ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

Mama tace ya shari’ar taku ta kasance kuma? Zunguro Ra’eez Jabeer yayi yana fad’in ana magana fa. Harara ya buga mashi yana kallon Mama. 

Murmushi tayi tana fad’in kaje ka duba jikin Rumaisar kafi jin dad’in bamu labarin. Rufe fuska Ra’eez yayi yana fad’in kai Mama! Dariya tasa Jabeer yace Mama ashe dai kin harboshi? Murmushi Mama tayi tana fad’in bara nashiga ciki na kira maka ita. 

Da sauri Ra’eez yace dan Allah Mama ki zauna dama labarin nazo baki. Dariya Jabeer yasa yana fad’in haka ne Mama kizauna nima labarin zai bani sai ja mani aji yake. 

Zama tayi tana fad’in ina jinka…… Labarin yanda shari’ar ta kasance ya bata har da zuwanshi gidansu Sameer. 

Jabeer yace saura bayani akan hoton Sameer da yanda ya amsa laifinsa. Ra’eez yace wallahi idan maye ne kai ka kama mutum sai ka cinyeshi duka. 

Jabeer yace naji kawai ka fad’a mana. Dariya Ra’eez yayi yana fad’in d’azu ma sai da Sameer ya tambayeni amma naki fad’a masa. 

A cikin week end da na fad’a maka zan had’a komai, duk iya bincike na na rasa yanda zan samo shedar da zata nuna Sameer ne ya aikata laifin, Baba na kira nake tambayarsa basu da wani abu da zai nuna Sameer ne ya aikata laifin. 

Sai yake fad’a mani alokacin daya d’aukota zasuje asibiti yana kok’arin gyara mata hijabinta yaji wani abu a akanta, yana dubawa yaga zobe shine ya cireshi ya aje, gashi nan ma zaije ya kaima Brr. Bajinta dan yana tunanin na Sameer ne. 

Cikin sauri nace masa ya dakata zanje na amsa dan nasan ko ya bama Brr. Bajinta bazaiyi amfani dashi ba, bayan na amso nazo ina tunanin yanda zanyi dashi. 

Komawa nayi unguwar su Sameer cikin sa’a na samo lambar wayarsa. Bayan na ajeta sai na shiga Whatsapp ina dubawa ko zan ganshi, cikin sa’a sai gashi, ina dubawa naga babu hoto a Dp d’inshi, har zan fita sai kuma na hau status ina cikin dubawa kawai naga ya d’ora wasu hotunanshi, yan dubawa sai naga hannunsa sanye da irin zoben da aka bani, saurin d’aukar hoton nayi. 

Ban b’ata lokaci ba naje aka wanke mani hoton, sosai naji dad’in wannan hujja, ana gobe za’a shiga kotu nayi wani tunani, sai kawai na daure na kira Sameer, har ya kwanta bacci amma ina fad’a masa nine yayi saurin tashi. 

Nan nake tambayarsa ya tabbata be bar wata sheda da zata tonashi ba? Sai yace mani yana da wata azurfa kuma tun bayan da abun ya faru be ganta ba, yasan kuma baya rabuwa da ita. 

Anan na fad’a masa zanyi kok’arin nemota abinda nake so dashi ya fad’a mani gaskiya. Sai yace mun be aikata komai ba. Sai nace masa amma yace mun bayan abun ya faru bega zobensa ba. 

Ganin na ganoshi babu b’ata lokaci ya tabbatar mani shine ya aikata laifin amma na rufa masa asiri, nan nayi masa nasiha na kuma ce masa ga zoben a hannuna, idan har ya iya fad’in gaskiya a kotu zan taimaka masa, kuma na tabbatar masa baza’a d’aureshi ba dole zab’i biyu za’a bashi nasan kuma Iyayensa bazasu bari a d’aureshi ba. 

Anan ya amince zeyi abinda nace, amma nace masa kada ya fad’i gaskiya har sai na nuna zoben sannan. Kaji yanda mukayi dashi. 

Jinjina Jabeer yayi masa yana fad’in gaskiya kai d’an baiwa ne Ra’eez, Allah kad’ai yasan irin baiwar da yayi maka amma ka gode masa. 

Mama tace gaskiya kayi kok’ari, kaga ka fita daga zargin kowa, Allah dai ya k’ara tsare ka kuma ya baka sa’a akan shari’ar da za…. Saurin tashi Ra’eez yayi dan yasan abinda Mama zata fad’a shi kuma baya son Jabeer yasan komai yanzu. 

Kallonshi tayi suna had’a ido yayi mata alama, nan take ta gane abinda yake nufi. Murmushi tayi tana fad’in duk son ganin Rumaisar ne baza’a tsaya na k’arasa addu’ar ba. 

Jabeer yace idan ba ya ganta ba hankalinsa ba zai kwanta ba, ni Allah ma yasa ka bamu labarin dai-dai. Duka Ra’eez ya kai mashi da sauri ya mik’e yana dariya. 

Tashi Mama tayi tana fad’in ai bakayi kokowa kana yaro ba gara kayi k’ari. Turo baki Ra’eez yayi yana hararar Jabeer da yake masa dariya. 

Bayan Mama ta tashi ta turo Rumaisa. Fitowa tayi sanye da hijabi dan kanta yayi sauki. Zama tayi tana gaishe su kanta ak’asa. Saurin matsawa Ra’eez yayi yana fad’in Pretty na ya kan naki? Murmushi tayi tana fad’in ya warke ai. 

Ra’eez yace bana son wasa da lafiyar ki kizo muje asibiti. Jabeer yace kaji mani mutumi, tace ta warke zaka jajibo mata wani asibiti. 

Ra’eez yace malan ba ruwanka, kai da ko tsuntsu baka kiwo taya zakasan yanda ake kula da mutum ma, dan Allah idan ana maganar Iyali kadena tsoma baki. 

Baki Jabeer ya rik’e yana kallon Ra’eez. Gwalo yayi masa ya zauna gaban Rumaisa ya juya ma Jabeer baya yana dariya k’asa-k’asa. 

Tashi Jabeer yayi yana zungurinshi da k’afa yana fad’in ni zan wuce bazan iya tsayawa kallon kayan haushi ba. Dariya Ra’eez yasa yana fad’in kaje kayi fira da Baba Madu yanzu zan fito muje masallaci. 

Wucewa Jabeer yayi yana murmushi, sai da ya kai k’ofa sannan yace daga masallaci wajen Raheenar ka zamuce ko dan nasan shine dalilin da yasa kace nazo nasan baka iya zuwa kai kad’ai. 

A zabure Ra’eez yayi kanshi jin Bom d’in da yake had’a masa. Da gudu Jabeer yayi waje yana dariya. Kwafa Ra’eez yayi ya dawo wajen Rumaisa kada ta yarda da abinda yace.

**** ****

Kai amma Alhaji ka tsallake rijiya da baya, gaskiya Ra’eez d’an albarka ne, shiyasa nace maka gara azo ayi maganar auren su da Raheena tun kafin wata ta kwace matashi. 

Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad’in abinda nake tunani kenan, jira nake yazo nasa Raheena tayi masa magana na fad’a masa ya turo iyayenshi ayi magana dan bana son aja bikin tunda mu duka kowa yana da halinsa. 

Momy tace yauwa Alhaji dan Allah kada yawuce wata d’aya, kaga sai ka bani kud’i muje Dubai nida Raheena mu zab’o kayan da take so, idan so samune a cikin sati mai zuwa muje. 

Alhaji yace haka ne, bakomai ku fara shiri zansa a nema maku Visa zuwa asabar sai ku tafi, dama bani da matsala akan kud’i dan akwai su a account kawai tura maki zanyi. 

Murmushi Momy tayi tana fad’in dole ayi bikin da zai girgiza mutane, naji dad’i da muka tara yanda kowa zaizo ya dangwali arziki. 

Alhaji yace ai da wuri zan bugo kati saboda kowa ya samu dan wannan babban biki ne. Momy tace Allah ya k’ara girma. Yace amin. 

**** ****

Washe gari tunda wuri Ra’eez yaje wajen aiki, yana zuwa kai tsaye d’akin ajiyar tsofaffin kundi ya nufa yana addu’ar Allah yasa mai kula da wajen yazo. 

Cikin sa’a ya sameshi, da sauri ya k’arasa ya fara gaishe shi kasancewar babban mutum ne. Murmushi mutumin yayi yana fad’in Malan Ra’eez ya gajiyar shari’ar jiya kuma? Ra’eez yace lafiya lau gajiya tawuce *Kawu Datti*. 

Murmushi yayi cikin jin dad’in abinda Ra’eez ya kirashi dashi. Kallonshi Ra’eez yayi yana fad’in dama Kawu Datti akwai wata alfarma da nake son na nema awajenka idan babu damuwa. 

Kawu Datti yace haba bakomai fad’i koma menene kaji Ra’eez. Cike da fatan nasara Ra’eez yace dama akwai wani kundi da nake son dubawa ne domin jiya Iyalan mutumin suka sameni ganin mun kammala wannan shari’ar suka kawo mani wata magana data girgiza ni, duk da nasan abun akwai wuya amma sun roke ni na tausaya masu kuma na masu alk’awarin zanzo na duba kundin ko bazan iya yin komai akai ba, shine nake son ka taimaka na duba kuma inason abun ya zama sirri dan Allah. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button