ALKALI NE Page 41 to 50

Kwanciya tayi tana fad’in ashe ma yana sona shine yake ja mani aji, nima bazan maida amsar ba sai gobe nima sai naja aji. Kwanciya tayi da anjima sai ta jawo wayar ta sake karanta abinda ya rubuta.
Can dai ta kasa daurewa, tashi tayi domin ta maida masa amsa… *Yayana nagode da soyayyarka agare ni, insha Allahu zaka sameni amatsayin Uwa tagari a wajen ‘Ya’yan mu, amma dan Allah kadena mani wasa da wata mace zuciyata bazata iya d’auka ba. Kayi bacci lafiya nagode.*
Tana turawa tayi saurin kashe wayar gaba d’aya tana murmushi.
***
Ra’eez daya kasa bacci yana rokon Allah yasa ta amince dashi, k’arar wayarsa yaji alamun shigowar sako, jiki na rawa ya jawota yana fatan Allah yasa yayi farin gani.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣5⃣
Ra’eez besan lokacin daya tashi zaune ba, filo ya jawo ya rungume yana sakin murmushi, ya dad’e yana jiran irin wannan ranar domin shima yashiga sahun masoya amma sai yau Allah yasa zai shiga.
Komawa yayi ya kwanta yana kok’arin kiran Rumaisa, sai dai kiran farko yaji wayar akashe. Murmushi yayi yana fad’in sarkin kunya, dama nasan bazan sameki ba.
Lumshe ido yayi yana tunanin ya kamata ya sama mata gurbin shiga makaranta kafin ayi bikinsu. Saurin girgiza kai yayi yana fad’in bana son ta fara karatu garin nan saboda ba lallai zaman mu ya d’ore anan ba, daga ranar da aka gano gaskiya dole zasu koma kano, gara ma ya bari bayan anyi biki a hankali sai tayi karatun ta.
Cike da gamsuwa ya jinjina kai. Shiru yayi yana tunanin Raheena. Murmushi yayi yana fad’in kiyi hakuri Mahaifinki ne ya jaza maki, amma dole su d’and’ana illar yaudara da zalunci, koba komai nima zakici moriyata.
Haka ya kwanta cike da tunanin masoyiyarsa har bacci ya d’aukesa.
*** ***
Kiran wayar Raheena ne ya tashesa a bacci da ya makara, saurin tashi yayi ya d’auka. Murmushi Raheena tayi tana fad’in lokacin sallah yayi. Ra’eez yace amma nagode maki, badan ke ba da na makara, amma nasan kema bakya tashi sallar asuba ya akayi har kika tashe ni? Raheena tace wallahi ada ne bana tashi sai da safe nake sallah, amma tun daga ranar da kace kaji dad’i dana tasheka kuma kana son mai sallah da wuri yasa nake tashi, saboda kai har alarm nasa wallahi.
Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in Allah yasa ki dawwama a haka, kuma ina so ki rik’a yin komai saboda Allah ba danni ba, hakan zai sa abun ya bi maki jiki ko dani ko bani kicigaba.
Raheena tace insha Allahu. Ra’eez yace nagode bara naje masallaci. Raheena tace ka sani cikin addu’ar ka. Murmushi yayi yana fad’in insha Allah. Sauka yayi ya nufi band’aki yana murmushi yayin da k’asan zuciyarsa ya fara tausayin Raheena danshi mutum ne mai tausayi.
***
Bayan ya kammala shirinsa na fita aiki ya tsaya yana duba wayarsa, yasan bayan ya fito wanka Jabeer ya kirasa, bayan sun gama waya ya ajeta saman gado yacigaba da shiri.
Kugu ya rik’e yana mamakin ina ta shige? K’aranta ya faraji alamun ana kiransa, dubawa ya farayi har ya gano daga k’ark’ashin gado k’aran yake fitowa. Murmushi yayi yana fad’in ashe kina nan.
Hannu yasa ta k’asan gadon sai dai tayi ciki hakan yasa ya tashi ya fara d’aga katifar, sai da yasa k’afarsa ya tokare katifar kafin ya duk’a ya d’auko wayar.
Bayan ya d’auko wayar har ya d’ago ya koma yana duba jikin gadon ganin kamar wata durowa a jiki, mamaki ne ya kamashi yana tunanin dama anama gado durowa? Murmushi yayi yana fad’in mutanan Da akwai dabara. Hannu ya kai zai bud’e wayarsa tayi k’ara, yana dubawa yaga Mama ce, saurin sakin katifar yayi ya tsinke kiran kafin ya kirata.
Tana d’agawa ta fara tambayarsa lafiya be fito ba har yanzu? Ra’eez yace na shirya wayata na tsaya nema amma gani nan. Kashe wayar tayi. Juyawa yayi yana kallon gadon kafin ya d’auki jakarsa da mukulli yayi waje yana tunanin abinda yake cikin durowar.
Yana tuki ya kira Alhaji Mansur, bayan sun gama gaisawa yake tambayarsa jikin Ummunsa? Ra’eez yace kamar koda yaushe Abba, kwana biyu banje ba saboda wani aiki da nakeyi amma yau daga ofis zan je na ganta.
Alhaji Mansur yace baka kyauta ba gaskiya, kasan dai yanda take jin dad’i idan kaje shine zaka kwana biyu ba tare daka lek’a ba. Ra’eez yace ayi hakuri Abbah zanje yau.
Alhaji Mansur yace shikenan, yasu Mamar taku da Rumaisa fa? Ra’eez yace duk suna lafiya ina hanyar zuwa gidan ma. Alhaji Mansur yace ina Kawun ka fa? Ra’eez yace duk yau zan lek’a insha Allahu.
Alhaji Mansur yace idan kaje wajensa ka had’amu ina so mugaisa, kaima idan ka samu lokaci akwai maganar da zamuyi, ina fatan kana kula a wajen aikin ka ko? Ra’eez yace sosai ma Abbah.
Alhaji Mansur yace haka ake so, da fatan kana kula da yanayin Alkalin ku? Ra’eez yace Abbah shekaran jiya har gidansa ya gayyace ni cin abinci wai yana sona, ashe d’iyarsa yake so ya had’amu, sai da mukaje gidan na samu ashe tsohon gidan Abbu ne.
Alhaji Mansur yace ka kula fa, duk yanda zai jaka jikinsa kada ka saki jiki dashi har ya gano wani abu daga gareka, bana so kowa yasan kana da alak’a da Mahaifinka, nasan waye Brr. Barau, yana da matuk’ar wayau, dan haka ka kula sosai.
Ra’eez yace insha Allahu. Alhaji Mansur yace ina fatan ba son yarinyar tasa kake ba ko? Zaro ido Ra’eez yayi yana fad’in haba dai Abbah, ai ko d’aura mani ita akayi na kwanceta na gudu.
Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad’in ai dole na tambaya kasan ita zuciya ba ruwanta da kiyayyar wasu. Ra’eez yace babu komai a zuciyata Abbah, ni yanzu ma ta Rumaisa nake dan jiya na fad’a mata abinda yake raina.
Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad’in ja’iri, ai na d’auka zaka cigaba da b’oyewa ne, ko jiya Ummanku tamun maganar nace ta barka idan ka gaji da ajiyar abunka zaka furta ne, ashema har ka shigar da kan ka.
Shafa kai Ra’eez yayi yana fad’in wallahi kuwa Abbah. Alhaji Mansur yace haka akeso, Allah ya tabbatar da alkhairi. Kasa amsawa Ra’eez yayi yana fad’in ina Labiba? Alhaji Mansur yace jiya ma tazo gida da yaranta.
Ra’eez yace zan kirata. Alhaji Mansur yace bara na barka gashi ma ka kusa makara, ka gaishe dasu Maman ta ku. Ra’eez yace nagode agaishe da Ummah.
****
Koda yaje gidan su Rumaisa bai isketa a tsakar gida ba, tana jinsa tayi saurin shiga band’aki. Bayan sun gaisa da Mama ta kawo masa abinci.
Yana ci suna fira yana fad’a mata Abbah yana gaisheta. Mama tace Allah sarki ko jiya munyi waya da Umman ka ai. Ra’eez yace anjima idan na taso zan biya wajen Kawu da Ummu.
Mama tace wallahi nima ina son naje na ganshi, Abdallah yana yawan tambayarsa. Ra’eez yace kushirya idan na dawo sai na biyo mutafi gaba d’aya, amma sai dai Abdallah ya hakura da islamiya tunda dawuri zan dawo.
Mama tace shikenan. Rumaisa ta kwalama kira amma taji shiru. Tsaki tayi tana fad’in bansan me kike a band’aki ba idan ki kashiga kamar wacce zata canza fata.
Ra’eez yace Mama kibarta tayi wankanta atsanake. Rik’e baki Mama tayi tana fad’in goya mata baya zakayi? Dama saboda kai nake kiranta tazo ku gaisa.