ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

Jabeer ne yaja Ra’eez suka bar wajen. Kusa da Sameer suka je wanda yake rungume jikin Mahaifiyarsa dan Dadynsa ana gamawa ya sulale ya bar wajen. 

Dafa Sameer Ra’eez yayi yana fad’in kayi abun kirki, kuma har abada baza kayi danasanin abinda kayi ba, kaci sa’a ba kotun musulunci bace da sai kasha bulala, amma yanzu kana da damar biyan dubu d’ari biyar idan baka son zaman gidan yari. 

Da sauri Mamansa tace kud’in zamu biya, mungode sosai lauya, idan bazaka damu ba ina son ganin ka idan kana da lokaci. Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in ayanzu Alhaji ya d’auki zafi, amma zanzo idan na samu lokaci. 

Haka suka fito ita da Sameer suka wuce gida ‘yan jarida sai d’aukarsu hoto sukeyi. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in wannan itace shari’ar ban dariya. 

Jabeer yace wallahi yanda kasan a film, ban tab’a ganin irin wannan shari’ar ba, daga kai har Brr. Bajinta kun bani dariya. Ra’eez yace ai shiyasa na barshi ya fara, da yake be iya wasan ba ai kaga kowa ya ganoshi. 

Jabeer yace amma nayi mamakin yanda Sameer yayi saurin amsa laifinsa. Ra’eez yace kila hakan yafi masa sauki. Kallonsa Jabeer yayi yana fad’in ban yarda da kai ba, anya babu sa hannunka? Dariya Ra’eez yasa yana fad’in muje ofis. 

Iyayen Halima basu tsaya jiran Ra’eez ba dan ya fad’a masu ana gamawa su wuce gida baya son agansu atare. Duk da sunji haushin Brr. Bajinta amma abinda yayi daga k’arshe yasa sukaji dad’i, hakan yasa sukaje sukayi masa godiya. 

Murmushi yayi yace haba babu komai, ai dama nace maku mune zamuyi nasara. Malan Haruna yace nawa ne kud’in ka? Brr. Bajinta yace haba kyauta nayi maku. Sosai sukayi masa godiya suka wuce cike da farin ciki. 

Zagaye kawai Alhaji Barau yake a ofis d’insa, ya rasa taya zai kalli abinda Ra’eez yayi masa, ya akayi ya canza komai beyi amfani da abinda suka bashi ba? Dole ya turkeshi sai ya fad’a masa abinda yake nufi. Waya ya d’auko yana niyar kiransa. 

K’ofa aka bud’e hakan yasa ya aje wayar. Alhaji Marusa ne yashigo fuskarsa d’auke da murmushi. Bayan ya zauna Alhaji Barau ya mik’a masa hannu suka gaisa dan shima haushinsa yakeji akan abinda yayi masu. 

Daurewa yayi dan baya so ya gano ya san komai. Alhaji Marusa yace Babban Alkali da girman kujerar ka. Alhaji Barau yace zaka fara ko. 

Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad’in alokacin da nace kada ka bama Ra’eez shari’ar me kace? Na fad’a maku nifa jikina be yarda dashi ba, yaron da yazo a ranar farko ya cinye babbar shari’ar da aka sha wahala akanta taya kake tunanin zai amshi tayin rashin gaskiya? Tun farko na fad’a maku amma bakuji ba, sai kace wai zasu iya d’aukarshi, to ko sun d’aukeshi ba sai yana da hujjar nunawa ba, haba Alhaji Barau ya kake so kabar tsohuwar basirar ka ta gushe ne.

Ajiyar zuciya Alhaji Barau ya saki yana fad’in kai dai ka bari kawai Alhaji Marusa, kwanan nan na rasa abinda yake damuna, ganin yana neman yarinyar wajena yasa nayi tunanin zaiyi duk abinda na sashi sai gashi ya watsa mani k’asa a ido, wallahi yanzu daka shigo kiranshi nayi niyar yi naji dalilin da yasa zaiyi mani haka. 

Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad’in shiyasa nace basirar ka ta tsufa, taya kana Alkali zaka kira lauyenka ka titse shi akan shari’ar da yayi bayan kasan gaskiya ce, ai Brr. Bajinta ne kawai ze maka haka ka titse shi a zauna lafiya. 

Abinda nake so da kai ka nuna baka damu ba, kuma kayi masa jinjinar ban girma ka gode masa akan abinda yayi, kuma ka fad’a masa baka san haka abun yake ba amma kace ka gode da yaje ya sake bincike, ina tabbatar maka idan ka fad’a masa haka zai yarda da kai, gashi ka yanke hukunci yanda ya kamata, domin ko wannan kud’i da za’a bata zai inganta mata rayuwar ta, kaga zaka fita daga zarginsa. 

Jinjina kai Alhaji Barau yayi yana fad’in nagode da zuwanka Alhaji Marusa da na kwafsa, damuwa ce tamun yawa hakan yasa na kusa rasa dabarata, amma zanyi yanda kace. 

Tashi Alhaji Marusa yayi yana fad’in zanje na rarrashi Alhaji, ya godema Allah da ba kisa yaron yayi ba, gashima har ka bada zab’i biyu, kuma nasan bazasu barshi ya shiga gidan yari ba. 

Alhaji Barau yace ka gaishe shi kuma ka bashi hak’uri nagode. Alhaji Marusa yace zaiji. 

***

Ina jinka Ra’eez, Jabeer ya fad’a yana sunno kanshi a fuskar Ra’eez. Dariya yayi ya tureshi yana fad’in kaga Malan kada ka dameni, taya zaka zo a wajen aiki ka ishe ni na baka labari idan wani yaji fa, kawai ka bari idan muka fita na fad’a maka. 

Jabeer yace ai gashi can ana kiran sallah muje muyi idan muka fito sai ka bani. Ra’eez yace muna fitowa na tashi dan wallahi na gaji, kasan dama idan nayi shari’a bana son nayi zaman aiki. Jabeer yace aiko sai dai mutafi tare dan bazanji dad’in zama wajen nan baka nan ba. 

Ra’eez yace idan kuma na bar kotun fa? Da sauri Jabeer ya kalleshi yana fad’in ban gane ba? Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in ina nufin idan aka mana canjin wajen aiki. Jabeer yace insha Allahu hakan bazata faru ba. Ra’eez yace Allah yasa. 

***

Bayan sun gama sallah yashiga domin ya fad’ama Alhaji Barau zai wuce gida. 

Cike da jin nauyi Alhaji Barau ya kalleshi yana fad’in Ra’eez na rasa bakin da zan maka godiya, hakika zuwanka wannan kotun alkhairi ne a wajena, so biyu kana ceto ni daga yanke hukuncin danasani, bazan iya biyanka da komai ba wallahi, nagode sosai, sam banyi tunanin haka abun yake ba, shiyasa wanda nasa yaje yayi mani binciken yana kawowa ban tsaya dubawa ba na baka saboda nasan na yarda da kai, ashe abubuwan da suke ciki ba gaskiya bane, nagode sosai da ka sake bincike, duk da kayi kok’ari baka fito fili ka nuna kasan gaskiya ba, amma kayi aikin da yakamata ace Brr. Bajinta ne yayi, tabbas nasan wannan shari’ar ta yau ta juya ma mutane kai, domin ku duka lauyoyin an rasa gane a wane b’angare kuke, gaskiya nagode sosai, shima Brr. Bajinta ya taimaka daya gyara kuskuren da ya kusayi. 

Murmushi Ra’eez yayi yace ai bakomai duk taimakon kaine, nima nasan bazaka bani abinda za’ayi rashin gaskiya aciki ba, hakan yasa dana duba shedar nasan baka duba ba, shiyasa banyi maka magana ba naje na sake sabon bincike. 

Alhaji Barau yace naji dad’i sosai tunda kasa bamuji kunya ba. Ra’eez yace ina son zanje gida kaina yamun nauyi ne. Murmushi Alhaji Barau yayi yace haba bakomai kaje kawai nima yau da wuri zan tashi nagaji. 

Tashi yayi yana masa sallama, da sauri Alhaji Barau yace zaka lek’a wajen mutuniyar ko? Murmushi ne ya kwace ma Ra’eez babu shiri, duk’ar da kai yayi alamun kunya yayi waje da sauri. 

Dariya Alhaji Barau yasa yana fad’in Allah nagode maka daka zab’a mani suriki nagari, gaskiya Raheena tayi dace, Allah nagode maka da banyi saurin sata ta fiddo da miji ba ashe yana zuwa. 

Da k’yar Jabeer ya bar Ra’eez dan yace sai ya tsaya ya bashi labarin yanda akayi, shi kuma Ra’eez yace ya gaji sai dai suyi waya anjima. Babu yanda ya iya dole ya kyaleshi ya tafi. 

Bayan sunyi sallama da Jabeer yana kok’arin shiga mota yaji anyi masa sallama. Juyowa yayi tare da amsawa. Murmushi ya saki ganin kamar yasan fuskar wanda yake tsaye. 

Hannu ya mik’a masa yana fad’in barka da kok’ari Brr. Ra’eez ina tayaka murna akan wannan nasara da kayi a wannan shari’a. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button