ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Sallama tayi masa, bayan ya amsa ta gaishe shi tana tambayarsa gajiyar aiki. Ra’eez yace lafiya lau. Raheena tace d’azu Dady yake fad’amun zaka zo ina ta murna sai kuma yace wai wani uzuri ya hana ka zuwa duk banji dad’i ba ko abinci kasa ci nayi, ta fad’a cike da shagwab’a. 

Murmushi yayi jin abinda ta fad’a. Raheena tace Allah baka san irin son da nake maka bane, saboda kai duk wasu abubuwa da nakeyi marasa kyau na dena, yanzu tsakanina da masu mana aiki sai alkhairi da girmamawa, abinci kuwa tuni na fara iyawa duk saboda kai. 

Ra’eez yace haka akeso ai, kinga har abada bazaki tab’a mantawa dani ba, domin ta sila ta kin samu rayuwa mai kyau. 

Murmushi tayi tana fad’in sosai kuwa, kaga nima zan zamo Uwa ta gari, zan kula da yaran mu wad’an da zamu haifa. Dariya Ra’eez yasa wacce besan da zuwanta ba. 

Raheena tace kadena dariya nasan auren mu bazai ja lokaci ba, dan Momy da Dady duk sun san da maganar, kai kawai nake jira ka amince dani kuma nasan zaka amince tunda gashi kana kula ni. 

Zeyi magana kiran Rumaisa yashigo wayarsa, dafe kai yayi aranshi yana fad’in ga sarkin kishi nan, amma bari ya gwada ta, sharewa yayi suka cigaba da magana. 

Rumaisa kuwa ganin call waiting yasa taji ranta ya b’aci, sake gwadawa tayi amma yana waya, haka tayi ta kiranshi kusan mintuna ashirin begama wayar ba, haushi ne ya isheta tayi wurgi da wayar ta kwanta. 

Hankalin Ra’eez gaba d’aya yana wajen Rumaisa, duk da yayi hakan ne dan ya tsokaneta amma sai yaji babu dad’i. Raheena kuwa sai zuba masa surutu takeyi, ganin yanda yake amsawa yasa tace Dear da alamu bacci kakeji. 

Ra’eez yace gaskiya kam. Raheena tace shikenan bara na barka bana so na takura maka, ina fatan zakayi bacci mai dad’i. Ra’eez yace sosai kuwa. Raheena tace Dear bazaka ce naci abinci ba? Ya kamata ka lallasheni ko abu marar nauyi ne naci. 

Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in to kisha tea da biscuit kafin ki kwanta. Murmushi ta saki tana fad’in yanzu kuwa my one. Sallama yayi mata ya kashe wayar.

Latso lambar Rumaisa yayi, har ta gama k’ara ba’a d’auka ba. Murmushi yayi ya sake kira amma bata d’aga ba. Sai da ya kira so biyar bata d’aga ba. Sako ya tura mata kafin ya aje wayar yana murmushi. 

Rumaisa tana kwance ta gama jin wayarta na k’ara amma taki d’agawa wai tayi fushi. Jin alamun sako yasa tayi saurin jawo wayar. 

*Tunda baki son jin muryata bara na nemo wadda zata taya ni fira kafin nayi bacci.*

Saurin tashi tayi tana kok’arin kiranshi. Murmushi ya saki a lokacin da yaga kiranta. Kashewa yayi kafin ya kirata. 

Tana d’agawa ta fara masa rigima. Dariya yasa yana fad’in ashe dai ana sona? Turo baki tayi tana fad’in Allah Yaya wata rana zakasa zuciyata ta buga. 

Ido ya zaro kamar tana ganinsa yace rufa mun asiri, idan zuciyarki ta buga nayi rayuwa da wa kuma? Da wacce kuke waya ka share ni mana. 

Dariya yayi yana fad’in nikam naji dad’i domin an nuna ana kishina yau. Rumaisa tace Yaya… Kinga ni bana son wannan Yayan, ga sunaye nan masu dad’i kinemo kisa mun. 

Murmushi tayi mai sauti tana fad’in ai bansan su ba. Ra’eez yace shikenan zancigaba da sauraran wacce take kirana da sunaye masu dad’i. Da sauri Rumaisa tace kayi hak’uri *Deel*. 

Saurin kallon wayar yayi yana sakin murmushi, zeyi magana ta kashe wayar. Kwanciya tayi ta rufe fuskarta tana murmushi. 

Sake kira yayi amma yaji akashe. Murmushi ya saki yana rungume filo, juyi yayi yana jin wani irin sanyi aranshi, tabbas soyayyar Rumaisa tayi nisa aranshi, baya jin zai iya rayuwa ba tare da ita ba, fatanshi a kammala wannan shari’ar ayi maganar aurensu. Haka yayi ta tunani har bacci ya d’aukeshi. 

***

A gurguje ya shirya, koda yaje gidansu Rumaisa da kyar yasha tea ya tafi ko had’uwa da Rumaisa basuyi ba dan tunda safe Alhaji Barau yayi masa waya akan maganar jiya hakan yasa yake ta sauri. 

***

Zaune yake a ofis d’in Alhaji Barau, mamaki yake ganin yau yashigo da wuri ko dan yau juma’a yasa yazo? Bayan sun gama gaisawa Alhaji Barau yace ai tun jiya naso kazo dan dai kace kana da uzuri. 

Dama akan maganar wannan shari’ar ce da aka baka, maganar gaskiya Ra’eez wannan yaron da zaka kare Yaron abokin kasuwancin mu ne, babban aminin Alhaji Marusa ne, kasan yanda talakwa suke idan suna jin haushin mutum, wannan yarinya ‘yan unguwarsu ma sun bata shedar bata da hali mai kyau, amma koma menene ina so ka duba shedun da aka baka da kyau, bana so ashiga kotu a samu matsala, domin wannan kotun kowa yasan yanda take da adalci bazan so ace a wannan karon dana zab’eka ace an samu matsala. 

Gyara zama Ra’eez yayi yana fad’in insha Allahu Alhaji bazan kasance mai samar da rashin adalci a kotun ka ba, kamar yanda kowa yasan wannan kotu da adalci ina mai tabbatar maka zan tsaya tsayin daka domin a tabbatar da gaskiya a wannan shari’a. 

Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad’in nasan bazaka bani kunya ba, nagode sosai, zaka iya tafiya. Tashi yayi, har ya kai bakin kofa yaji muryar Alhaji Barau yana fad’in Raheena tace na gaishe ka. 

Murmushi kawai Ra’eez yayi ya d’aga kai kafin ya fice. ‘Yar dariya ya saki jin wani rashin kai a wajen Alhaji Barau, wai Uba ne yake bada irin wannan sakon. Tsaki kawai yayi yawuce. Kallon mutumin da suka taho tare da Brr. Bajinta yayi, kauda kai yayi yawuce dan ya gane Mr. Kallah tun wancan zuwan da suka had’u. 

Bayan sun gaisa da Alhaji Barau Mr. Kallah ya kalli Brr. Bajinta yana fad’in d’an bamu waje zamuyi magana. Gimtse fuska Brr. Bajinta yayi dan beji dad’in abinda yayi masa ba. 

Kallonshi Alhaji Barau yayi yana fad’in kaje kawai. Kai ya jinjina kafin ya fice fuska a d’aure. 

Gyara zama Mr. Kallah yayi yana fad’in ka ganni da sammako ko? Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad’in mamakin da nakeyi kenan, gashi baka kira kace zaka zo ba. 

Mr. Kallah yace wani abu ne ya bani haushi siyasa na taso dan nasan baka da masaniyar abun. Alhaji Barau yace menene kuma ya faru? Mr. Kallah yace mutumin ka mana Alhaji Marusa. 

Cire glass Alhaji Barau yayi yana fad’in wani abun yayi ko? Tab’e baki Mr. Kallah yayi yana fad’in ai nasha fad’a maka Alhaji Marusa beda gwani, tunda ya iya yakice ‘yan uwansa nasan cewar kowama zai iya yakicewa. 

Alhaji Barau yace dan Allah ka bani labari duk kasa kaina ya fara caji. Gyara zama Mr. Kllah yayi yana fad’in ajiya cikin dare ina duba Email d’ina sai ga sako yashigo mani daga *Mark* yana fad’a mani maganar da Alhaji Marusa yayi masa akan wannan kasuwancin da mukace zamu bud’e na shigo da manyan kayan zamani da Mark ya gano mana, kasan harkar akwai k’aruwa sosai, dan matuk’ar muka dace mun gama zama masu kud’i a duniya, kai ina tabbatar maka wannan aikin dole ka ajeshi dan zaman garin nan ma began mu ba. 

Jinjina kai Alhaji Barau yayi yana fad’in ina jinka. 

Mr. Kallah yace ashe Alhaji Marusa ya zagaye ya fad’ama Mark shi kad’ai zai sayi kayan saboda shine ya dad’e a harkar kasuwaci daga baya ya jawo mu, ya kyale mu zai yaga mana wani abu idan komai yayi dai-dai, to ahaka suka tsaya, kasan Mark beda munafurci, shine ya turo mani da sako jiya cikin dare yake fad’a mani yayi mamaki da abinda Alhaji Marusa ya fad’a saboda yasan yanda muka aminta da juna, shi kuma baya iya munafurci dan baya so yaga ta silarshi ya raba abokai, hakan yasa ya fad’a mani domin muje mu sasanta kan mu. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button