kasa wata damuwa aranka wani ciwon ya shige ka. Kai ya d’aga yana masu sai da safe. 

Har yashiga mota Rumaisa ta fito, jiki a sanyaye ta k’arasa bakin motar. Idanuwa ya tsura mata ganin yanda take kuka. Fitowa yayi ya hard’e hannuwansa a kirji yana kallonta. 

Kasa magana tayi sai kawai ta juya, da sauri ya kamo hannunta ya maidota baya, sakinta yayi kafin yace ta goge fuskarta. 

Hannu tasa tana goge fuskarta wasu hawayen suna zubowa. Murmushin k’arfin hali yayi yana fad’in kina so na kasa bacci ne? Kai ta girgiza. 

Ra’eez yace to bana son kukan ki, idan naje gida zan kiraki kimun fira mai dad’i da zata sakani bacci kinji? Kai ta d’aga tana murmushi. 

Ra’eez yace da kyau Pretty nah, yanzu kishiga gida sai na kiraki, kuma kici abinci kinji? Kai tazo d’agawa yayi saurin fad’in magana zaki mun Malama. 

Dariya tasa tana rufe fuskarta. Shima murmushi yayi yana jin sauki a zuciyarsa. Kallon shi tayi tana fad’in kayi tuki a hankali Yaya. Murmushi yayi yashige mota yana fad’in zanyi amma sai kince kina sona idan ba haka ba a 180 zanje gida. 

Zaro ido tayi tana fad’in kai Yaya. Gira ya d’aga mata yana fad’in sosai kuwa. Murmushi tayi tace to ka rufe idonka zan fad’a. Ra’eez yace Allah beyini makaho ba kuma bazan rufe ba, idan bazaki fad’a mun ba zanje na saurari na wasu Mat… I love you! 

Kafin ya kallota sai kurar gudunta ya iske tayi cikin gida. Besan lokacin daya saki wata dariya ba. Baki ya rik’e yana fad’in lallai ma Pretty, anya itace ma tayi maganar? Lumshe ido yayi yana mai-maita abinda ta fad’a. 

Rufe motar yayi ya nufi gida, shi kad’ai sai murmushi yake saki, a hankali ya furta lallai soyayya tana da dad’i, kuma tana taimako sosai, kafin minti goma zuciyata zafi take ina cikin damuwa, amma cikin mintuna biyar na samu canji. Allah nagode maka da ka saka soyayya a zukatan mu. 

K’aran wayarsa ce ta katse mashi abinda yakeyi, saurin d’auka yayi yana fad’in Abbah ina hanyar gida dana k’arasa zan kira ka. Abbah yace shikenan amma ka kirani fa. Kashe wayar yayi. 

K’ara gudun motar yayi dan yasan tunda Abbah yace zeyi magana dashi to ba k’aramun abu bane, yaso ma tun d’azu ya kirashi a ofis to yasan Abbah baya son magana a waje shiyasa bai kirashi ba. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

2⃣7⃣

Cikin sauri ya kammala abubuwan da ya saba kafin ya kwanta, kallon agogo yayi yaga k’arfe 8:30, wayarsa ya jawo yayi kiran Abbah kirjinsa yana bugawa, tun lokacin da yaji yana son magana dashi yake jin fad’uwar gaba. 

Bayan sun gaisa Alhaji Mansur yace Ra’eez ya Ummun taka da jiki? Ra’eez yace da sauki sosai Abbah, sai dai sunan Alhaji Barau da Mama ta ambata agabanta ya jefata cikin tashin hankali har sai da akayi mata allurar bacci kafin aka samu kanta. 

Jinjina kai Abbah yayi yana fad’in da alamu sauki ya fara zuwa. Ra’eez yace haka Dr. Saddek ma ya fad’a, yace zai shigo asibitin gobe domin suyi mata awo. 

Abbah yace to Allah yasa muji alkhairi. Ra’eez yace amin Abbah. Gyaran murya Abbah yayi yana fad’in Ra’eez ya kamata a birkito da abinda ya faru shekaru 11 da suka wuce. 

Ajiyar zuciya Ra’eez ya saki jin abinda Abbah ya fad’a. Ya naji kayi shiru Ra’eez? Abbah ya fad’a jiki a sanyaye. Murmushin yake Ra’eez yayi yana fad’in bakomai Abbah, kawai maganar ce naji tazo mun daga sama. 

Abbah yace ya kamata kasa wannan maganar aranka, ka tuna akowane lokaci zamu iya maidota domin bazamu tab’a barin jinin Alhaji ya tafi abanza ba, idan kaga haka ta faru to bamu da cikakkar hujjar da zamu gabatar ma kotu. 

Ra’eez yace nima wannan abun yana damuna Abbah, wani lokacin ina ganin kamar bamu da shedar da zamu iya mik’a su Alhaji Barau kotu, duk wata hujja sune suke da ita, koda kotun duniya zamu kaisu sune zasuyi nasara akan mu. 

Abbah yace kada kayi saurin sarewa Ra’eez, mai gaskiya Allah baya tab’ar dashi, ko alhakin Malan Sani ya isa yasa a wannan karon muyi nasara, domin zalunci baya d’orewa. 

Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in insha Allahu muna kammala shari’ar da zamuyi ranar litinin zan fara shirya yanda tamu zata kasance, zanje na lalubo kundin shari’ar su Abbu domin na fara dubashi. 

Abbah yace haka nake son ji Ra’eez, ai fad’uwar gaba asarar namiji, kasa aranka zamuyi nasara. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in insha Allahu Abbah. 

Abbah yace sai kuma maganar waccan motar da take ajiye a gareji, badan kace kana sonta ba da ansayar da ita da ayita ajiyarta bata komai. 

Ra’eez yace dan Allah Abbah abarta, inaso idan nazo Kano na kaita ayi mata seti dan ita nake son nacigaba da hawa. Murmushi Abbah yayi yana fad’in haba Ra’eez, ai zamaninta yawuce, idan aka ga kana hawanta sai arik’a maka kallon matsolo. 

Dariya Ra’eez yasa yana fad’in Allah Abbah sai na hauta kona ‘yan watanni ne, tun lokacin da Abbu ya siyeta nake cewa idan na girma zai koya mani ita, kuma yace zai ajeta har na girma a cikinta zai fara koya mani mota, kaga tunda ban fara koyo acikinta ba ai gara na hauta. 

Abbah yace wannan haka yake, bakomai duk lokacin da kazo sai ka kaita a dubata, amma maganar shari’ar da zakuyi ina fatan babu wata matsala? Ra’eez yace akwai Abbah, amma insha Allahu komai zaizo da sauki, idan muka kammala zan baka labari. Abbah yace shikenan Allah ya bada sa’a. Ra’eez yace amin. Sallama yayi mashi ya kashe wayar. 

Kwanciya yayi yana kallon saman d’akin, tunanin ta yanda zai nemo kundin shari’arsu Abbu kawai yakeyi, dole ya k’ulla alak’a da ma’aikacin d’akin ajiyar kundi. 

K’arar wayarsa ce ta maido dashi daga tunanin da yakeyi. Raheena ya gani, d’an tsaki yayi kafin ya d’auki wayar. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button