ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

Cikin sauri tace bacci yakeyi. Raheena tace Rumaisa ce? Kai ta d’aga tana fad’in itace. Raheena tace dama naje asibiti akace an sallameshi shine nake son naji inda yake nazo. 

Rumaisa tace ai bacci yakeyi ki bari zuwa anjima da rana sai amaki kwatance kizo. Ba haka Raheena taso ba amma haka ta daure tayi mata godiya tare da kashe wayar. 

Murgud’a baki tayi tana fad’in jarababbiya kawai, hakanan kin takuwara ma mijina, wallahi badan shiri bane da na nuna maki iya karki dan bazan lamunci had’a Annur da kowa ba. 

Haka tayi ta masifa tamkar agaban Raheena take. Ra’eez da tun farkon wayar ya tashi ido ya tsura mata sai murmushi yakeyi ganin yanda ta dage tana masifa ita kad’ai. 

Kamar ance ta juyo, waro ido tayi ganin Ra’eez ya tashi yana kallonta, da sauri ta yunkura zata gudu yayi saurin jawota ta fad’o jikinshi. Tusa kanta tayi tana mashi shagwaba. 

Dariya yayi ya tashi tare da cire hannunshi ajikinta yana fad’in babu inda zaki sai kin mai-maita abinda kika fad’a. 

Rufe fuska tayi ta zame gefe tana fad’in nifa bance komai ba. Ra’eez yace shikenan, amma ki sani ina binki bashi. Saurin d’aga kai tayi tana fad’in naji. 

Wayarsa ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Raheena, kallon Rumaisa yayi yana kallon wayar. Tsam ta tashi tayi waje da sauri. Murmushi yayi kafin ya d’aga. 

D ina kwana ya jikin? Lafiya lau, ya amsa cike da yanga kamar mace. Wayyo D d’azu na kira Rumaisa ta d’auka wai kana bacci, dama ina so nazo na dubaka tunda ance an sallameka. 

Yatsina fuska yayi yana fad’in ki barshi bana son kina zuwa kunyar Mama nakeji. Murmushi tayi tana fad’in nikam bazanji dad’i ba idan banzo ba, kasan fa har yanzu gajiyar Dubai bata sakeni ba amma tunda naji baka lafiya naji bazan iya zama ba, muma ranar lahadi muka dawo cikin dare, naso na kira alokacin amma naga dare yayi, da safe kawai Dady ya fad’a mana kana asibiti nan take naji gajiyar ta tafi. 

Murmushi yayi yana fad’in kun dawo lafiya ko? Raheena tace lafiya lau, kayan suna hanya sai zuwa jibi zasu iso, D bakaga zab’en da nayi mana ba, tsarabar ka tana nan idan kazo zan baka. 

Girgiza kai yayi yana fad’in ki adana mun ita sai nan gaba zan amsa. Kai ta jinjina kamar yana ganinta tace angama Angona, fatana Allah ya baka lafiya. 

Ra’eez yace ina so na kwanta. Murmushi tayi tana fad’in ka huta lafiya idan ka tashi ka kirani kada na kira kuma baka tashi ba na katse maka bacci. 

Ra’eez yace angama. Kashe wayar yayi yana sakin murmushi. Hannu yasa yana shafa wuyansa, ta wani gefen yana tausayin Raheena, bayaso Allah ya kamashi da laifin yaudara, Raheena batayi masa komai ba, asalima lokacin da abun ya faru batasan komai ba, mahaifinta ne me laifin shi yakamata ya amshi hukunci ba ita ba, amma dole ya dakatar da komai koda hakan zai ruguza amintakar da Alhaji Barau yayi masa, domin ko yanzu suka b’ata bazai damu ba, domin lokacin fafatawa yayi. 

Ajiyar zuciya ya saki yana tunanin hanyar da zaibi dan kada ya cutar da zuciyar Raheena, yasan koya rabu da ita yayi mata gata, domin ta silar shi ta canza rayuwar ta wacce duk wanda ya aureta zaiji dad’in hakan. Lumshe ido yayi yana tunani. 

*** 

Har la’asar suna tare da Jabeer, tashi sukayi domin suje gidan su Jabeer daga can su wuce gida. A tare suka fito. Mama tace ina kuma zakuje? Jabeer yace ai gara mu fita hakan zeyi masa dad’i, zamuje gidan mu daga can mu wuce. 

Mama tace to abincin daren fa? Ra’eez yace Mama kinsan bana cin abu mai nauyi da dare. Mama tace to Jabeer fa? Jabeer yace nima hakan take mama. 

Murmushi tayi tana fad’in haka kawai kun maida kan ku turawa, ai shikenan sai Allah ya kaimu, amma kasha maganin ka. Ra’eez yace to Mama. 

*** ***

Kamar ya saba da ‘yan gidan su Jabeer haka sukayi ta fira, har isha’i suna tare, anan suke jin Kawun Jabeer zaizo gobe. Jabeer yace yauwa idan yazo zanyi masa maganar ka, kaga sai muzo musameshi muji yanda zaice. Ra’eez yace Allah ya kaimu. 

Wayarsa ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Yaya Rafeek, bayan sun gaisa yace yana jiransu a gidanshi tare suke da Adnan k’anin Sameer zasuyi magana akan mutuwar Naseer. 

Ra’eez yace gamu nan zuwa. Tashi sukayi suna masu sallama suka nufi gida cike da farin ciki, koba komai zasu fara samun hujjar shiga kotu. 

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button