ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

Bud’e ido Ra’eez yayi jin muryar Mama. Gyara kwanciyarshi yayi yana fad’in sannu Mama. Murmushi tayi tana fad’in kai ne da sannu, ya jikin naka? Da sauki Ra’eez ya amsa. 

Kallon Rumaisa yayi suna had’a ido ya kashe mata ido d’aya, murmushi tayi itama ta rama. Mama tace zamu koma sai gobe idan Allah ya kaimu tunda ga Jabeer nan yazo. 

Ra’eez yace kai Mama, ku bari zuwa dare bana son ku tafi. Da sauri Raheena tace haba ka barsu suje su huta ai akwai gajiya, tunda gashi nazo zan zauna da kai har wajen tara sai na tafi. 

Murmushi Mama tayi tana fad’in sannu da kokari angode. Turo baki Ra’eez yayi yana fad’in to Rumaisa ta zauna sai ya kaiki ke da Abdallah anjima zai maidata. 

Mama zatayi magana Raheena tace gaskiya baza’a wahalar mun da K’anwa ba, da ganinta ta gaji taya zaka ce ta zauna bayan ko ta zauna sai dai ta koma wancan falon tunda bazata iya zama anan ba dan a takure take. 

Murmushi Rumaisa tayi tana fad’in maganar ki gaskiya babbar Yaya, nima bazan zauna ba kada na shiga hakkin ki. Raheena tace to ka gani, Mama kawai kuje ku huta zan kula dashi. 

‘Daure fuska Ra’eez yayi ya koma ya kwanta, jiyake kamar ya kwad’a mata mari saboda haushi, shi sam beso zuwanta ba yaso ace Pretty d’insa ce akusa dashi yau su sha soyayya amma wannan anacin tazo ta zauna. 

Muryar Mama yaji tana fad’in to sai da safe kaci abinci sosai kafin kasha magani. Kai ya d’aga yana hararar Rumaisa. Dariya tayi ta wuce tana fad’in Yayana Allah ya baka lafiya kaji. 

Suna fita Raheena ta matso tana fad’in D ashe ba bacci kake ba kawai ka rufe ido ka barni shiru,. Kauda kai yayi bece komai ba. Hannunshi ta kamo tana fad’in idan ina tare da kai tamkar ahalinka ne a kusa da kai, domin zan d’auke maka abinda bazasu iya d’auke maka ba ma. 

Saurin zare hannunshi yayi yana mata wani kallo. Baki ta rik’e tana fad’in yi hak’uri wallahi mantawa nayi, zamana akusa da kai sai nake ganin kamar agidan mu muke shiyasa na iya rik’e ka amma ba halina bane. 

Zeyi magana Rafeek ya shigo. Murmushi ya saki yana fad’in Hajiya Raheena kece mai jinyar kenan? Murmushi ta saki tana gaishe shi, sosai taji dad’i, duk da bata sanshi ba amma tasan abokin Ra’eez ne, lallai Ra’eez yana sonta, gashi har abokanshi sun santa. 

Zama Rafeek yayi yana fad’in Ra’eez ya jikin? Ra’eez yace da sauki Yaya ya aikin? Rafeek yace akwai wahala, sai yanzu fa na tashi, abinci kawai na biya naci agida. 

Ra’eez yace sannu da aiki. Shigowar Jabeer yasa Ra’eez ya kalli Raheena yana fad’in ki tashi ki wuce gida magriba ta kusa. ‘Bata fuska tayi tana fad’in ka barni sai zuwa anjima bazan iya barin ka a….. Kallon da yayi mata yasa tayi saurin tashi tana turo baki. 

Murmushi Jabeer yayi yana fad’in wai a ina aka tab’a korar d’an jinya? Rafeek yace ai mace ce ga magriba ta kusa kaga babu dad’i ta zauna nan, da ace babu kowa dan ta zauna ba wani abu bane, amma bana son ina ganin mace a waje da dare domin ba mutuncinta bane. 

Murmushi Raheena ta saki jin abinda Rafeek ya fad’a, sai yanzu ta gane Ra’eez baya son tayi dare a waje, sannan ga abokansa duk maza yana kishi ta zauna a cikinsu. 

Jaka ta d’auka tana fad’in D kana da gaskiya, tunda akwai maza a d’akin be kamata na zauna acikinsu ba, wasu ma zasu iya zuwa kaga babu dad’i a kalle maka ni, shikenan zan tafi sai zuwa goben. 

Dariya Jabeer yayi yana fad’in ai kinsan abokina akwai kishi. Harara kawai Ra’eez yake aiko masa, be kulashi ba yacigaba da fad’in nan gaba kila bazai barmu shiga gidansa ba. 

Raheena tace ai jin dad’i ne ka samu mai kishinka. Jabeer yace sosai kuwa, ai Allah ya nuna ranar biki. Raheena tace amin. 

Juyawa tayi tana fad’in D kaci abinci da yawa dan Allah. Rafeek yace zaici, ki gaida gida. Fita tayi tana murmushi. 

Tsaki Ra’eez yaja yana fad’in wallahi Jabeer kashiga hankalin ka. Jabeer yace daga fad’in gaskiya. Ra’eez yace shikenan, insha Allahu kaine zaka aureta. 

Dariya Jabeer yasa hada rike ciki yana fad’in amma baka ta kirki, yanzu ka rasa da wadda zaka had’ani sai Raheena, haba ai koda bani da budurwa bazan iya aurenta ba. 

Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in me yasa kake shiga maganarta to? Jabeer yace kawai ina tausayinta ne, duk da bansan zafin so ba amma ina tausaya mata domin ta kamu da sonka, kuma ma ni bazan iya auren wacce take son wani ba, to na aureta nace na auri wa? Ka auri mace, Ra’eez ya fad’a. 

Dariya Rafeek yayi yana fad’in wallahi idan mutum yana kusa da ku sai kusashi ciwon ciki saboda dariya, yanzu kai Jabeer ai taimakon ka Ra’eez yayi daya baka ita, domin naga ko ‘yar tsana baka da ita. 

Dariya Ra’eez yasa yana fad’in wallahi kuwa Yaya, kaganshi nan kullum yana gida, lokacin bacci haka yake kwanciya babu mai sashi farin ciki, dan na bashi Raheena ai banyi laifi ba. 

Jabeer yace sai dai ka bani Rumai…. Kamar walkiya Ra’eez ya diro daga gado, dariya Jabeer yasa yayi bayan Rafeek. Nufoshi Ra’eez yayi sai ga likita ya turo k’ofa. 

Dariya Rafeek yasa yana fad’in likita kaga marar lafiyar ka ko? Murmushi likita yayi yana fad’in da alama yau zan baku sallama. Zama Ra’eez yayi yana fad’in wallahi da yafi. 

Dariya suka sa Jabeer yace aikuwa sai jibi. Rafeek yace tunda dai ya warke ai shikenan. Matsawa Likita yayi yana fad’in bara na duba na gani. 

Har likita ya gama dubashi yana hararar Jabeer. Kallon Rafeek likita yayi yana fad’in gaskiya jikin lauya da sauki, ko yanzu zaku iya tafiya gida. 

Rafeek yace nima naga alamun sauki gara asallameshi mu koma gida. Likita yace shikenan bara ayi sallah. Jabeer yace mungode. 

Sai da sukayi sallah kafin suka had’a kaya suka wuce. Kai tsaye gidan Ra’eez suka wuce dan Rafeek yace Jabeer ya kwana acan zuwa gobe sai suje wajen Mama aji abinda ta yanke akan zaman Ra’eez. 

**** ****

Washe gari tare da Jabeer suka nufi gidan su Rumaisa, Mama tayi mamakin ganin su dan sauri take ta had’a kayan abinci Rumaisa ta kai masu. 

Bayan sun gaisa suka fad’a mata sallamar da akayi masu. Murmushi tayi tana fad’in to Allah ya k’ara sauki, kaga yanzu sai kuje a kwaso kayanshi ga d’aki can ya zauna aciki. 

Jabeer yace Mama ina ganin abar Ra’eez a gidanshi zaifi, domin a ayanzu akwai shirin da zamu fara kuma yana buk’atar natsuwa, tun bayan da ya bani labarinshi na fara tunanin yanda zan taimakeshi, rashin lafiyarsa da sanin abinda yake damunshi yasa na yanke shawarar komawa kusa dashi kafin Allah ya bama Ummu lafiya, hakan yasa na samu Iyaye na nayi masu bayanin zan koma gidanshi mu zauna, kuma sun amince mun. 

Jinjina kai Mama tayi tana fad’in gaskiya mungode, dama haka Allah yake, idan ka rasa wani jigo sai ya baka madadinsa, hakika kai aboki ne nagari, Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa. 

Jabeer yace amin. Rungume Jabeer Ra’eez yayi yana hawaye. Murmushi Jabeer yayi yana fad’in meye na kuka kuma, yanzu ka zama d’an uwana. 

Bayan sun karya Jabeer ya bar Ra’eez anan yawuce gidansu saboda zaije wajen aiki. Shimfid’a Mama tayi masa a falo ya kwanta dan bacci yake ji saboda maganin da yasha. 

Sai da Rumaisa ta kammala aikinta kafin taje ta zauna a kusa dashi, duk da bacci yake amma haka ta zauna tana gadinshi. 

Wayarsa ce tayi k’ara, tana dubawa taga ansa Raheena. Tsaki tayi ta maida wayar silent. Ganin an cigaba da kira yasa ta d’auka. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button