ALKALI NE Page 41 to 50

Alhaji Mansur yace wannan haka yake, kuma naji dad’i sosai, dama abinda nake son na fad’a maka kenan, domin acikin satin nan bani da tunani sai na yanda zamu maido da shari’ar ku baya, domin kwanakin baya na had’u da tsohon ma’aikacin Alhaji Abubakar, dan yanzu a Kano yake aiki shima ya zama babba, Allah ne yasa zamu had’u har labari ya kawo muka zo maganar Alhaji Maiwada, ya tabbatar mani a yanzu baya tsoron kowa, kuma duk lokacin da muke buk’atar taimakonsa ashirye yake, abokinsa da aka canza ma wajen aiki Moses shi ya mutu a had’arin mota, amma yace shi zai zo ya bada sheda.
Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad’in wallahi nima kwanan nan mafarkin da nake yawanyi kenan, wai an sake shari’a kuma munyi nasara, ina nan ina fad’ama Allah nasan kuma zai shige mana gaba, ko ban fita a nan ba matuk’ar asirin azzalumancen zai tonu burina ya gama cika.
Alhaji Mansur yace zaka fita, matuk’ar asirin su ya tonu dole a wanke ka, dan haka kacigaba da daurewa komai zai zo k’arshe. Malan Sani yace insha Allah. Sallama sukayi ya kashe wayar.
Sai da yaci abincin da suka kawo masa suna ta fira, bayan ya gama Ra’eez ya bashi ledar da suka kawo masa mai d’auke da kayan bukata, kud’i ya bashi yana fad’in zamuje wajen Ummu.
Godiya Malan Sani yayi masa yana fad’in agaisheta. Tashi sukayi kowa jikinsa a sanyaye, duk dauriya irin ta Malan Sani sai da kwalla ta cika masa ido, azuwansu sai yaji damuwarsa ta yaye, yanaji kamar a gida suke zaune, amma yanzu da zasu tafi sai yaji duk babu dad’i.
Mama kuwa saurin fita tayi tana kuka, bayanta Rumaisa tabi itama kukan takeyi, kama Abdallah Madu yayi sukayi hanyar fita shima jikinsa a sanyaye. Kallon Malan Sani Abdallah yayi yana fad’in Baba sai yaushe zakazo gidan mu? Saurin juya baya Malan Sani yayi hawayen da yake b’oyewa suka zubo masa, yana jin muryar Abdallah amma ya kasa magana, ganin haka yasa Madu yayi saurin jansa sukayi waje.
Hannu Ra’eez yasa ya goge idonshi kafin ya dafa Malan Sani yana fad’in Kawu zamu tafi sai mun sake dawowa. Ajiyar zuciya ya saki yana fad’in Ra’eez kada ka sake kawo su, idan zaka zo kazo kai kad’ai dan Allah.
Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in insha Allah. Tare suka fito suka k’arasa wajen ma’aikacin. Kallonsu yayi cike da tausayi yana fad’in zaku koma? Ra’eez yace magriba ta kusa, mungode sosai.
Hannu yasa ya ciro kud’i ya mik’a masa yana sake masa godiya. Amsa yayi yana fad’i ai babu komai nima nagode. Sallama yayi masu Malan Sani ya d’auki kayanshi ko juyowa beyi ba yayi gaba yana kuka.
A mota gaba d’ayansu shiru sukayi kowa yana jimami, Abdallah kanshi da yake yaro shiru yayi ya kwanta jikin Rumaisa yana goge mata fuskarta, har suka isa asibiti babu mai magana.
Sai da Ra’eez yayi ma Dr. Sadeek waya, dan yanzu ya zama babba baya aiki a asibiti sai dai sune masu kula da wajen, hakan yasa ya damk’a Ummu a hannun babban likitan da yake wajen duk da idan yashigo yana kawo mata ziyara.
Bayan sun gama wayar suka fito suka nufi d’akin da Ummu take. A zaune suka isketa tana sanye da hijabi ta kurama tv ido wadda ake shirin addu’ar safe da marece, wata dattijuwa ce zaune a gefe da alama itace take kula da ita.
Idan kaga Ummu sai ka d’auka mai hankali ce, domin komai fess a jikinta, fuskarta ta nuna alamun manyanta kad’an saboda tana samun kulawa ga cima mai kyau sai fatar ta tayi kyau sosai, sam yanzu bata komai sai dai wani lokacin idan ta fara kuka tana kiran Abbun Ra’eez sai ta kai wani lokaci ta nayi, wani lokacin dole sai anyi mata allurar bacci kafin suke samun saukinta.
Wani lokacin kuma sai tayi sati bata nuna alamun hauka ba, magana ma batayi sai dai mai kula da ita ta rik’a kula da abinda take so tayi mata, dan yanzu kam ta zama shiru-shiru, idanuwanta duk sun canza kala sun rage girma saboda kuka.
Da sallama suka shiga d’akin, matar da take zaune tayi saurin amsawa ta mik’e tana masu sannu da zuwa. Har suka shigo Ummu bata kalli inda suke ba, yanda kasan bata cikin d’akin dan yau ‘yan miskilancin take.
Bayan sun gaisa da matar ta basu waje tayi waje. Ido Ra’eez ya tsura ma Ummu kwalla tana cikowa a idonshi, kusa da ita ya matsa yana mai kamo hannunta.
Shiru tayi bata kulashi ba. Zama yayi ya jawota hawaye suna gangarowa a fuskarshi. Mama dasu Rumaisa duk sai sukaji wani sabon kuka, a hankali Ra’eez yace Ummu kiyi hak’uri aiki ne yamun yawa shiyasa banzo ba amma bazan sake ba.
Tamkar bada ita yayi magana ba haka ta kyaleshi idanuwanta suna kan Tv tamkar mai fahimtar abinda akeyi. Matsowa Mama tayi ta kamo Ra’eez tana fad’in kayi shiru mu bata lokaci zatayi magana idan ka tursasata kanta zai iya d’aukar zafi.
Zama sukayi kowa da abinda yake tunani, Ra’eez kam yana rik’e da hannun Ummu yaki sakinta. Can yayi saurin kallonta yana fad’in Ummu jiya fa nayi mafarkin Abbu ina kwance a kan gadonshi har… Zumbur tayi tana kallonshi, kamoshi tayi tana fad’in Abbun ka? Nima jiya yazo mun anan ma ya kwana, hannu tasa tana buga gadon da take zaune.
Murmushi sukayi dukansu, Ra’eez yace Ummu meyasa baki tsaidashi har nazo ba? Dariya tayi tana tafa hannu tace ai yau idan yazo igiya zansa na d’aureshi, jiya nace ya zauna tare dani shine yamun wayau ya gudu, amma ka barshi yau sai na d’aureshi kaga bazai sake barina ba ko.
Murmushi Ra’eez yayi ya gyara zama tare da d’ora kanshi saman cinyarta yana fad’in sosai ma Ummu, zan kawo maki igiya ki d’aure manashi kullum murik’a ganinshi.
Nan fa Ummu ta saki jiki da Ra’eez sukayi ta firar Abbu, haka ya biye mata yana taya ta shirme duk dan suyi labari, Mama da Madu kuka kawai sukeyi a b’oye ganin yanda Uwa da ‘Danta suke fira ta marasa hankali.
Cikin firar sai dai Ra’eez yasa hannu ya goge hawayen da suke zubo masa saboda firar tana sakashi shiga cikin yanayi, ita ko Ummu dariya kawai takeyi suna firar Abbu.
Da haka Mama ta zuba mata abinci, amsa Ra’eez yayi suna fira yana bata abaki, itama haka tarik’a bashi, duk da akoshe yake haka yake amsa yanaci yana hawaye.
Bayan sun gama tacigaba da bashi labarin shirmenta. Har akayi sallah suka fita shida Madu da kyar ma ta yarda suka tafi. Bayan sun dawo ta jawo Ra’eez tana fad’in kaima yau anan zaka kwana idan Abbunka yazo sai muyi fira muci abinci gaba d’aya.
Murmushi Ra’eez yayi ya haye saman gadon yana fad’in tabbas anan zan kwana Ummu muga Abbu atare. Wayarsa ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Alhaji Barau ne, tsaki yayi kafin ya d’auka.
Bayan sun gaisa ya fad’a masa idan anyi sallar isha’i yana nemansa muhummiyar magana ce. Ra’eez yace shikenan sai nazo, kashe wayar yayi yana tsaki.
Mama ce ta tambayeshi wanda ya kira? ‘Bata fuska yayi yana fad’in Alhaji Barau ne wai yana… K’arar da Ummu tasa ne yasashi saurin yin shiru. Kular abincin da take kusa da ita tayi wurgi da ita tana fad’in sai na kashe shi, wallahi sai na kashe shi, Abbunka baya sonshi, ya takura ma Abbunka.
Saurin tashi Ra’eez yayi yana kok’arin rik’eta amma ya kasa, da sauri Madu ya fita domin kiran ma’aikatan, kafin suzo duk ta hargitse wajen tana ihu, hannun Ra’eez kuwa duk taji masa ciwo.
Allura akayi mata cikin mintuna biyu bacci ya d’auketa. Zama Ra’eez yayi tare da sakin wani irin kuka mai cin rai. Kamoshi Madu yayi yana lallashinsa.