ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Sallama sukayi kowa ya nufi motarsa zuwa gida. 

****

Wai Raheena har yanzu Ra’eez bece komai ba? Kallon Momy tayi tana fad’in yace mana, uhm! Wallahi Momy D, ya iya soyayya, bakiga yanda yake sona ba, damma suna da shari’a ranar litinin da wannan week end d’in tare zamu yishi anan gidan. 

Murmushi Momy tayi tana fad’in amma naji dad’i sosai, shiyasa jiya nayi magana da Dadynki akan shirin bikin ki, waje nake so muje a had’o komai. 

Rungume Momy tayi tana fad’in gaskiya naji dad’i, bakiga yanda k’awayena suke santinshi ba, rannan dana d’ora wani hotonshi dana had’a da nawa bakiga yanda mukayi kyau ba kamar atare muka d’auka, wasu sai cewa suke nayi dace. 

Momy tace zauna nan su rufe ki da dad’in baki wata ta kwace maki shi. Zaro ido tayi tana fad’in haba dai Momy, ai Ra’eez nawa ne ni kad’ai, idan ban sameshi ba Allah kad’ai yasan halin da…. Saurin rufe mata baki tayi tana fad’in ko da zan rasa komai sai kin aureshi, dan haka ki kwantar da hankalin ki, kisa aranki anyi auren ku, dan yanda na fara fad’ama k’awayena an kusa aurenki bazan bari naji kunya ba. 

Murmushi Raheena tayi tana fad’in ina sonki Momy na. Mai aikinsu ce ta shigo da sallama. Bayan sun amsa ta kalli Raheena tana fad’in Aunty lokacin shiga kicin yayi. 

Saurin tashi Raheena tayi tana fad’in amma nagode, muje kada mu makara. Dariya Momy tayi tana fad’in Allah nagode maka, gaskiya naji dad’in zuwan Ra’eez rayuwarki Raheena, ta silarsa gashi kin canza, sallah akan lokaci, ga girmama masu aiki sannan abinci ma kin iya, ai dole ma na dage ki auri Ra’eez. 

*** ***

Cikin kwana biyu Ra’eez ya kammala abubuwan da yakeyi, ko Ummunsa da kyar yake zuwa ya duba ta saboda beda lokaci, sunyi magana da Dr. Saddek yace sai litinin zasuyi mata awon akwai wani likita da suke jira zaizo. 

Gidan su Rumaisa ma so d’aya yake zuwa da rana yaci abinci, yafiso ya kammala komai ta yanda zai shiga kotu da kwarin guiwa, hatta da wayoyinsa baya d’auka sai idan kiran me muhimmanci ne. 

***

Safiyar litinin da wuri ya kammala shirinsa, haka ya nufi gidan su Rumaisa, bayan sun gaisa yace zai wuce. Mama tace abinci fa? Ra’eez yace Mama yayi safiya da yawa idan muka kammala zanci. 

Girgiza kai tayi tana fad’in zauna kasha ko shayi ne. Haka ya zauna Rumaisa ta kawo masa. Zama tayi tana kallonshi harya kammala. Murmushi yayi yana fad’in kimun addu’a Allah ya bani sa’a kinji. 

Kai ta d’aga tana fad’in inayi maka ai, kuma nasan zakayi nasara. Ra’eez yace nagode, da mun kammala zan maido maki da lokacin ki dana ara. Murmushi tayi ta mik’e. 

Addu’a sosai Mama tayi masa kafin yawuce wajen aiki. 

Ofis d’insa ya fara wucewa kafin lokacin shiga kotun yayi.

K’arfe goma babbar kotu tacika da mutane suna jiran isowar Alkali. Bayan daya shigo kowa ya samu waje ya zauna ana jiran afara. 

Bayan ya zauna ya umarci magatakarda daya karanto shari’a. Tashi yayi ya fara karantowa. 

*A yau litinin goma ga watan oktoba shekara ta dubu biyu da sha tara wannan kotu mai albarka zata saurari k’arar da Malan Haruna ya shigar ta Sameer Aliyu Jabb’ama, wanda yake zarginsa da yima d’iyarsa ‘yar shekara sha shidda fyad’e.* Risnawa yayi ya mik’a takardar. 

Bayan da Alkali ya gama dubawa yace lauyoyin da zasu gabatar da shari’a fa? Tashi sukayi, fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad’in sunana Brr. Bajinta, nine wanda yake kare wad’anda suke k’ara. 

Sunana Brr. Ra’eez, nine nake kare wanda ake k’ara. Jinjina kai Alkali yayi yana fad’in lauyen da zai fara bismilla. 

Fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad’in ya mai shari’a inaso zanyima Sameer wasu tambayoyi idan kotu ta bani dama? Koti ta baka dama, Sameer ya fito gaban kotu. 

Brr. Bajinta… Kotu zataso taji sunanka. 

Sunana Sameer Aliyu Jabb’ama. 

Brr. Bajinta… Malan Aliyu kaji abinda ake tuhumarka dashi, shin ko da gaske ne ka aikata abinda ake zarginka dashi? 

Sameer… Ban aikata abinda ake zargina dashi ba gaskiya. 

Brr. Bajinta… Kana nufin baka san Halima ba? 

Sameer… Tabbas ni bansanta ba idan ba ranar da tazo wajena wai tana sona ba, ni kuma tamun yarinta nayi soyayya da ita sai nace ta tafi ta bani waje, nan fa ta fara mani rashin kunya wai idan tana son abu dole ta sameshi kuma zanga abinda zatayi mani, shine fa kawai naji anzo ana fad’in wai nayi mata fyad’e. 

Brr. Bajinta… Kana nufin dai baka tab’a kaita gidanku ba? 

Sameer… Aini banda lafiyar da zan iya kwanciya da mace ma, hakan yasa ko aure banyi ba. 

Brr. Bajinta… Ko kana da shedar da zaka nuna ma kotu cewar baka da lafiyar kusantar mace? 

Sameer… Kwarai ina da sheda tana wajen likita na. 

Brr. Bajinta… Shikenan iya kar abinda ka sani kenan akan wannan abun da ake zargin ka? 

Sameer…. Iyakar abinda na sani kenan. 

Brr. Bajinta… Zaka iya tafiya, inaso nayi ma likitan Sameer tambaya idan kotu ta bani dama? Kotu ta baka dama. 

Brr. Bajinta…. Kotu zata so taji sunanka da aikin ka. 

Sunana Dr. Sa’eed Jafar, nine likitan da yake kula da lafiyar Sameer kusan shekaru ukku kenan. 

Brr. Bajinta…. Likita wace irin rashin lafiya Sameer yake da ita da har yake zuwa wajen ka? 

Dr. Sa’eed…. E to, a shekarun baya sunzo wajena shida Mahaifinsa kasancewar nine likitan gidansu, alokacin Mahaifinsa yake sheda mani wai Sameer har lokacin baya kula mata, daya bincikeshi sai yace masa shi kawai baya sha’awar mace, shine sukazo wajena, alokacin ne na gano Sameer beda lafiyar da zai iya kusantar mace, hakan yasa na d’orashi akan magani, wannan shine sakamakon binciken da akayi masa, ga magungunan da yake sha. 

Brr. Bajinta… Shikenan zaka iya tafiya. Ina so nayima Dr. Kaseem tambaya. Kotu ta baka dama. 

Brr. Bajinta.. Kotu zataso taji sunan ka da aikin ka. 

Sunana Dr. Kaseem Nuhu, nine likitan daya duba Halima alokacin da Iyayenta suka kaita asibiti. 

Brr. Bajinta… Dr. Kaseem alokacin da aka kai Halima asibiti a wane hali take? 

Dr. Kaseem…. E to, gaskiya ba wani cikin damuwa sosai aka kaita ba, asalima da k’afafuwanta taje, bayan da Mahaifinta yayi mani bayanin fyad’e akayi mata sai muka shiga da ita d’aki domin mu dubata, to abinda na gani yasa nayi mamaki da akace wai fyad’e ne, domin babu alamun wani ciwo ajikinta, da ganin yanayinta kamar ta saba mu’amula da maza haka, sai kawai na rubuta mata magungunan ciwon jiki na kwantar ma da Mahaifinta da hankali dan gaskiya besan halin da d’iyarsa take ciki ba, na fad’a masa anyi mata d’inki kawai zata kwanta na kwana biyu. 

Brr. Bajinta… Idan na fahimceka Halima ba fyad’e akayi mata ba kenan? 

K’arya ne ya mai shari’a, wallahi ‘Diyata bata tab’a aikata masha’a ba, wannan likitan k’arya yakeyi, domin shine ya dubata sai dai idan siyeshi akayi kuma….. 

Bubbuga tebur Alkali yayi hakan yasa Malan Haruna ya koma ya zauna hawaye suna bin fuskarshi, kallon Brr. Barau kawai yakeyi zuciyarsa na masa zafi, yanda yake tafiyar da aikinsa kamar shine yake kare mai laifi. 

Kallonshi Alkali yayi yana fad’in kada ka sake magana akotu dan nan ba kasuwa bace, idan kana da magana kajira abaka dama, Brr. Bajinta zaka iya cigaba. 

Risnawa yayi yana fad’in Dr. Kaseem zaka iya tafiya mun gode. Ina so nayima Halima tambaya idan kotu ta bani dama? Kotu ta baka dama. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button