ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Bubbuga tebur Alkali yayi jiki a sanyaye, gaba d’aya Ra’eez ya kwance masa notin kanshi, daurewa yayi ya tattaro jarumta yasa aranshi. 

Mahaifin Sameer ne ya tashi yana fad’in k’arya ne wallahi, kowa ya sheda Yarona beda lafiya, ina rokon wannan kotu da ta d’aga wannan shari’ar domin aje ayi binciken kwakwalwar Sameer dan wannan maganar da yayi tayi kama da ta masu tab’in hankali. 

Da hankalina Dady! Sameer ya fad’a yana kuka, kallon Alkali yayi yana fad’in zan fad’i gaskiya ya mai shari’a. 

Jinjina kai Alkali yayi kafin yasa akayi shiru. Komawa Ra’eez yayi ya zauna. Sake kallon Sameer Alkali yayi kafin yace muna sauraron ka….. 

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button