ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Jiki a sanyaye Halima ta fita gaban kotu, da kyar take iya d’aga k’afarta, kanta ak’asa hawaye ne kawai suke sauka ajikinta. 

Brr. Bajinta.. Meye cikekken sunan ki? 

Sunana Halima Haruna. 

Brr. Barau… Shin ko kinsan wancan? ya nuna Sameer. 

Kai Halima ta d’aga. 

Brr. Bajinta… Baki zaki bud’e kiyi magana. 

Halima na sanshi. 

Brr. Bajinta… Meye alak’ar ku dashi? 

Halima… Babu wata alak’a tsakanina dashi, abinda na sani duk lokacin da zanje islamiya yana tare ni da maganganun banza ni kuma bana kulashi, wata rana nayi latti nazo wucewa kawai naga yasha gabana, zanyi magana kawai ya shafa mani wani kyalle a fuskata, daga nan ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai bud’e ido nayi na ganni kwance a d’akinsa cikin jini, kuka nasa shine yace ko nayi shiru koya k’aramun, cikin tashin hankali na kama bakina, sani yayi na tashi yace na fice kuma kada na bari kowa yasan daga d’akinsa nake, nasan dai na fita daga gidansu na kama hanyar gida, kafin na kai gida bansan abinda ya faru ba sai dai na bud’e ido a gadon asibiti. 

Brr. Bajinta… Halima kuma kin tabbata Sameer ne kika gani? Kai ta d’aga tana fad’in wallahi shine. 

Brr. Bajinta… Shikenan zaki iya tafiya. Ya mai shari’a iya tambayoyin da nake dasu kenan, ina fatan wannan kotu zatayi duba da shedun da aka gabatar domin a kwatar ma me hakki hakkinsa. Nagode. 

Wasu daga cikin kotun dariya suka farayi k’asa-k’asa dan ganin wata bahaguwar shari’a, domin yanda Brr. Bajinta yayi tamkar ba shine yake kare Halima ba. 

Ra’eez kuwa yana zaune ya nutsu ya gama had’a duk wasu bayanai da aka gabatar ma kotu. 

Bayan kowa yayi shiru Alkali yace lauyen da yake kare wanda ake k’ara bismilla. 

Ra’eez… Ya mai shari’a ina so nayima Dr. Sa’eed tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. 

Ra’eez… Likita naji bayanin daka bayar yanzu a kotu akan rashin lafiyar Sameer, shin dama har namiji ya girma baya iya gane beda lafiya ne? 

Dr. Sa’eed….. Yana ganewa mana, ai tun lokacin da namiji ya isa balaga zai iya fahimtar yanayin da yake ciki. 

Ra’eez… Amma naji kace shekaru ukku da suka wuce aka gano Sameer beda lafiya wanda nasan Sameer zai kai shekaru talatin da hud’u ko da biyar ma, shin kana nufin tun alokacin baya besan cewar beda lafiya ba? Kada fa maganarka ta jawo masa bakin jini yazo ya rasa matar aure nan gaba. 

Dr. Sa’eed… E to, kasan ba kowane yake maida hankali akan lafiyarsa ba, wasu kuma zaka samu haka suke Mata basa gabansu koda suna da lafiya. 

Ra’eez…. Mungode likita zaka iya tafiya. Ya mai shari’a ina so nayima Dr. Kaseem tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. 

Ra’eez… Dr. Kaseem kace lokacin da aka kawo Halima wajenka da k’afarta ta tako ko? 

Dr. Kaseem… Kwarai kuwa da k’afarta ta tako. 

Ra’eez…. Kenan lokacin da aka kawota kaine ka amsheta? 

Dr. Kaseem… Saurin d’ago kai yayi yana kifta idanuwa. Ra’eez yace tambayarka nakeyi. E to ba nine na amsheta ba amma nine na dubata. 

Ra’eez… Ai ba cewa nayi kaine ka dubata ba, tambayar ka nake kaine ka amsheta? 

Dr. Kaseem… Ba nine na amsheta ba. 

Ra’eez… To ya akayi ka gane da k’afarta tazo? 

Dr. Kaseem… Yanayinta ya nuna bata cikin wahala ai. 

Ra’eez…. Murmushi yayi yana fad’in amma ai ka kwantar da ita har na kwana biyu kafin ka basu sallama. 

Dr. Kaseem… Kasan idan marar lafiya ya nuna sauki ajikinsa hakan yake bamu damar sallamarsa, to ita ta nuna rashin kwari a jikinta hakan yasa dole na kwantar da ita. 

Ra’eez….. Alokacin da aka kawo ta asibiti jikinta duk jini, gashi kai kuma kace babu alamun fyad’e ajikinta saboda ba shine na farko ba, ko zaka fad’a mana jinin na meye? 

Dr. Kaseem… E to, da yake akwai ciwo a jikin hannunta ina ji jinin ciwon ne. 

Ra’eez… Shikenan zaka iya tafiya. Ina so nayima sister Asabe tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. 

Hannu Brr. Bajinta yasa yana gyara wuyan rigarshi, dama yasan Ra’eez bazai tab’a goyon rashin gaskiya ba, gashinan anyi gudun gara an fad’a gidan zago. 

Haka sauran mutanan kotun duk kansu ya d’aure, gashi dai sunji kowa da lauyenshi amma kuma abun ya juye. 

Ra’eez… Kotu zata so taji sunanki da aikin ki. 

Sunana Asabe Habu, kuma ni ma’akaciyace a asibitin Dr. Kaseem wanda ya kasance na kud’i ne. 

Ra’eez…. Shin ko zaki fad’ama kotu abinda ya faru alokacin da aka kawo Halima asibitin ku? 

Asabe…. E muna zaune gab da magriba sai ga Mahaifinta ya shigo da ita a hannunsa a rud’e, alokacin ma ko motsi batayi ga jikinta duk jini harya b’ata rigar Mahaifinta, yana kuka ya rok’emu akan mu taimaka masa, alokacin ni d’aya ce nan na nuna masu gado ya kwantar da ita, turata nayi zuwa d’aki domin bata taimakon gaggawa, gaskiya abinda na gani ya tada hankalina, sai dai kafin na fara dubata sai ga Dr. Kaseem ya shigo sai yace mun na tafi zai k’arasa dubata, naso na tsaya na taimaka masa sai yace kawai na tafi, hakan yasa na tafi. 

Ra’eez…. Jinjina kai yayi yana fad’in kamar meye kika gani ya tashi hankalin ki? 

Asabe… Yanda aka ci mutuncinta yasa hankalina ya tashi, domin ko waye ya aikata mata haka to da k’arfi ya shigeta. 

Ra’eez… Mungode zaki iya tafiya. Ina so nayima Sameer tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. 

Ra’eez… Malan Sameer, kace Halima tace sai tayi maka rashin kirki ko? To dama can kuna takun sak’a ne da ita? 

Sameer….. Gaskiya ko magana bamayi domin bansanta ba, nasan dai ta k’ofar gidan mu take bi idan zataje makaranta, saboda tana ganina yasa tazo tace mun tana sona ni kuma nayi mata wulak’anci shine tace zan gani. 

Ra’eez…. Sameer ko kasan wannan zoben? 

Sameer… Hankali tashe Sameer yake kallon zoben hannun Ra’eez, tabbas tun bayan rabuwarsu da Halima ya nemeshi ya rasa ashe yana jikinta. Wata irin zufa ce ta fara keto masa, kwalla ne suka cika masa ido, kasa magana yayi sai dai ya duk’ar da kai. 

Ra’eez… Murmushi yayi yana fad’in wannan zoben Malan Haruna ya sameshi ne a jikin gashin Halima alokacin da yake kok’arin kaita asibiti, hakan yasa ya cireshi ya aje, gashi kuma a wannan hoton naka naga irin zoben a hannunka, wata kila ko kama ce kawai. 

Hawaye ne suka fara zubo ma Sameer, a yanzu kam ya sare domin yasan dole a ganoshi, gara kawai yayi kundunbale ya fad’i gaskiya kamar yanda Ra’eez ya kirashi ya fad’a masa ya gano gaskiya shine ya aikata laifi, idan ya tona kanshi shi zai tsaya masa ayi masa hukunci mai sauki. 

Ajiyar zuciya ya saki yana sake kallon hoton hannun Ra’eez, ya rasa a in da ma ya samu hoton. 

Ra’eez… Juyowa yayi yana fad’in ya mai shari’a da alama wannan zoben da Malan Haruna ya bayar bana Sameer bane tunda gashi ya kasa amsawa, ze iya yuwuwa kawai kama ce, domin za’a iya samun irinshi a waje da yawa, kamar yanda Dr. Sa’eed ya sheda ma kotu Sameer beda lafiyar da zai iya hayk’ema mace ina so wannan kotu tayi duba da wannan magana tashi domin ta….. 

Nine na aikata laifin ya mai shari’a, Sameer ya fad’a da k’arfi cikin muryar kuka. Da sauri kowa ya kalleshi. Murmushi Ra’eez ya saki kafin yayi saurin canza fuska ya juyo. 

Gaba d’aya wajen ya hargitse da surutu, Brr. Bajinta kuwa kamar wanda aka dasa haka yake kallon Ra’eez, lallai ya tabbatar yafi k’arfin tunanin Alhaji Barau ba shi bama, wannan rainin hankalin yayi yawa, bayan ya gama fito da gaskiya kuma ya koma yana kok’arin kare Sameer. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button