ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad’in lallai ankawo maka cigaba a ofis d’inka, domin samun lauyoyi masu hazak’a yana k’arama waje kima, sannu Ra’eez kacigaba da dagewa kaji. 

Kai Ra’eez ya d’aga. Alhaji Barau yace ga wani file nan kaje ka dubashi yanzu aka kawoshi, bana son ka wahalar da kanka domin ba wata babbar shari’a bace kasan wasu mutanan basu da kwakkwarar sheda kawai saboda sun maida kotu wajen wasa komai su kawo k’ara. 

Ra’eez yace zan duba. Kai Alhaji Barau ya jinjina yana fad’in zaka iya tafiya. Sallama yayi masu ya fita. Mr. Kallah yace gaskiya natsuwar Yaron nan tayi mani sosai, daga ganinsa d’an manyan mutane ne. 

Alhaji Barau yace shiyasa nake son had’ashi da Yarinyar waje na. Mr. Kallah yace wai Raheena kake magana? Alhaji Barau yace ita fa, ai kasan ita kad’aice mace sauran maza ne. 

Mr. Kallah yace lallai kayi tunani, kaga nan gaba ko zaka aje aiki zaka iya d’orashi a matsayin ka, kaga shikenan bamu da sauran damuwa kotu ta zama tamu. Alhaji Barau yace kamar kashiga zuciyata. Dariya sukasa suna kashewa. 

**

K’arfe d’aya dai-dai wayar Ra’eez tayi k’ara, yana dubawa yaga sunan daya sama Rumaisa a saman wayar ( *Cutie*) . Murmushi yayi kafin ya katse kiran, dan baya d’aukar mata waya sai dai ya kashe ya kira. 

Da kallo Jabeer ya bishi ganin yanda yake sakin murmushi. Wayar yasa a kunne yana jiran ta d’auka. Tana d’agawa suka gaisa, shiru tayi ta kasa magana. Ra’eez yace an gama fushin dani ne? Rumaisa tace dama lokacin sallah ne yayi. 

Sosai ya saki murmushi dan ya gano manufarta. Rumaisa tace katashi kayi sallah to. Jinjina kai yayi kamar tana gabansa yace yanzu kuwa rankiyadad’e, nagode da wannan kulawa, kinga yau kin riga Rah…. Katse wayar tayi dan bata son ya k’arasa fad’ar sunanta. 

Dariya yayi yana kallon wayar. Dafashi Jabeer yayi yana fad’in Mr. Love idan ka gama muje kada atayar. Girgiza kai yayi yana fad’in waya fad’a maka soyayya nakeyi K’anwata ce fa. 

Jabeer yace naga alama, tashi mutafi to. Dariya Ra’eez yayi yana fad’in da gaske fa nakeyi. Jabeer yace kaji kama kai, kaji nace wani abu ne? Muje kada atayar. Sosa kai Ra’eez yayi suka fita. 

Kasancewar a ofis ya bar wayar suna shigowa ya iske wayarsa tana k’ara, kafin ya d’aga ta katse. Hannu Jabeer yasa ya d’auke wayar yana fad’in yanzu kuma waye ya kira? Ido ya zaro yana fad’in missed call takwas fa. 

Hannu Ra’eez ya kai zai amshe wayarsa yana murmushi. Jabeer yace sai dai kuma lambar babu suna amma duk mutum d’aya ne. Ra’eez zaiyi magana wayar ta sake k’ara. 

D’auka Jabeer yayi yasata a speaker, harararsa Ra’eez yayi yana amsar wayar, kafin ya cire a speaker Raheena tace Allah yasa ba laifi nayima Yayan nawa ba, tun d’azu nake kira amma shiru har kasa hankalina ya tashi fa. 

Saurin cireta yayi yasa a kunne yana kallon Jabeer da yake masa dariya. Zama yayi yana fad’in Raheena ce? Shagwab’e fuska tayi tana fad’in yanzun ma bakayi saving lambar tawa ba? Murmushi yayi yana fad’in ayi hak’uri mantawa nayi. 

Raheena tace nayi ai baka laifi a wajena, ina fatan dai kaci abinci? Ra’eez yace sallah ya kamata ki fara tambaya ko dai bakiyi ba kema? Rufe baki tayi dan itama batayi sallar ba bare ta tambayi wani, wayancewa tayi tana fad’in ai nasan baka wasa da sallah shiyasa ban tambaya ba, amma nayi tawa. 

Ra’eez yace to kin kyauta dan bana son mutum mai wasa da sallah. Raheena tace insha Allahu bazan sake wasa da sallah ba tunda baka so. Ra’eez yace da naji dad’i kuwa. 

Murmushi tayi tana fad’in bazan sake ba, yanzu dai kaci abinci? Ra’eez yace banci ba. Raheena tace gaskiya bazanji dad’i ba ace har yanzu baka ci abinci ba, bani minti talatin yanzu zan kawo maka. 

Ra’eez yace nasa Mama tamun sakwara kibarshi nagode. Raheena tace kai Yayana dan Allah ka barni nazo. Ra’eez yace kibarshi nagode. Shagwab’e fuska tayi tana fad’in to kamun alk’awari zakazo anjima kaji. 

Ra’eez yace zan duba nagani. Raheena tace nagode, ka kular mun da kanka. Ra’eez yace nagode. Kashe wayar yayi yana murmushi. 

Zama Jabeer yayi yana kallonshi hada tagumi. Gira Ra’eez ya d’aga mashi yana fad’in ya dai? Jabeer yace lallai kai d’in azimun ne. 

Gyara zama Ra’eez yayi yana fad’in kacika sa ido wallahi. Jabeer yace naji amma a bani amsa ta. Ra’eez yace kasa ido kacigaba da kallo kawai. Jabeer yace bazaka fad’a ba kenan? Ra’eez yace ka bari idan na tashi zuwa sai muje tare. Jabeer yace yanzu naji batu. Dariya sukayi suka cigaba da aiki. 

Suna tashi Ra’eez yace ma Jabeer dole sutafi tare suci abinci a wajen Mama, Jabeer yace shikenan daga can sai mu wuce ko? Ra’eez yace shikenan amma sai munyi magriba. Jabeer yace sai dai mu fara biyawa gidan mu kada Ummana taga na dad’e sai mu wuce. Ra’eez yace shikenan muje. 

***

Bayan sun biya gidansu Jabeer suka wuce gidan su Rumaisa. Tunda Jabeer yaga yanda Rumaisa take sunne kai ya gano abinda yake tsakanin su, musamnan da yaji Ra’eez yana fad’in ta sako hijabi su biyu ne. Shiru kawai yayi yana dariyarsa. 

Ra’eez yace kai fa d’ansa ido ne. Jabeer yace me kaji nace kuma? Kwafa Ra’eez yayi ya jawo kwano suka fara cin abinci. Mama tace lallai Jabeer ka ciri tuta, da alama hankalin Ra’eez ya kwanta da kai, ban tab’a ganin Ra’eez da aboki ba sai yau. 

Murmushi yayi yana fad’in nima nace masa nayi shiyasa ya amince dani Mama. Murmushi tayi tana fad’in gaskiya naji dad’in had’uwar ku, Allah yasa hakan ya zama alkhairi, sai ku kula da aikin ku kunsan yanda yake da had’ari. Gaba d’aya suka amsa da insha Allah. 

Bayan sun gama suka tashi. Mama tace tafiya zakuyi ne? Jabeer yace zan rakashi wajen… Take masa k’afa Ra’eez yayi hakan yasa yayi shiru. Kallonshi Rumaisa ta tsaya yi. Ra’eez yace yanzu zan dawo Mama. 

Wayarsa ce tayi k’ara, yana d’agawa yace gamu nan zuwa, kashewa yayi yana fad’in muje. Kallon Rumaisa Jabeer yayi yaga yanda ta had’e fuska, fita sukayi tana mai binsu da kallo cike da bakin ciki. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

2⃣4⃣

Tsaye suke a jikin mota acikin harabar gidan su Raheena, tunda suka shigo anguwar fuskar Ra’eez ta canza, haka kawai yake jin wani d’aci a zuciyarsa, a hanya sai wasa da dariya suke da Jabeer amma suna shigowa anguwar yanayinsa ya canza. 

Jabeer ya d’auka wani abunne shiyasa yayi shiru, amma a yanzu da suke tsaye suna jiran fitowar Raheena sai yaga abun yayi yawa, domin yana zolayarsa akan ya fad’a masa tsakanin Rumaisa da Raheena wacece yake so aciki amma sai yaga Ra’eez bai san yanayi ba dan hankalinsa yana wajen kallon gidan, musamman ginin da yake can bayan gidan. 

Hannu Jabeer yasa ya tab’o Ra’eez, da sauri ya juyo jin an dafashi. Ido Jabeer ya tsura mashi ganin yanda idanuwansa sukayi ja. Duk’ar da kai Ra’eez yayi yana kok’arin b’oye b’acin ransa. 

Jabeer yace Ra’eez lafiyar ka kuwa? Murmushin yake Ra’eez yayi yana fad’in lafiya lau me kagani? Jabeer yace tun shigowar mu anguwar nan naga yanayin ka ya canza, tsayuwar mu anan kuma sai naga abun ya k’aru, gashi kana kallon wani waje har idanuwanka sunyi ja, da alama akwai abinda ya sosa maka zuciya ko? Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in bakomai kawai kai ne kaga haka. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button