ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

Murmushi Rafeek yayi yana fad’in zamu kula insha Allah. Likita yace ba sai mun kwantar dashi ba zaku iya maidashi gida tunda nasan zaku kula dashi acan. Rafeek yace likita inaso ka bashi gado ko na kwana biyu ne, domin Ra’eez yana da buk’atar hutu sosai, idan ya koma gida bazai iya hak’ura beje aiki ba, koda munce kada yaje acan wajen aikin bazasu gane beda lafiya ba, amma idan suka san yana kwance a asibiti dole zasu d’aga masa k’afa. 

Jinjina kai likita yayi yana fad’in shikenan bara a bashi VIP room domin babban mutum ne. Dariya Rafeek yayi yana fad’in lallai kanaji da Ra’eez, ko dai ya tab’a tsaya maka ne? Murmushi likita yayi yana fad’in ko d’aya, ban tab’a zuwa kallon shari’arsa ba ma, kawai dai yanayin aikinsa ne yake burgeni, domin an bani labarin shari’arsa ta farko, sannan an bani labarin wadda yayi wancan satin, tun daga lokacin kawai nake sonshi. 

Rafeek yace to mungode, akwai magungunan da za’a siyo ne? Likita yace yanzu kam tunda a nan za’a barshi zamuyi masa komai, kuma nine zan biya domin gwarzo na ne. 

Tashi Rafeek yayi yana fad’in nagode abokina. Likita yace haba bakomai, muje akaishi d’akin saboda akwai allurar da zan saka masa a ruwa wadda zata sashi bacci mai k’arfi. 

***

Sai da aka gama masa komai kana Rafeek yace ma Jabeer yaje gida ya fad’ama su Momynsa tunda yace anan zai kwana, amma kada ya fad’a ma Maman Rumaisa tunda dare yayi abarsu zuwa gobe. 

Jabeer yace ai ba sai naje ba sai nayi masu waya kawai. Rafeek yace baza’ayi haka ba, kwanciya asibiti tana buk’atar shiri, kaje ka fad’a masu nasan kaima bazaka rasa abinda zaka d’auko ba. Jabeer yace shikenan bara naje ai kana nan ko? Rafeek yace ina nan har sai ka dawo zan tafi. 

***

Bayan mintuna Jabeer ya dawo. Haka Rafeek yayi mashi sallama yace zuwa safe zaizo ya kawo masu kayan kari. Godiya Jabeer yayi masa, har bakin mota ya rakashi sannan ya dawo. 

*** ***

Washe gari wajen k’arfe bakwai da rabi Rafeek ya iso asibiti ya kawo masu kayan kari, alokacin Ra’eez ya fito daga wanka yana zaune ya idar da sallah, dan Jabeer be tashe shi da asuba ba ganin yanda baccinsa yayi nauyi. 

Tashi yayi jiki a sanyaye dan har lokacin baya jin kwarin jikinsa, zama yayi yana gaishe da Rafeek. Matsowa yayi yana fad’in Ra’eez ya jikin? Ra’eez yace da sauki nagode Yaya. 

Zama yayi yana fad’in kadena gode mani domin duk abinda zanyi maka dan Allah ne nayi, dan haka bana son godiyar ka, kallon Jabeer yayi yana fad’in kaci abinci kaje gida ka shirya sai ka sanar ma su Mama bayan ka shiryo ka taho da ita sai ta zauna dashi kafin mu taso. 

Tashi Jabeer yayi yana fad’in ka had’a masa abincin idan naje gida zanci ni. Rafeek yace shikenan amma ka biya ka fad’a masu kaga kafin ka shiryo itama ta gama shiryawa. Jabeer yace to. Sallama yayi masu yana fad’in Ra’eez sai na dawo. 

**** 

Cike da damuwa Mama ta kalli Jabeer tana fad’in shiyasa nace ya dawo nan da zama yana ganin mu bazai rik’a damuwa ba, amma ya je ya zauna acan dole yarika damuwa, a d’akin Abbunsa fa yake kwana a saman gadonshi, taya bazai d’aura aure da damuwa ba, amma ka barni dashi dole ya dawo nan duk da yafi sabawa da can amma bazan bari wani abu ya sameshi ba. 

Jabeer yace haka ne Mama, nima tunda wannan abun ya faru nake wani tunani, amma mujira asallamosa sai musan abunyi. Mama tace shikenan kaje ka shiryo zan k’arasa aiki kafin ka dawo, abinci ma Rumaisa zata tsaya tayi idan ta gama sai ta same ni can ai tasan asibitin. 

Jabeer yace shikenan sai na dawo. Kallon k’ofar d’akin Rumaisa yayi yana murmushi dan tunda ya shigo ya fara magana ya ganta tsaye tana hawaye. Suna had’a ido tayi saurin sakin labulen. Murmushi yayi yana ma Mama sallama ya fice. 

**

Ko da sukaje alokacin Ra’eez ya koma bacci anyi masa allura bayan yaci abinci yasha magani. A tare da Rafeek suka fito zasu wuce aiki, Mama sai godiya take masu. Bayan sun tafi ta zauna cike da tausayin Ra’eez. 

***

K’arfe 12:00 Rumaisa ta iso asibitin, waya tayima Mama ta fito suka shiga ciki, a bakin k’ofar shiga suka had’u da likita tare da Alhaji Barau da Brr. Bajinta. 

A jingine da filo suka iskeshi yana shan lemun da Mama ta bashi kafin ta fita. Da sallama suka shiga. Kallonsu yayi da idanuwanshi da suka fad’a a dare guda. 

Murmushi yayi yana masu sannu da zuwa. Shigowa sukayi Alhaji Barau yana fad’in kaga ikon Allah ko Brr. Bajinta, jiya fa mukayi waya yace mun ya dawo lafiya ashe a asibiti ma zai kwana. 

Brr. Bajinta yace aishi ciwo beda lokaci, idan mutuwa ce ma haka zamu jita daga sama. Hannu ya mik’ama Ra’eez yana fad’in sannu ya k’arfin jikin? Ra’eez yace da sauki. 

Gaishe da Alhaji Barau yayi. Alhaji Barau yace lafiya lau ya jikin? Ra’eez yace da sauki sosai. Su Mama suna gefe tashiga gaishe su. Kallonta Alhaji Barau yayi yana fad’in lafiya lau ya mai jiki? Mama tace da sauki. 

Tashi sukayi Alhaji Barau ya aje kud’i masu yawa a gefen Ra’eez yana fad’in ban siyo komai ba ga wannan an saya masa lemu Allah ya k’ara lafiya, zuwa anjima da dare zamuzo tare da Hajiya, amma nasan Raheena tanaji zata taho nan. 

Godiya Ra’eez yayi mashi fuskarsa a d’aure. Brr. Bajinta yace to Allah ya k’ara lafiya. Sallama sukayi ma su Mama suka fice. Tsaki Ra’eez yayi yana jin wani bakin ciki, hannu yasa ya ture kud’in daya aje suka fad’i k’asa. 

Matsowa Mama tayi tana fad’in munafikin Allah, da yardar Allah k’arshensa bazeyi kyau ba, zezo ya kawo ma mutane kud’in haram. 

A hankali Ra’eez yace Mama d’auke su nadena ganin su, ki ajesu idan kika fita ki badasu sadaka. Mama tace sai dai sadakar, amma wallahi ko da yunwa nake kwana bazan iya cin kwandalar munafuki ba. 

Kwashe su tayi ta nemi bak’ar leda tasa sannan tasasu ajaka. Matsowa Rumaisa tayi idanuwanta cike da kwalla, tsaye tayi a gefen gadon tana wasa da yatsunta. 

Tashi Mama tayi tana fad’in bara naje waje kila na samu mabarata. Har ta fita Rumaisa bata d’ago kai ba sai hawayen da suke sakko mata. 

Tsura mata ido Ra’eez yayi shima idanuwanshi cike da kwalla, a hankali yasa hannu ya jawota ta fad’o jikinshi, kamar jira take ta kifa kanta tare da sakin kuka. 

Lumshe ido yayi hawaye masu zafi suka sakko mashi, tabbas daga jiya zuwa yau yana jin wani irin ciwo a rayuwarshi, amma dole yasa jarumta aranshi matuk’ar yana so yabar asibitin nan gobe. 

Sun dad’e a haka yana bubbuga mata baya, a hankali tayi shiru tana ajiyar zuciya. Duko da kanshi yayi yana fad’in Pretty kinaso ciwo na ya tashi ne, kinsan dai kukan ki yana d’aga mani hankali sosai, gashi jinina ya hau idan kina kuka zai k’ara hawa. 

Saurin tashi zaune tayi tana goge idonta. Murmushi yayi yana fad’in ashe dai ba’aso na mutu? Turo baki tayi tana fad’in dan Allah Yaya na kadena maganar mutuwa. 

Waro ido yayi yana fad’in yau kuma na koma Yaya? Kai ta girgiza tana murmushi. Ra’eez yace to afad’amun sunan. Murmushi tayi tace kai Annur! Dariya yasa yana fad’in yanzu naji. 

Tashi tayi ta zuba masa abinci, gyara masa filo tayi ya gyara zamansa kafin ta mik’a masa filet d’in. Ido ya tsura mata be amsa ba, jin shiru yasa ta kalleshi. Turo baki yayi yana mak’ale hannu a baya. 

Murmushi tayi ta zauna gefen gadon ta fara bashi abaki. Haka yarik’a amsa idan yaci d’aya sai yace dole sai taci dan yasan bataci komai ba saboda rashin lafiyarsa. Haka suka cinye hada k’ari, abincin da sukaci sunyi mamaki dan basu san sunci ba. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button