ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Dariya Alhaji Barau yasa yana buga tebur. Mr. Kallah yace indai Alhaji Marusa ne kuka ma sai ya saka. Tashi Alhaji Barau yayi yana fad’in wallahi k’aryarsa tasha karya, idan yana tak’ama da jinin fulani ajikinsa zan nuna masa irin namu cin duduniyar, ka barni dashi, cikin ruwan sanyi zan nuna masa rashin wayonsa. 

Zama yayi yana fad’in kai baka tab’a tunanin dalilin da yasa na rabashi da gidanshi na Surelere ba? Duk da gidan ya kasance da zalunci aka amshe shi amma dai ya biya kud’in gidan, domin nasan da Iyalan Alhaji Maiwada suna nan har abada bazasu manta da wannan gidan ba. 

Tun lokacin da wannan gidan ya zama mallakinsa na kudira araina sai na rabashi dashi, hakan yasa cikin ruwan sanyi da muka fara gabatar da kasuwanci atare lokacin da muka samu kaya masu kyau bayan an raba ya nuna yana son wasu daga cikin nawa na barmasa babu ja, da wannan na yaudareshi har ya siyar mani da gidan akan kud’i kalilan gashi yanzu ina rayuwata aciki nida iyalina hankali kwance. 

Dariya Mr. Kallah yasa yana fad’in baka da kyau Alhaji Barau, ai tun alokacin na cika da mamakin yanda akayi ya siyar maka da gidan a wannan kud’i, ashe dai ka nuna masa kafishi sanin kan duniya. 

Alhaji Barau yace ai karatun lauya ba k’arya bane, cud’anya da mutanen da nayi betashi abanza ba tunda gashi yayi mani amfani. Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad’in a wannan karon ma baza muyi sanya ba, bana so abotar mu ta tab’u amma kada ka bari yasan munsan komai. 

Alhaji Barau yace sa ido kayi kallo kai dai. Dariya sukasa suka cigaba da tattaunawa. 

****

Bayan sun fita sallah Ra’eez be jira Jabeer ba ya sulale yaje ya dubo Ummunsa, sosai yaji dad’in ganinta dan jikinta da sauki, sai dai be samu ganin Dr. Saddek ba saboda yana sauri, hakan yasa yawuce. 

Lokacin daya koma duk yanda Jabeer yaso yaji inda yaje be fada masa ba yace kawai Mama ce tayi masa kiran gaggawa hakan yasa ya yarda. 

Bayan sun tashi daga aiki Ra’eez yace Jabeer ya masa rakiya zuwa gidan su Yaron da zai tsaya mawa. Jabeer yace kamar kasan abinda yake raina kenan, gara muje domin kaji ta bakinsa. Ra’eez yace haka ne, sai dai bana so kowa yasan naje wajenshi. 

Jabeer yace muje akwai abinda zan fad’a masa wanda zai hanashi fad’ama kowa. Mota suka shiga suka tafi. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

2⃣8⃣

Sun dad’e a tsaye jikin mota suna jiran su samu wanda yasan Yaron da suka zo wajenshi. Kallon Jabeer Ra’eez yayi yana fad’in kaga na manta sunan yaron da Baba ya fad’a mana rannan. 

Jabeer yace anya ya fad’a mana sunansa kuwa? Gaskiya bana jin ya fad’i sunanshi. Waya Ra’eez ya ciro yana fad’in bara na tambayeshi gara musan sunanshi bana so asan wajenshi muka zo. 

Bugu d’aya Baba ya d’auka, bayan sun gaisa Ra’eez ya tambayeshi sunan Yaron? Bab yace sunanshi *Sameer* gidansu shine na biyu akan layinsu yana nan mai bakin gate. 

Ra’eez yace shikenan sai munyi waya. Kashewa yayi yana kallon gidan da suke fuskanta. Jabeer yace meye sunansa? Sameer! Ra’eez ya fad’a yana mayar da wayarsa aljihu. 

Wani matashi ne yazo wucewa, da sauri Ra’eez yayi masa sallama, bayan sun gaisa yake tambayarsa ko yasan Sameer da yake wancan gidan? Murmushi Matashin yayi yana fad’in *B-Boys* zaka ce. 

Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in shi nake nufi. Matashin yace yanzu zaka ganshi ya dawo dan lokacin zuwanshi bitch yayi. Jabeer yace lallai babban yaro ne. Matashin yace idan B-Boys ne ai beda wasa akwai son harka da jin dad’i. 

Ra’eez yace mungode. Sallama yayi masu yawuce. Jabeer yace da ka sallameshi taya zamu iya ganeshi bayan bamu tab’a ganinshi ba? Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in sa ido kawai kayi kallo, mu k’arasa k’ofar gidansu zamufi saurin cimmasa. 

Basu dad’e a wajen ba sai ga wata rantsatstsiyar mota mai bakin glass ta shigo layin, tun kafin ya iso sauti yake tashi, ganin mutane a bakin gate kuma Matasa ya hana Sameer yin horn, amma a k’aidarsa yana doso gidansu yake horn, kafin ya iso an bud’e gate sai dai kawai ya shige. 

Sautin motar ya rage kafin yaja burki ya sauke glass d’in motar. Hannu yasa ya cire bakin glass da yake idonshi yana bin su Ra’eez da kallo, ko ba’a fad’a masa ba yasan wad’an nan matasan masu ji da kansu ne, domin su duka kyawawa ne, shigar jikinsu abun kallo ce domin dogayen kaya sukasa kasancewar yau juma’a. 

Saurin matsawa Ra’eez yayi fuskarshi d’auke da murmushi ya mik’a mashi hannu yana fad’in barka da zuwa Sameer. Jiki a sanyaye Sameer ya bashi hannu suka gaisa. 

Ra’eez yace idan bazaka damu ba inaso ka juya kan motarka zuwa inda tamu take akwai maganar da nake so muyi. Kallon rashin fahimta Sameer yayi masa. 

Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in kada ka damu, sunana Brr. Ra’eez, nine wanda zan kareka a kotu ranar litinin. Jinjina kai Sameer yayi yana fad’in am sorry ban ganeka ba, muje. 

Zaune suke a cikin motar Sameer sun zuge glass ta yanda baza’a gansu ba. Kallon Sameer Ra’eez yayi yana fad’in duk da an bani duk wata sheda dazan kareka nafi son nazo wajenka naji da bakin ka hakan zaisa nasan yanda zanyi na kare ka da kyau. 

Jiki a sanyaye Sameer ya kalli Ra’eez yana fad’in wallahi Halima sharri take mun fa. Ra’eez yace kasanta kenan? Girgiza kai yayi da sauri yana fad’in haka naji wasu suna kiranta anan nasan sunanta. 

Jabeer yace anan unguwar take ne? Sameer yace nifa bansan gidan su ba, kawai tana sona nayi mata wulakanci shine tace sai tasa an d’aure ni, bayan kwana biyu har na manta sai ga mahaifinta yazo wai nayima d’iyarsa fyad’e, ni mema zanyi da wannan k’azamar nida nake harka da…. Saurin had’iye abinda zai fad’a yayi. 

Ra’eez yace dama kana harka da wasu matan ne? Saurin girgiza kai yayi yana fad’in nifa ko lafiyar kirki banda ita hakan ne ma yasa banyi aure ba amma har k’anina yayi aure. 

Ra’eez yace ashsha, to Allah ya kyauta, shikenan zamu wuce, amma bana so kowa yasan nazo wajen ka idan ba haka ba shirin mu zai rushe. 

Jabeer yace kana fad’ama Mahaifinka lauyen ka yazo shikenan hankalinsa zai tashi zaiyi tunanin ka fad’i wata magana. Cike da gamsuwa Sameer yace babu wanda zan fad’amawa dan Allah kada ka bari a rufe ni. 

Ra’eez yace kada ka damu kotun mu wajen adalci ne. Jinjina kai Sameer yayi yana fad’in nagode. Sallama sukayi suka fita zuwa motarsu. 

Kallon Ra’eez Jabeer yayi yana fad’in meka fahimta agame dashi? Beda gaskiya kawai, Ra’eez ya fad’a. Dariya Jabeer yayi yana fad’in kaifa lauyensa ne ya zaka fad’i haka? Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in su lauya manya, ai kasan Allah baza suyi nasara ba. Jabeer yace sai ka kula fa, bana so su Alhaji Barau su san cewar da gangan ka kadasu. Ra’eez yace kai dai kasa ido zakasha kallo, cikin week end d’in nan zan gama komai. 

Jabeer yace Allah ya bada sa’a. Hannu Ra’eez ya bashi yana fad’in sai litinin ko? Jabeer yace haba dai, bazaka shigo ba? Ra’eez yace sai dai wani satin, dan wannan satin bazan fita ba inaso na shiryama wannan shari’ar. Jabeer yace shikenan, nima zan kwanta na huta sai munyi waya. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button