ALKALI NE Page 51 to 60

Hannu Ra’eez ya bashi yana fad’in nagode, amma kamar nasan fuskar nan? Murmushi yayi yana fad’in *Rafeek Labaran Zaki*, Ma’aikacin gidan redion *Liberty*.
Jinjina kai Ra’eez yayi yana murmushi yace yanzu kam na tuna, nagode Rafeek amma ai ba nine nayi nasara ba.
Murmushi Rafeek yayi yana fad’in wanda ka kare dai ya faad’i amma ai kaine hasken shari’ar, gaskiya kayi matuk’ar burge ni, na saurari shari’ar ka ta farko a wannan kotun, duk da alokacin ana gamawa na tafi saboda saurin da nakeyi, naso mu had’u amma wani aiki yasha kaina ga tafiye-tafiye, sai a wannan karon naji labarin wannan shari’ar shine nazo domin naji yanda zata kasance, sai gashi nazo nasha mamaki, gaskiya kai d’in na daban ne.
Ra’eez yace nagode. Rafeek yace gaskiya ina so mu kulla abota idan bazaka damu ba, yanzu naga kana sauri amma zan amshi lambarka duk lokacin da kake da lokaci zan iya kawo maka ziyara.
Kallonshi Ra’eez yayi, yasan dai ya girme mashi sosai, sai yaji kunya da yace zasu kulla abota. Kamar Rafeek yasan abinda yake tunani yayi saurin fad’in nayi maka tsufa ko? Dariya Ra’eez yasa yana girgiza kai.
Rafeek yace ita abota ai ba’a duba girma, idan na yarda da hankalin mutum ina abota dashi koda na haifeshi bare kuma nasan ban haife ka ba, dan haka kada ka damu kawai naji ka kwanta mani ne.
Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in nagode Yayana, kada ka hanani kiranka da haka domin nima naji inaso na kiraka da hakan domin ina buk’atar hakan.
Murmushi Rafeek yayi yana fad’in nima ina buk’atar samun K’ani domin na rasa nawa shekaru da yawa, amma tunda na samu wani nafi kowa farin ciki.
Wayarsa ya mik’a mashi, amsa yayi yasa masa lambarsa ya kirashi yana fad’in ga tawa nan, sai munyi waya nagode. Ra’eez yace nima nagode.
Mota yashiga yana kok’arin kunnawa wayarsa tayi k’ara, yana dubawa yaga lamba ce, yana d’auka yaji muryar Sameer da alamun kuka.
Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in lafiya Sameer? Cikin sanyin murya Sameer yace ina so mu had’u ne ko zaka mun kwatancen gidan ka? Ra’eez yace kada ka damu bara nazo Mamanka ma tace tana son gani na.
Sameer yace nagode sai kazo. Kashe wayar yayi yana murmushi, yaso yaje gida ya huta anjima yaje wajen Ummunsa amma dole yaje yaji dalilin kiran…..
Ur’s.
Nabeelert Lady????[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣0⃣
Cikin kuka Sameer ya rungume Ra’eez yana fad’in nagode sosai Ra’eez da abinda kamun, wallahi yanzu ina jin sanyi araina, gashi dai na girma amma na kasa gane hakan, abinda nake so yanzu naje na nemi yafiyar Halimatu, da zata amince dani wallahi zan aureta ma.
Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in bakomai kadena kuka, tunda dai har kayi nadama Allah zai yafe maka, sai dai kaje ka nemi yafiyar Halima, idan da hali zaka iya tuna sauran matan da ka lalata ma rayuwa suma kaje ka basu hak’uri sannan kayi masu alkhairi hakan zaisa ka sake samun nutsuwar zuciya sosai.
Zama Sameer yayi yana fad’in zanje, wallahi zanje Ra’eez, duk da nasan ba lallai bane na iya samun wasu amma duk matan da nayi harka dasu nasan su, nagode Allah da basu da yawa kuma zanje na nemi yafiyarsu, amma ni ina son kashige mun gaba muje gidan su Halima.
Ra’eez yace kada kadamu zan zo muje, amma shawarar da zan baka ka ajiye kudirin ka na son aurenta a gefe, ina mai tabbatar maka Halima bazata amince da kai ba, duk da hakan taimako ne agareta amma baza ta amince ba, gara ka bata hak’uri idan akwai taimakon da zaka sake mata kayi mata kaje ka cigaba da istigfari ka samu wata mata can daban ka aura hakan zai fi maka kwanciyar hankali.
Jinjina kai Sameer yayi yana fad’in shikenan, dama tausayinta ne yasa nace zan aureta badan soyayya ba, saboda dama sha’awarta kawai nakeyi amma zanyi yanda kace.
Ra’eez yace kaga tunda baka sonta gara ka hakura, domin shi aure soyayya ce jigonshi, Allah ya k’ara tsare gaba.
Sameer yace amin, amma dan Allah a ina ka samu hoto na? Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in tunda komai yawuce ai shikenan ba sai kaji ba.
Sameer yace shikenan, ai nasan sirrin ku ne na lauyoyi na barshi. Maman Sameer ce tashigo bakinta d’auke da sallama.
Bayan sun gaisa ta kalli Ra’eez tana fad’in nagode sosai, dama godiya nake so nayi maka domin ka taimake mu, sam banyi danasanin fad’uwar mu ba, domin gata kayima Sameer, gara mutum yaji kunyar duniya akan ta lahira, gashi ta silarka Sameer ya natsu, shima Alhaji da yayi fushi na sameshi nayi masa bayani kuma ya fahimce ni yace ayi maka godiya yana jin kunyar ka ba zai iya fitowa ba.
Ra’eez yace haba babu komai Allah ya tsare gaba. Sukace amin. Kallon Sameer tayi tana fad’in Alhaji ya tura maka duka kud’in da za’a kai kotu, sai ka shirya gobe kaje Ra’eez yayi maka jagora ka kai kud’in a aika ma su Halimar.
Sameer yace nagode Mamy, kuma Ra’eez yace zai rakani wajen Halimatu na bata hak’uri. Mamy tace angode sosai Ra’eez.
Tashi Ra’eez yayi yana fad’in nizan tafi, Sameer sai munyi waya kila ko zuwa goben ne sai muje can. Tashi Sameer yayi yana fad’in nagode sosai.
Mamy tace ka gaida gida dan Allah karik’a zagayowa muna gaisawa. Ra’eez yace insha Allahu. Sallama yayi mata suka fita shida Sameer.
Sai da ya shiga mota kafin Sameer ya rufe masa k’ofar yana masa godiya. Sai da ya b’acema ganinsa kafin ya koma gida cike da farin ciki.
*** ***
Sai yamma sosai ya isa asibiti, bayan sun gama shiriritar su da Ummunsa ya wuce ofis d’in likita dan Dr. Saddek ma yazo yana jiranshi.
Bayan sun gama gaisawa Dr. Saddek yace gaskiya Ra’eez jikin Ummunka yayi sauki sosai, domin a hoton da mukayi mata akwai cigaba sosai, matuk’ar zata cigaba da tunawa da abubuwan da suka faru abaya to zata dawo hankalinta, shiyasa yanzu an canza mata magani kuma akwai cigaba.
Ra’eez yace nagode sosai likita Allah ya saka da alkhairi, bansan da abinda zan saka maku ba. Dr. Sadeek yace haba ai babu komai, Allah dai ya bata lafiya. Ra’eez yace amin. Sallama yayi masu yawuce gidan su Rumaisa.
Tun a hanya Jabeer ya kirashi akan zaije gidansa sai Ra’eez yace ya sameshi gidan su Rumaisa. Dariya Jabeer yasa ya fara zolayarsa, be kulashi ba ya kashe wayar yana dariya.
Yana zaune bayan sun gama gaisawa da Mama tana masa murnar nasarar da yayi Jabeer ya kirashi. Tashi yayi yaje ya shigo dashi.
Bayan sun gaisa da Mama tasa Rumaisa ta kawo masu abinci. Ra’eez yace Mama ki barshi an kusa kiran sallah idan mukayi sai muci. Mama tace ai shikenan.
Jabeer yace Rumaisa bazaki fito mu gaisa ba? Murmushi Mama tayi tace ai tana jinka. Ra’eez yace ya akayi yau bata je islamiya ba ma? Mama tace kanta ne yake ciwo harta shirya zataje naga yanda jijiyoyin kanta suka tashi shiyasa nace tasha magani ta kwanta sai Abdallah ne kawai yaje nasan shima yanzu yana hanya.
Cike da damuwa Ra’eez ya kalli d’akin Rumaisa, badan yana kunyar Mama ba sai yaje ya ganta. Jabeer yace Allah ya bata lafiya ciwon kai beda dad’i. Mama tace amin.