ALKALI NE Page 51 to 60

Wajen k’arfe 3:00 Jabeer ya iso, a d’akin waje ya iske Mama tana jan carbi Abdallah yana gefenta wanda Rumaisa taje ta d’aukosa a makaranta.
Duk’awa yayi suka gaisa yayi mata ya mai jiki. Mama tace yaji sauki sosai suna ciki kashiga. Tashi yayi yana fad’in Allah ya k’ara sauki.
Yana tura k’ofar Rumaisa tana kok’arin bama Ra’eez aiba a baki. Cak ta tsaya tare da duk’ar da kai tana murmushi. Da sallama yashigo yana murmushi.
Harara Ra’eez ya aika masa yana gyara zamanshi. Zama Jabeer yayi yana fad’in ae dole a tura Mama waje ashe ana nan ana…. Da sauri Rumaisa tayi waje cike da kunya.
Dukan wasa Ra’eez ya kaima Jabeer yana fad’in wannan ai wulakanci ne mutum yana jin dad’i da iyalinsa azo a takura masa.
Jabeer yace lallai kam Yaro ka samu, banda wukalanci a asibiti zaku zo kuna soyayya saboda rashin kunya kayi wani kwance ana baka abinci abaki.
Ra’eez yace wani ma ya samu hakan, kaga malan bana son sa ido. Dariya Jabeer yayi ya bashi hannu suka gaisa yana tambayarsa jiki.
Ra’eez yace da sauki sosai, ai Pretty tana zuwa naji na warke gabad’aya. Jabeer yace da alama yau ita zamu bari ta kwana kaga kafin gobe sai ka koma dai-dai.
Dariya Ra’eez yasa yana fad’in wallahi baka da kirki, mutumin ka fa yazo shida d’an kazaginsa. Jabeer yace ina zuwa na fad’a mashi shine yace dole yazo ya dubaka.
Ra’eez zeyi magana aka turo k’ofa, Raheena ce tashigo bakinta d’auke da sallama. Jabeer ne ya amsa yana mata sannu da zuwa. Wani b’acin rai ne ya ziyarci Ra’eez, shikenan zatasa Pretty cikin damuwa.
Cikin sauri ta k’ara so idanuwanta suna kawo ruwa, gefen gadon tazo zama da sauri Ra’eez yasa k’afarsa a wajen yana mata nuni da kujera. Jiki a sanyaye taja kujera ta zauna ta fara gaishe su.
Tashi Jabeer yayi yana fad’in matso da kujerar jikin gadon keda kika zo jinya. Murmushi tayi ta matso tana tambayar Ra’eez jiki. Zamewa yayi ya kwanta yana amsawa.
Kallonshi tayi tana fad’in sannu Dear, wallahi bakaji yanda hankalina ya tashi da Dady ya fad’a mun ba, tare muke da Momy tana wajen wasu anan da alamu ‘yan uwanka ne shine ta tsaya suna gaisawa.
Kai Ra’eez ya jinjina yana fad’in nagode. Momy ce tashigo bakinta d’auke da sallama. Jabeer ne ya amsa mata yana mata sannu. Bayan ta zauna suka gaisheta tayima Ra’eez sannu.
Kallon Raheena tayi tana fad’in to ke haka ake zuwa jinyar bazaki zuba abinci ki bashi ba? Murmushi Raheena tayi tana fad’in Momy yanzu zan zuba mashi ai.
Momy tace yauwa, matsa ki zauna gefen gadon ki bashi ba sai ya wahalar da hannunsa ba. Saurin juyawa Jabeer yayi ya fita saboda dariyar da ta taho mashi. Da sauri Ra’eez yace akoshe nake yanzu naci abinci.
Raheena zatayi magana sai ga Rumaisa ta shigo da sauri, tunda taga Raheena hankalinta ya kasa kwanciya musamman da Momy ta fad’a masu daga inda suke.
Ganin Raheena akusa da gadon Ra’eez yasa tayi saurin k’arasawa, bata san lokacin data zauna gefen gadon ta kamo hannun Ra’eez tana fad’in Annur baka buk’atar komai ko? Runtse ido Ra’eez yayi ganin Rumaisa zata rusa masa shiri.
A firgice Raheena ta kalli Rumaisa jin abinda tace. Ganin Ra’eez ya runtse ido yasa Rumaisa tayi saurin sakin hannunsa tana fad’in Yaya dama fa Mama tace nazo na tambayeka idan akwai abinda kake buk’ata tunda taga surikarta tazo jinya.
Murmushi ne ya sauka a fuskar Raheena da Momy wad’an da sukayi zuru suna jiran k’arin bayani. Da sauri Ra’eez ya bud’e idonshi jin abinda Rumaisa tace, a cikin idanuwanta ya sauke nashi, sai dai ganin yanda idanuwanta suka canza yasashi gano tsananin kishi a ciki.
Da sauri Raheena tace lallai wannan k’anwar tamu tana ji da Yayanta, kada ki damu ina nan zan bashi duk abinda yake buk’ata, idan kina son zuwa gida ki huta zaki iya tafiya dan sai dare zan bar nan shima dan bazeyuwu na kwana anan ba da zan kwana dashi.
Momy tace sosai kuwa, tunda kinzo zasu iya tafiya su huta dan nasan tun safe suke nan. Kai Rumaisa ta jinjina dan bazata iya magana ba tayi saurin barin d’akin.
Runtse ido Ra’eez yayi cike da jin haushin Raheena da Momynta, yasan Rumaisa zata shiga damuwa, ko abinda tayi ganin ya rufe ido ne yasa ta fad’i haka kuma ya gano da biyu ta fad’a.
Tashi Momy tayi tana fad’in Ra’eez Allah ya k’ara sauki, zan tafi na barku kuyi firar ku, Raheena idan direba ya maidani zai maido maki motar sai ya koma gida saboda idan kin tashi komawa sai kiyi amfani da ita.
A hankali Ra’eez yace nagode. Raheena tace Momy sai na dawo. Momy tace ki kula dashi sosai fa. Raheena tace to Momy.
Sallama tayi masu Mama ta wuce. Jabeer da yake kok’arin shiga yaji abinda ya faru dan tunda yaga Rumaisa ta fito idanuwanta jawur yasan akwai abinda ta gani.
Yana shiga Ra’eez yayi saurin tashi yana fad’in Jabeer kayana akwai matsala fa, kaje ka gyara komai bana so asamu matsala suyi kura. Murmushi Jabeer yayi yana fad’in da alamu ajiyar tayi kura sosai, bara naje na kakkab’e kada k’ura tayi mata illa.
Kwanciya Ra’eez yayi yana fad’in kayi sauri dan Allah. Raheena tace Dear meyasa zaka aje kaya baka rufe ba ai dole k’ura ta b’ata su, Allah yasa ba fararen kaya bane nasan dole a sake wanke su????.
Kasa rik’e dariya Jabeer yayi da sauri ya fita yana fad’in farare ne tass sosai Raheena yanzu zanje na gyara komai. Raheena tace sai ka dawo. Murmushi kawai Ra’eez yayi yana lumshe ido jin abinda Jabeer ya fad’a.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣4⃣
Saurin b’oye fuska Rumaisa tayi tana kok’arin goge hawayen da suke fuskarta jin labarin da Jabeer ya bata. Murmushi Jabeer yayi yana fad’in a mana afuwa matar lauya, laifin mu ne da bamu fad’a maki shirin mu ba, amma yanzu ina fatan kin fahimci labarin dana baki, sam Ra’eez baya son Raheena, yana so shima ya rama abinda akayi ma Abbunsa ne.
Jinjina kai Rumaisa tayi tana fad’in Allah ya so ban kwafsa ba, ai da farko kansu ya d’aure da na kirashi Annur, amma jin na ambaceta amatsayin surikar Mama sai hankalinsu ya kwanta, nima haka kawai naji na fad’i surikar Mama dan naga yanayin fuskar Yaya kamar beji dad’in abinda nayi ba.
Jabeer yace ai kin kyauta, ina fatan kuma zaki taya Ra’eez yakin da yake gabansa, ki d’auka Raheena namiji ce kawai, kuma kirik’a kokarin kaucema had’uwar ku waje d’aya hakan zesa zuciyarki ta natsu.
Rumaisa tace wallahi bakomai, ni mai iya sadaukar da farin cikina ne matuk’ar Yaya zai cika burinsa, yau ko cewa akayi saiya aureta zan iya amincewa idan har hakan zaisa ya cika burinsa.
Jabeer yace hakan ma bazata faru ba, domin yanzu ne zamu fara aiwatar da komai, kinga ana kammala shari’ar sai musha biki. Murmushi tayi ta rufe fuska.
Jabeer yace muje na ajeku gida tunda nazo. Rumaisa tace bara nayima Mama magana. Jabeer yace shikenan.
Tare da Mama suka shiga d’akin, mamaki Rumaisa tayi ganin Ra’eez a kwance ya rufe ido kamar me bacci ga Raheena a kusa dashi sai kallonshi takeyi. Saurin amsa sallamarsu Raheena tayi tana matsawa hada duk’ar da kai.