ALKALI NE Page 41 to 50

Gyara tsayuwa Ra’eez yayi yana fad’in mecece damuwar ka Baba? Hannu Dattijon yasa ya goge kwallar data zubo masa yana fad’in nazo wajen nan dasa ran ganinka domin nasan zaka iya kwato mana hakkin mu, tun ranar dana fara kallon shari’ar ka da akayi ta farko na yaba da kwazon ka, duk da ban tab’a tunanin zan samu kaina a kotu na kawo k’ara ba amma tun a wancan lokacin nake aiyana koda shari’a zata had’oni a kotu tabbas kaine wanda zan nema, sai gashi lokaci yazo shari’a ta kawoni kotun ku, an zalunceni anci mutuncin Auta ta, nazo neman lauya sai na samu ance kaine wanda zai kare Yaron daya lalata rayuwar ‘Yata, abun ya bani mamaki alokacin da Brr. Bajinta ya tarbeni kamar dama ni yake jira, kuma anan take yace shine zai tsaya mani, tunda ya fad’i haka jikina ya kasa amincewa dashi, domin nasan shi lauyan manyan mutane ne, narasa inda zansa raina hakan yasa nace dole sai na ganka naji da gaske kaine zaka tsayama wannan Yaron ko kuwa.
Ajiyar zuciya Ra’eez yayi cike da tausayin wannan Dattijo, tabbas su Brr. Bajinta sun shirya wani abu, tun daga jin bayanin Baba yasan akwai alamun tambaya.
Kallon Dattijon yayi yana fad’in Baba kayi hak’uri, insha Allahu kaine zakayi nasara, tabbas nine wanda ‘Yallab’ai ya bama damar kare wanda kake k’ara, amma ina mai tabbatar maka kaine zakayi nasara.
Dattijo yace ta yaya Yaro? Nasan irin basirar ka baza’a iya kada ka ba, yanzu kam inaji na hak’ura da wannan shari’ar, cuta ce an cuci Auta ta, zan koma gida muyi hakuri da K’addarar da Allah ya aiko mana, shi kuma mun barsa da Allah, zai biyamu alokacin da beda kowa.
Jabeer ne yayi saurin fad’in Baba kada kace haka, tunda abokina yace kaine zakayi nasara to kasa aranka zakayi d’in, bazamu bari a danne maku hakkin ku ba, ka yarda damu.
Jinjina kai Dattijon yayi yana fad’in shikenan, na amince da ku, Allah ya bamu sa’a. Ra’eez yace amin Baba, yanzu kashiga mota ina so naje naga Autar taka dan bana so kowa ya gammu tare, kuma kada ka fad’ama kowa munyi magana da kai kawai kayi abinda Brr. Bajinta yace maka. Dattijo yace nagode sosai. Mota suka shiga Ra’eez yana fad’in na makara ma akwai inda zamuje, amma daga can sai na d’auko su Mama mu wuce kawai. Shima Jabeer yashiga tashi motar ya bisu abaya.
Ur’s.
Nabeelert Lady????*Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣6⃣
Idanuwan Ra’eez ne suka ciko da kwalla tun daga lokacin da yayi ido biyu da Yarinyar Baba wacce bazata wuce shekara 16 ba amma an lalata mata rayuwa. Hannu yasa ya goge idonshi yana kallon Mahaifiyar Yarinyar yana fad’in Mama kuyi hakuri, insha Allahu zakuyi nasara, duk da ba nine zan tsaya maku ba kusa aranku ku nake ma aiki.
Goge idonta tayi tana fad’in na yarda da abinda kace, mungode da wannan taimako. Ra’eez yace bakomai, ya sunanta ne? *Habiba* sunanta, ita kad’ai gare mu mace dama su ukku ne, biyu maza sai ita, babban cikinsu ya rasu yanzu su biyu ne, muna murnar ta kammala babbar makaranta Malan yana cewa za’a sama mata wata makarantar tunda burinta ne ta karanci aikin lafiya sai gashi an lalata mata rayuwa, duk da bamu da k’arfi mun yanke shawarar tsaya mata tayi ilimi domin ta cika burinta, hatta da Yayanda iya karsa babbar makarantar sakandire, ganin bamu da hali yasa bece zai wuce ba haka ya fara sana’a, sai gashi yanzu Allah ya d’aukakashi, ganin haka yace dole Habiba tayi karatu zai tsaya mata, amma yanzu an cutar da ita.
Ra’eez yace insha Allahu sai burinta ya cika. Habiba ina so kisa jarumta aranki, kada kiyi kallon an ruguza maki rayuwa ki hakura da karatun ki, da izinin Allah sai kin d’aukaka, kisa aranki zakiyi karatu, domin shi kad’ai zakiyi kijawoma kanki daraja a wajen kowa, idan kika zama wata babu wanda zaifi karfin ki, amma idan kika sare ma rayuwa haka zakiyi ta cikin kunci, saboda ko aure zakiyi babu wanda zai d’auke ki da daraja, amma idan da ilimin ki zakiga yanda za’a daraja ki.
Kai Habiba ta jinjina tana share hawayen idonta. Jabeer yace duk yanda za’a maki tambaya a kotu kada ki bari a saki fad’in abinda ba shikenan ba, ki tsaya akan gaskiyar ki kuma kada kiji tsoro, koda Brr. Bajinta ya zo yace ki fad’i abinda zai tsara maki kada kice bazaki amince ba, ki bari sai anje kotu sai ki canza abinda ya fad’a ki fad’i abinda kika sani.
Baba yace mungode sosai Allah ya saka maku da alkhairi. Gaba d’aya sukace amin. Amsar lambar wayar Baba Ra’eez yayi yasa masa tashi yana fad’in zamu rik’a magana a waya kafin litinin ashiga kotun.
Baba yace nagode sosai. Tashi sukayi Baba ya rakosu sai godiya yake masu. Bayan ya koma gida Ra’eez yace wallahi duniya babu gaskiya, ka duba fa acikin shedun da Alhaji ya bani hada rahoton likitan daya duba Habiba, saboda shima d’an rashawa ne har ya canza abinda ya gani, amma ka barni dashi dole zai zo kotu zamuji komai, nima zan caza masa kai.
Jabeer yace ai duniya babu gaskiya, da likita, da ‘Yan sanda da Lauyoyi dama ana samun azzalumai, domin kowa kud’i yake so, shiyasa duk inda suke kansu a had’e yake. Ra’eez yace Allah ya kyauta, bara na wuce sai gobe ko.
Jabeer yace gobe juma’a bazan fito da wuri ba. Ra’eez yace kaji d’an gayu, dan Allah kazo da wuri bazanji dad’i ba idan bakanan. Dariya Jabeer yayi yana fad’in shikenan Allah ya kaimu.
Wayar Ra’eez ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Raheena ce, d’agawa yayi. Sallamarta yaji tana mai kwantar da murya, yana amsawa ta fara gaisheshi. Murmushi yayi ya amsa aranshi yana fad’in lallai su Raheena an fara canzawa.
Daga can Raheena tace kira nayi naji yanda ka tashi daga aiki. Ra’eez yace lafiya lau gani zan tafi gida ma. ‘Dan zaro ido tayi tana fad’in biyar fa ta kusa amma baka koma gida ba? Ra’eez yace naje wani waje ne yanzu zan tafi.
Murmushi tayi tana fad’in bara na barka idan kaje mayi waya, ina fatan dai kaci abinci? Ra’eez yace idan naje zanci dai. Raheena tace shikenan kaci dani, amma yaushe zaka zo? Tab’e baki yayi yana fad’in wani aiki zanyi kuma yana buk’atar natsuwa, bazan samu hutu ba har sai na kammalashi.
Raheena tace shikenan amma dan Allah ka rik’a kirana hakan zai mun dad’i naga kiranka awayata. Ra’eez yace shikenan. Sallama sukayi ya kashe wayar.
Har zaisa aljihu wayar ta sake k’ara. Murmushi ya saki yana mai tsinke kiran domin ya kira. Sakin baki Jabeer yayi yana kallonshi.
Pretty na kinga na dad’e ko? Murmushi tayi tana fad’in damuwata rashin cin abincin ka gashi yamma tayi. Ra’eez yace ni kuma damuwata na wuni banji muryaki ba kuma banga fuskarki ba, amma gani nan yanzu zanzo amun kwalliya mai kyau, da nazo na ganki naci abinci sai mu tafi.
Murmushi tayi tana fad’in sai kazo, kayi tuk’i a hankali. Ra’eez yace angama Pretty na, ki kula da kanki. Dariya Jabeer yasa yana fad’in dama haka kake? Ra’eez yace namafi haka, ka zauna nan ayi babu kai, wallahi abokina soyayya dad’i gareta, gaskiya an barka abaya.
Jabeer yace abinda bangane ba shine, yaushe ka fara soyayyar? Ra’eez yace lokacin kana bacci. Dariya Jabeer yasa yana fad’in Allah da gaske nake, nasan dai kace mun kana son Rumaisa kuma nasan baka fad’a mata ba, amma kuma gashi kuna waya kamar wad’an da suka dad’e suna soyayya.