ALKALI NE Page 41 to 50

Jabeer yace bazaka fad’a mani ba ne kawai, amma har fa magana nake maka hankalin ka yana wani waje har sai da na tab’oka kafin kasan ina magana.
Ra’eez yace babu komai kawai ina tunanin dalilin da yasa Raheena take son nazo bayan nasan babu komai atsakanin mu, duka jiya muka fara ganin juna kuma.
Jabeer yace kaima kasan soyayya ce kad’ai zatasa ta nemeka, nifa tun wayarku ta d’azu na fahimci komai, sai dai kaine ban gane maka ba, a gida ga Rumaisa sannan kuma anan ga Raheena, ban sani ba ko auren gata zakayi.
Ra’eez yace meye kuma auren gata? Jabeer yace auren mata biyu a lokaci guda mana, idan ba gata ba taya zaka had’a mata biyu kana soyayya dasu alokaci guda kuma dukansu wajen kunya ne babu wacce zaka iya ajewa.
Murmushi kawai Ra’eez yayi bece komai ba. Jabeer yace duk da bansan komai a labarin ka ba amma na fahimci kana da alak’a mai k’arfi dasu Rumaisa, kaga kuwa bazaka iya yaudararta ba, ga ‘Yallab’ai kuma, kaga kana aiki a k’ark’ashin sa bazaka iya yaudarar d’iyarsa ba.
Ra’eez yace haka ne, domin Rumaisa ruhin jikina ce, da soyayyarta na girma, domin soyayyarta ta samo asali tun lokacin da naji sunanta, bayan da muka fara gaisawa awaya sai ta k’ara shiga zuciyata, aranar dana fara ganinta duk da muna yara amma najita a jinin jikina, daga lokacin da na mallaki hankalin kaina sai na fahimci ta zama b’argon jikina, in tak’aice maka mutuwace kad’ai zata iya rabani da Rumaisa.
Baki Jabeer ya rik’e yana kallon Ra’eez wanda yake zuba bayani har wani lumshe ido yake yayin da hannunsa yake saman kirjinsa yana nuni dashi. Dariya yayi yana fad’in ita kuma Raheena fa? Ra’eez zaiyi magana yaji k’amshin Raheena ya dakar masa hanci.
Shiru yayi yana kok’arin d’ago kanshi. Cike da yanga Raheena take taku kamar bata son taka k’asa, kayan jikinta kamar zatayi nishi su yage saboda yanda suka matse ta, k’aramin gyale ta yafa a saman kanta ko d’ankwalin kayan bata sa ba, sai gashin data k’ara data bazo a bayanta.
Kallo d’aya yayi mata ya d’auke kanshi cike da takaici, badan akwai abinda yake sak’awa aranshi ba da babu abinda zaisa yazo wajen wannan abar.
Fuskarta d’auke da murmushi ta k’araso wajensu tana fad’in sannun ku da zuwa wallahi banyi zaton zaka zo ba. Fuska a had’e Ra’eez yace sallama ya kamata ki farayi ba wannan maganar ba.
Saurin dafe bakinta tayi ta juya tana fad’in kayi hak’uri na manta ne amma bazan sake ba. Seda ta koma da baya kafin ta dawo bakinta d’auke da sallama.
Gaba d’aynsu suka amsa Jabeer yana fad’in sannu da shanyamu Raheena. Murmushi tayi tana fad’in kuyi hak’uri bansan kun taho ba ne kuma shirina dad’ewa gareshi kusan awata d’aya ina shiryawa.
Ra’eez yace idan kika cigaba da haka bazaki sake ganin mu a wajenki ba, domin mu bama jiran da yawuce minti biyu. Hannuwa ta had’e tana fad’in ayi hak’uri, daga yau bazan sake ba, tunda dai baka son jira nima bazan sake dad’ewa ina shiri ba koda baka nan zanyi kok’arin koyon sauri matuk’ar hakan zai saka farin ciki.
Murmushin gefen baki Ra’eez yayi ya kauda kai. Jabeer ne yace Hajiya Raheena ina wuni. Murmushi tayi tana fad’in la…. Kallon da Ra’eez yayi mata yasa tayi saurin yin shiru.
Ra’eez yace lallai ma, abokin nawa zai gaisheki ki amsa, bayan kinsan daga sallama gaisuwa itace tafi dacewa. Hannu tasa ta d’an bigi kanta tana fad’in dan Allah kuyi hak’uri wallahi ban saba da hakan bane amma zanyi kok’arin gyarawa tunda abinda kake so kenan. Ina wunin ku? Jabeer yace lafiya lau.
Raheena tace mushiga ciki bana fira awaje akwai wajen zaman baki acan. Ra’eez yace bana fira a cikin falo nafi son waje saboda nafi buk’atar iskan waje.
Murmushi ta saki tana fad’in duk yanda kace, ga kujeru acan muje kuzauna to. Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in muje.
Bayan sun zauna mai aiki ta iso da kayan motsa baki a faranti, har k’asa ta duk’a tana gaishe su, bayan sun amsa ta fara kok’arin zuba masu lemu.
Da sauri Ra’eez yace kibarshi kije kawai. Raheena tace haba ka barta mana aikinta ne fa. Kallonta Ra’eez yayi beyi magana ba. Raheena tace shikenan jeki.
Kallon Jabeer tayi tana fad’in gashi bansan sunan ka ba. Jabeer yace zakiji a bakin abokina ai. Kallon Ra’eez tayi tana fad’in Yayana kusha ko ruwa ne mana wane zan zuba maku? Ra’eez yace da ace kece kika had’a komai da kanki kuma kika d’auko daga gida kika kawo har nan shine zan sha, amma ni bana cin abinda masu aiki suka had’a.
Shagwab’e fuska tayi tana fad’in kayi hak’uri daga yau nice zan rik’a maka hidima, duk da bana shiga kicin amma zan fara akan ka.
Tab’e baki Ra’eez yayi yana fad’in amma kin bani kunya, yanzu kamar ki ace bata shiga kicin idan kikayi aure waye zai rik’a maki aikin kuma? Rausayar da kai tayi tana fad’in ai na iya dafa indomie.
Ra’eez yace Jabeer kaji fa. Dariya Jabeer yasa yana fad’in aikin kenan, ai yanzu duk wata mace data fito daga gidan hutu indomie kad’ai zaka sameta ta iya girkawa, wasu ma ko ruwan zafi basu iya d’orawa ba, shiyasa ka ganni nan bazan iya auren macen data fito daga gidan masu kud’i ba.
Raheena tace kai Jabeer kada ka tunzura Yayana mana, wallahi daga yau zan fara koyon komai matuk’ar zaisa shi farin ciki ni kuma zanyi koda zan cutu ne.
Murmushi Jabeer yayi yace lallai Ra’eez ana ji da kai, sai dai kace mani Raheena K’anwar kace amma gashi naji wata maganar kamar… Harara Ra’eez ya sakar masa hakan yasa yayi shiru yana dariya.
Raheena tace e Yayana ne amma wanda za’a iya aura, Jabeer ina so ka tayani neman soyayyar abokin ka, tunda Allah yasa na fara jin sunanshi a wajen Dady naji soyayyarsa a zuciyata, aranar dana fara d’ora idanuwana akansa sai naji komai ya kwance mani, maganar gaskiya bazan b’oye maka ba inama abokin ka soyayya mai zafi, wallahi bana ji zan iya rayuwa babushi.
Tashi Jabeer yayi yana fad’in lallai wannan maganar babbace, Raheena sai nace Allah ya bada sa’a, amma sai kin dage dan abokina mai zafi ne. Wucewa yayi yana kallon Ra’eez yana dariyar shakiyanci, yana mamakin Raheena yanda take fad’ar magana kamar itace saurayin sam babu aji, gata dai ‘yar gayu amma tana kwafsawa.
Ko kallonsa Ra’eez beyi ba amma yasan dariya yake masa. Wayarsa ce tayi k’ara alamun sako yashigo hakan yasa ya maida hankalinsa yana dubawa.
Rumaisa ce, murmushi yayi kafin ya bud’e *Yayana gaskiya ka dawo gida akwai d’orin da zakamun kuma yanzu nake so kamun.* murmushi yayi ya maida wayar a aljihunsa.
Yana d’ago kai suka had’a ido da Raheena da ta langwab’ar da kai tana masa wani irin kallo, saurin d’auke kansa yayi aranshi yana fad’in wannan yarinyar bata da kunya wallahi.
Saurin tashi yayi yana fad’in zamu tafi. Da sauri ta mik’e tana fad’in haba My D, shikenan bazaka tsaya muyi fira ba daga zuwa zaka tafi ko amsata baka bani ba fa.
Kallonta Ra’eez yayi yana fad’in idan kika gyara halayenki da bana so alokacin zan fad’a maki abinda na yanke wanda nasan kece zai taimaka.
Murmushi tayi tana fad’in kasa naji dad’i sosai, kuma daga yau zan fara gyara duk abinda baka so, nan da wata d’aya zan zama macen da ta iya girki sosai.
Ra’eez yace zangani ai. Jerowa sukayi zuwa wajen motarsu sai labari take basa kamar zata shige jikinsa, shi kuwa hankalinsa yana wajen Rumaisa ya kosa ya koma.