ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Tashi yayi yana murmushi yace zamu gaisa a waya ai, idan Abdallah ya dawo agaishe mani dashi sai na dawo. 

Mama tace to Allah ya bada sa’a ya kare ka daga sharrin mahassada. Ra’eez yace amin. Kud’i ya aje mata yayi waje da sauri dan yasan halinta. Tana tambayarsa abinda zaici amma yayi waje. 

Madu ne ya taso yana fad’in Ra’eez har ka fito? Ra’eez yace nafito Baba Madu ya kasuwar? Madu yace gatanan Alhamdulillahi sai godiya. Kud’i Ra’eez ya ciro ya mik’a masa yana fad’in ga wannan, anjima idan na dawo ka shirya zamu kaima Kawu da Ummu ziyara. 

Madu yace gaskiya daka kyauta, angode sosai Allah yayi albarka sai ka dawo. Ra’eez yace amin na tafi. 

Yana shiga mota ya latso wayar Rumaisa, bugu biyu ta d’auka bakinta d’auke da sallama. Lumshe ido yayi yana amsawa tare da fad’in kin gama gudun? Murmushi tayi mai sauti ta fara gaishe shi. 

Ra’eez yace bana cin mike, wallahi idan kina mani rowar ganin ki zakisa na rik’a kula wasu. Da sauri Rumaisa tace kayi hak’uri to. Ra’eez yace bazanyi ba, aikinsan bazan iya aikin kirki ba idan ban ganki ba ko. 

Saurin tashi tayi tayo waje tana bashi hak’uri, kamar ance ya d’aga idonshi sai ganinta yayi a k’ofar gida ta langwab’ar da kai tana kallonshi hannunta rik’e da waya tana murmushi. 

Da sauri ya kashe wayar ya fito. Yana zuwa tayi saurin duk’ar da kanta k’asa tana sake gaisheshi. Tsura mata ido yayi yana fad’in ashe dai ana tsoron kishiya? Turo baki tayi tana fad’in ni bana tsoro. 

Dariya yayi yana fad’in gashi daga fad’in magana kin fito, ai dama nasan ba wani abinda kikeyi aband’aki saboda kada Mama ta kira ki kawo mani abinci yasa kika shige band’aki, to daga yau bazan sake cin abinci ba matuk’ar ba kece kika kawo mani ba. 

Kallonshi tayi tana fad’in shikenan bazan sake ba. Murmushi yayi yana fad’in yauwa Pretty na, ina fatan dai jiya kinyi bacci mai dad’i? Kai ta d’aga a hankali tace sosai ma. 

Ajiyar zuciya ya saki yana fad’in bara na tafi aiki na kusa makara, idan na dawo zamuje wajen Kawu da Ummu. Murmushi ta saki tana fad’in sai ka dawo ka kular…. Shiru tayi tana sunne kai. 

Murmushi yayi mai sauti yana fad’in zan kular maki da kaina sosai. Da sauri tashige ciki tana murmushi. Girgiza kai yayi ya juya zuwa mota ya tafi. 

Da Mama taci karo a tsakar gida. Saurin duk’ar da kai tayi kamar marar gaskiya. Murmushi Mama tayi tana fad’in zaku k’araci gulmar ku dai. Turo baki Rumaisa tayi tace kai Mama me nayi kuma? Mama tace ina zan sani, idan tayi wari dai naji. 

Dariya Rumaisa tayi tashige ciki. Murmushi Mama tayi tana fad’in Allah ka tabbatar da alkhairi. Idanuwanta ne suka ciko da kwalla tana fad’in Allah ka kawo mana k’arshen wannan masifa da muke ciki, Allah ka fiddo bawanka haka nan, ka bama Hajiya lafiya kuma ka tona asirin munafukai. 

**** ****

Zaune suke a ofis suna ta aiki Ra’eez yana kok’arin had’a aikin da Alhaji Barau ya bashi akan wani case wanda za’ayi da Yaron abokin kasuwancinsu, Alhaji Marusa shine yayi mashi jagora domin yasan matuk’ar akazo kotun su case d’in zai mutu cikin ruwan sanyi. 

Bayan da aka kawo ma Alhaji Barau sai yace Ra’eez zai bamawa. Alhaji Marusa yace abama Brr. Bajinta domin shine namu, shine yasan yanda muke tafiyar da komai, bana so azo a samu matsala. 

Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad’in ina da dalilin da yasa na bama Ra’eez, domin idan muka bama Brr. Bajinta aikin su wad’an can zasu iya d’aukar Ra’eez ya tsaya masu, na tsora ta da yaron domin yana da wata baiwa, koni da nayi gogayya alokacin ina Barrister bazan nuna masa komai ba, kaga dan ya goga da Brr. Bajinta tuni zai kadashi, wannan dalilin ne yasa na bashi case d’in, domin zamu bashi shedar bogi kuma kaga dole da ita zaiyi amfani, nasan zasu iya d’aukar Brr. Bajinta domin sun san yana kada mutane, kaga shikuma sai yaki zaluko kwararen hujjoji, kaga kuma kotu da kwararen shedu take aiki, shikenan case ya mutu. 

Tafi Alhaji Marusa yayi yana fad’in Alhaji Barau har yanzu kana nan yanda na sanka, shiyasa akoda yaushe hankalina yake kwance, domin nasan kowace katob’ara nayi ina da mai tsaya mani. 

Alhaji Barau yace ai baku da matsala, wani abun ma sai ya zama surikina. Dariya sukasa, Alhaji Marusa yace amma duk da haka Brr. Bajinta ya tarbi wad’an da suka kawo k’arar yace zai tsaya masu kada suje su bama wani lauyan. Alhaji Barau yace kaima ka kawo shawara, shikenan hakan za’ayi. Dariya suka sake sawa da haka suka bar zancen akan a bama Ra’eez case d’in, sai gashi kuma an bashi. 

Shiru Ra’eez yayi yana kallon takardun da masinjan Alhaji Barau ya kawo masa. Sake dubasu yayi yana mamakin irin wannan abu, gashi dai an bashi takardar case, ina ruwanshi da aiko masa da shedu kuma? Ai wannan aikinsa ne yaje ya nemo komai da kanshi, kuma yana so ma ya gana da yaron da zai tsaya mawa. 

Tsaki yayi yana fad’in bazan biye tasu ba, dole na gano lauyen da zai tsaya ma d’ayan b’angaren domin nasan irin shirin da zanyi, tunda yaga haka ajikinsa yasan abinda aka bashi babu gaskiya aciki, shi kuma yayi alk’awarin bazaiyi aikin rashin gaskiya ba. 

Jabeer ne ya dafashi yana fad’in Ra’eez lafiya kuwa? Ajiyar zuciya yayi yana fad’in wallahi nashiga tunanin wani rainin hankali da akeso amun ne. Jabeer yace akan mefa? Takardar Ra’eez ya mik’a masa yana fad’in wani k’arfin hali nake gani yanzu, sai kace wanda yake aikin gata, ace ina lauya amma sheduma sai an nemo mani kawai zuwa zanyi na gabatar dasu. 

Dariya Jabeer yayi yana fad’in da sannu dai zaka fara gano halin mutumin. Tsaki Ra’eez yayi yana fad’in ko kasan wanda zamu kara dashi? Jabeer yace yawuce Brr. Bajinta. 

Saurin kallonshi Ra’eez yayi cike da alamun tambaya. Jabeer yace nasan dole hakan ne zata kasance, domin farkon zuwana da nayi wani case nayi nasara anyi mani irin haka, sai dai alokacin ban gama gogewa da kowa ba sai nayi yanda suka ce, kuma nida Brr. Bajinta muka kara, abun ya bani mamaki ganin yanda yake ma wanda yake karewa wata irin tambaya, sai ka kad’auka shine yake kare wanda nake karewa, gashi dai abinciken da suka bani nasan akwai alamun tambaya, bangama shan mamaki ba sai da shari’ar tazo k’arshe, ina ji ina gani aka yanke ma wanda Brr. Bajinta yake karewa hukunci, mutane sunyi mamakin yanda sabon zuwa kamata ya iya kada kwararren lauya, kuma a shari’ar da mukayi ya fini baki amma duk da haka nine nayi nasara. 

Jinjina kai Ra’eez yayi yana sakin murmushi ta gefen baki, kallon Jabeer yayi yana had’a takardu yace ka barni dasu, zanyi wasa dasu, za’aga yanda ake shari’a a wajena domin bazan bari su sani aikata kuskure irin nasu ba. 

Jabeer yace sai kayi da gaske kam. Ra’eez yace dole inaso na had’u da yaron domin bazan shiga shari’a da abinda suka bani ba. Jabeer yace kayi dai-dai, tashi muje sallah.

*** ***

Bayan sun tashi daga aiki kowa ya fito ya nufi motarshi, wani dattijo suka gani zaune a gefe ya buga tagumi ya lula tunani, har sun wuceshi sun kai wajen motarsu sukaji alamun motsi. 

Dattijon suka gani yayo wajensu da d’an sassarfa. Tsayawa sukayi suna kallonshi. Bayan ya k’araso ya matsa kusa da Ra’eez fuskarsa d’auke da damuwa. Ra’eez ne ya fara gaisheshi yana fad’in lafiya dai Baba? Wanda aka kira da Baba yace ba lafiya ba Yaro. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button