ALKALI NE Page 41 to 50

Ra’eez yace kasan duk soyayyar da aka tara, aka jik’ata ta tsimu ba’a sanin lokacin da ake fara ta, idan kuma aka fara ba’a mata bakunta, to haka tamu take, ajiya muka bayyanata gashi kuma har tabi mana jiki.
Jinjina kai Jabeer yayi yana fad’in lallai kam, soyayya tayi kam, sai nace Allah ya bada sa’a, ga Raheena kuma a gefe. Ra’eez yace ba ruwanka kasa ido kawai kayi kallo.
Jabeer yace hada jiki ma duk zansa, ina jiran ranar da zansha kallon da kyau. Ra’eez yace E naji. Murmushi Jabeer yayi yana fad’in soyayya ko wahala. Ra’eez yace ga wanda bai samu ba ko. Tab’e baki Jabeer yayi yana fad’in kaga Malan sai da safe. Ra’eez yace ai gara katafi ka tsareni da surutu Pretty na jirana.
Murmushi Jabeer yayi yana fad’in agaishe da Pretty to. Ra’eez yace wannan sunan ya fita abakin ka wallahi. Baki Jabeer ya kama yana fad’in yanzu kuwa. Dariya sukasa sukayi sallama kowa ya nufi gida.
****
Ganin yanda Rumaisa tayi kwalliya sai gyare-gyare takeyi yasa Mama ta koma d’aki tana mata dariya dan tasan Ra’eez yakusa dawowa. Abincinsa ta shirya a falo ta koma d’aki wajen Mama.
Zama tayi tana satar kallon Mamar. Murmushi Mama tayi tacigaba da linke kaya. Kallonta Rumaisa tayi tana fad’in wai Mama naji kinyi shiru sai murmushi kikeyi. Mama tace kuka kike son inyi? Turo baki Rumaisa tayi tana fad’in amma ai ba haka kikeyi ba.
Mama tace ya kike so nayi bayan kina ta shiri da alama bak’o zakiyi ban sani ba. Rufe fuska Rumaisa tayi tana murmushi tace ba wani bakon da zanyi kawai fa abincin Yaya ne na aje masa yace sauri yakeyi kada mu makara.
Mama tace naga alama ai, wannan kwalliyar ta zuwa unguwar ce ko? Tashi Rumaisa tayi tana kwalama Abdallah kira. Dariya Mama tayi tana fad’in kwayi ku gama.
Da gudu Abdallah ya shigo hannunsa d’auke da leda yana fad’in Aunty Yaya ya dawo kinga ya siyo mun kayan dad’i. Amshe ledar tayi tana fad’in kawo insha. Abdallah yace kai Aunty yace fa taki tana mota zai baki.
Rumaisa tace ya akayi ka sani? Abdallah yace daya bani nace masa ina taki shine yace ai taki ta dabance tana mota. Murmushi Rumaisa tayi ta d’auki alewa d’aya.
Muryar Ra’eez taji yana fad’in banda kwad’ai dai. Murmushi tayi tashige falo. Da sallama ya k’arasa shigowa. Mama ce ta fito tana amsawa. Har k’asa ya duk’a yana gaisheta.
Amsawa tayi tana masa sannu da aiki. Ra’eez yace kunjini shiru wallahi wani aiki aka bani ranar litinin ma zamu shiga kotu wata shari’a.
Mama tace aifa shari’a bata k’arewa, to Allah ya tabbatar da alkhairi kuma ya baka sa’a. Ra’eez yace amin. Hannun Abdallah taja tana fad’in kashiga kaci abincin mutafi ko. Sosa kai yayi ya kasa tashi. Murmushi tayi ta wuce d’aki, cike da kunya ya shiga falo. Rumaisa tana jin Mama ta shiga d’aki ta fito da sauri.
Tsayawa tayi a bakin k’ofa tana wasa da hannunta. Ido ya tsura mata yana murmushi, takowa tayi tashigo bakinta d’auke da sallama. Amsawa yayi yana fad’in bazaki dena wannan kunyar ba ko? Saurin zama tayi tana masa sannu da zuwa.
Ra’eez yace yunwa nakeji fa. Saurin bud’e abinci tayi ta fara zuba masa. Kallonta yake yana jin sanyi, sosai tayi masa kyau, tasa bak’ar jallabiya ta yane kanta da pink d’in mayafi fuskarta tasha kwalliya mai sauki.
Mik’a masa abincin tayi tana shirin tashi. Kallonta yayi yana fad’in ina zaki? Kanta ak’asa tace abinci zan barka kaci. Murmushi yayi yana fad’in aiko bazanci ba.
Zama tayi tana murmushi tace to kaci. Cokali ya d’auka yana fad’in damma bance ki bani ba. Saurin cusa kanta tayi a cinyoyinta tana murmushi. Murmushi shima yayi ya fara cin abinci yana mata fira.
Bayan ya gama ta kwashe kayan suka fito. Rufe gidan sukayi Madu na jiransu. Shida Ra’eez ne a gaba su kuma suka shiga baya. Suna tafiya Ra’eez yace wai Mama ina Aunty Hassana kullum ina so na tambayeki ita? Mama tace Allah sarki Sister Hassana sarkin kirki, ai sun dad’e da tashi, tunda aka canzama mijinta wajen aiki itama ta nemi canjin wajen aikinta suka tafi suna Abuja.
Ra’eez yace lallai kunyi nisa sai dai waya. Mama tace tana kirana muna gaisawa kuwa ai tana da kirki har cewa tayi zata zo ta d’auki Rumaisa taje mata hutu can.
A zabure Ra’eez yace ba dai Abuja ba wallahi, waye zai kaita haka kawai mayun garin nan su sa mata ido. Dariyar da Madu yayi ce ta ankarar dashi abinda yayi. Hannu yasa yana sosa kai.
Rumaisa kuwa duk’ewa tayi tana murmushi. Mama tace ni kuwa har na amince mata k’arshen wata zata zo su tafi. Kicin-kicin yayi da fuska yana kallon Rumaisa ta madubin motar, be sake magana ba kawai yayi shiru.
Murmushi Mama tayi tana kallonshi. Madu yace ai Halima baza’ayi haka ba, Ra’eez shine babba kuma shine namiji, dole sai ya amince zata je ko Ra’eez? Fuska a d’aure yace bazan amince ba ma, dan hadda zata fara babu inda zataje hutu.
Dariya Mama tayi, yanda yayi maganar kasan haushi ne yake cinsa. Madu yace angama Alhaji Ra’eez nima ban amince ba. Mama tace ai shikenan tunda kun fini k’arfi. Murmushi Ra’eez yayi yana shafa gefen fuskarshi.
Wajen Kawu suka fara zuwa dan kada magriba tayi. Zaune suke a cikin d’akin da ake ganawa da masu laifi. Bayan sun gama gaisawa da ma’aikacin wajen wanda dama sun saba da Ra’eez, shine ya aika akira Malan Sani.
Kallon Ra’eez yayi yana fad’in ya aiki kuma? Ra’eez yace aiki muntashi sai gobe kuma. Yace to Allah ya taimaka, bara na baku waje ku gaisa. Godiya Ra’eez yayi masa ya fita.
Tunda Malan Sani ya tunkaro wajen idanuwan Mama suka cika da kwallah, da gudu Abdallah yaje ya taroshi, duk ya tsufa saboda wahala, sai dai har yanzu jikinsa akwai jarumta, dan yasa dakiya aranshi hakan yasa zuciyarsa bata raunana ba bare ta shafi lafiyarsa.
Yana zuwa Ra’eez ya tashi yana gyara masa wajen da zai zauna. Zama yayi murmushi d’auke a fuskarshi. Hannu ya mik’ama Madu suka gaisa yana tambayarsa rayuwa.
Har k’asa Ra’eez da Rumaisa suka duk’a suka gaishe da Malan Sani. Kamosu yayi yana murmushi yace lafiya lau ina fatan ana kula da karatu Rumaisa? Kai ta jinjina tana b’oye hawayen da suka taho mata.
Kallon Mama yayi ganin ta kasa magana sai share hawaye. Wani abu ya had’iye yana fad’in Halima kuka dai, shiyasa fa bana so kina zuwa domin kina raunana mani zuciya, bayan kin tafi kuma ina jinyar zuciyata, ina tsoron kada hakan ya fara tab’a lafiyata, idan bazaki rik’a dakewa ba gara ki zauna agida sai murik’a gaisawa ta waya.
Hannu tasa ta goge idonta tana fad’in na dena, gaishesa ta farayi. Murmushi yayi yana fad’in lafiya lau ya gidan? Bazan tambayi komai ba domin nasan ina da masu kula da ku, sannan idanuwana sun ga abinda nake son gani, kuma naji dad’i a zuciyata.
Ra’eez yace Kawu Abbah yace idan nazo zaku gaisa bara na kirashi. Malan Sani yace Allah sarki ya iyalan nashi? Ra’eez yace lafiya lau. Waya ya d’auka ya kira Abbah.
Bayan sun gaisa ya mik’ama Malan Sani. Gaisawa sukayi yana tambayarsa rayuwa. Malan Sani yace lafiya lau Alhaji, ai rayuwar gidan yari tabi jikina, nasa araina nan d’in Muhallina ne, domin ina son naga ranar da Allah zai kawo mani k’arshen zama acikinta, ina son nayi wata rayuwar hakan yasa nasa juriya araina dan gudun damuwa ta kassarani.