ALKALI NE Page 51 to 60

Har na gama abinda zanyi da ita su maida ta bata tab’a sanin abinda ya faru, hakan yasa nakeyin komai hankali kwance, yayin da wasu matan sune suke kawo kansu gare ni.
Tun ranar dana fara ganin Halima na kwad’aitu da ita, duk da itace mafi k’arancin shekaru da nasan na tab’a hayk’emawa, naso na cireta araina saboda ganin k’arancin shekarunta amma hakan beyuwu ba, nafi wata ina fama da kwad’ayinta, nayi yaki sosai da zuciyata amma shed’an yariga ya kwad’aita mani ita, a hankali na fara mata magana sai dai bata tsayawa kula ni, kasancewar ta hanyar gidan mu take wucewa zuwa makaranta yasa duk lokacin da zata wuce ni kuma nake fitowa domin na ganta.
Ganin na rasa hanyar da zanbi yasa kawai nayi amfani da abinda nakema sauran matan, Halima itace mace ta farko dana tab’a kaita cikin gidan mu da sunan fyad’e, domin duk abuna banayi agida, sai dai idan sauran ‘Yan matana ne su wannan ina kawosu har d’akina, sai gashi na kasa hak’ura akai mani Halima inda nake kai sauran matan.
Wata rana da yamma ina zaune na gama had’a komai ina jiran wucewarta, tun ina jiranta har na fara fidda rai saboda aranar ta makara, har na tashi zan koma gida na yanke shawarar zansa a sato mani ita sai kawai na ganta zata wuce, farin ciki nayi, kasancewar unguwar mu bata da hayaniya yasa nayi saurin shan gabanta.
A tsorace tayi baya tana neman hanyar guduwa amma nayi saurin saka mata kyallen hannuna, dama na aiki mai gadin gidan mu, saurin d’aukarta nayi muka shige ciki.
Ajiyar zuciya ya saki hawaye suna zubo masa, kallon Halima yayi yana fad’in ban tab’a aikata fyad’en da nakasa samun natsuwar zuciya ba sai akanta, sam bana baccin kirki.
Bayan da komai ya faru sai gashi ta farka, nayi mamakin farkawarta domin maganin yana da k’arfi, amma sai ta farka kuma ta sheda ni, ganin haka yasa na tsoratar da ita, tashi tayi ta bar gidan, sai da nabi bayanta naga tayi hanyar gidansu, agaban idona ta zube hakan ya tabbatar mani maganin bai saketa ba, komawa nayi gida har lokacin maigadi bai dawo ba.
Bayan nashiga d’aki jinin da nagani ya tashi hankali na, saurin shiga wanka nayi amma jikina yana rawa, kasa daurewa nayi na kira d’aya daga cikin yarana nace yayi sauri yaje yaga halin da take ciki kuma ya gano mani asibitin da za’a kaita.
Ina tsaye a harabar gidan mu sai ga Dady, ganin da yayi mani cikin tashin hankali yasa ya tambaye ni, bana masa k’arya hakan yasa na fad’a masa komai, nan take yace kada na damu na bari muji asibitin da za’a kaita.
Muna nan Gayen ya kirani ya sheda mani yaga Mahaifinta ya samo mota sun nufi asibitin Dr. Kaseem, mamaki ne ya kamani nasan talakawa ne amma suka nufi asibitin kud’i, Dady yace kila baya son ya kaita babban asibiti atsaya b’ata masu lokaci wajen kiran ‘yan sanda shiyasa ya kaita can.
Nan take Dady yakira Dr. Kaseem ya fad’a masa halin da ake ciki, kuma yace kada a karb’i kud’in su. A lokacin ya fita amma yace zaiyi sauri ya koma asibitin kuma zai rufe komai.
Wannan dalilin ne yasa Dr. Kaseem ya kori sister Asabe ya duba Halima kuma ya rubuta bayanin k’arya, domin yace har d’inki yayi mata.
Bayan kwana biyu da faruwar haka sai muka samu labarin an kaini kotu, hankalina yayi matuk’ar tashi, kuka nasa Dady yace kada na damu babu abinda zai faru, nan take yakira Dr. Sa’eed ya fad’a masa abinda yake so, babu b’ata lokaci ya shirya sakamakon k’arya akan rashin lafiyata, har gida ya kawo ma Dady suka tattauna yanda komai zai kasance, haka ya cika masa jaka da kud’i ya tafi.
Wallahi tun daga lokacin da haka ta faru ban sake samun natsuwa ba, hakan yasa a yanzu naga ya dace na fad’i gaskiya, kuma zan amshi ko wane hukunci aka yanke mun.
Shiru kotun tayi ana sauraren kukan Sameer. Dadynsa kuwa zama yayi jiki a sanyaye yana goge zufa, gashi d’an siyasa yana tsoron hakan ya tab’a masa mutuncinsa.
Jiki a sanyaye Alkali ya gama rubutu, gaba d’aya kunyar kallon Mahaifin Sameer yakeyi, babu yanda ya iya, Allah ma yaso Sameer ne ya tona komai yasan bazasu zargeshi ba.
Bayan ya kammala rubutu ya d’ago yana kallon Sameer…… Bisa hujjojin da aka gabatar ma wannan kotu da kuma samun babbar sheda daga bakin wanda ya aikata laifi cewar ya amince shine ya aikata wannan laifi, wannan kotu mai adalci ta yanke ma Sameer hukuncin daurin wata biyar agidan yari ko kuma tarar naira dubu d’ari biyar, sannan zai biya Halima tarar naira million talatin domin keta mata haddi da yayi, haka kuma zai cigaba da kula da lafiyarta har ta samu sauki, sannan idan rabo yashiga tsakanin su zai kula da ita har ta haihu da bayan ta haihu har zuwa lokacin da zata yaye abinda ta haifa ta bashi abunshi, idan kuma zata rik’e masa to shine yake da alhakin kula dasu.
Dr. Kaseem da Dr. Sa’eed zasu biya tarar dubu hamsin-hamsin bisa kamasu da akayi da kawo ma kotu shedar k’arya, idan aka sake kamasu da makamancin irin wannan laifin kotu zata soke lasisin su.
Kallon mutane yayi yana fad’in ina fatan wannan hukunci zai zama izna ga sauran mutane. Saurin tashi Brr. Bajinta yayi yana fad’in ina neman alfarmar wannan kotu data k’ara ma Sameer tarar da zai biya Halima saboda ya keta mata haddi, ya rabata da abinda yafi komai muhimmanci agareta. Nagode ya mai shari’a.
Jin jina kai Alkali yayi yana fad’in bisa duba da k’orafin lauya mai kare Halima wannan kotu ta amshi rokon ka, dan haka Sameer zai biya Halima tarar naira million hamsin, kuma dole ne ya biyasu akan lokaci… Kotttt.!!!!!
Gaba d’aya kowa ya tashi ana jinjina ma Alkali bisa hukuncin adalcin da ya yanke, haka kowa yarik’a masa jinjinar ban girma, wannan adalci da kowa yake samu yasa suke k’ara son Alkalin su.
Hannu Brr. Bajinta ya bama Ra’eez yana fad’in a wannan shari’ar dai na kada ka, amma duk da haka kayi kok’ari, nan gaba sai kayi kok’arin kada ni.
Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in na tayaka murna, amma nan gaba ka rik’a kok’arin tsayawa akan aikin ka kadena kok’arin juya akalar kariyar ka zuwa ga wani daban, sannan karika aikata abinda ya dace ba sai an fad’a maka ba.
Cira idanu ya fara yana yaken dole dan ya tuna d’azu da Ra’eez ya duko yana fad’a masa yayi sauri yatashi ya nemi a k’ara ma Halima kud’i hakan zaisa ya wanke kansa wajen mutane, hannunsa ya cire yana fad’in haka ne, kuma nagode.