ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

Murmushi Kawu Datti yayi yana fad’in kada kaji komai Ra’eez, kasa aranka tamkar da kurma kayi magana, domin bazan iya fidda sirrin makiyina ba bare kuma kai, wallahi Ra’eez tun shari’ar da kayi akan ‘Yar uwata nake jinka araina, nasan baka san Amina ‘yar uwata bace, idan baka manta ba shari’ar ka ta farko wata Amina daka tsaya mawa, to ita d’in tamkar ‘Ya take awajena, kuma mijinta shine silar zamana anan gashi har yanzu ina cin gajiyar aikin, dan haka ka d’auke ni tamkar d’an uwanka bazan tab’a cin amanar ka ba. 

Jinjina kai Ra’eez yayi cike da farin ciki yace nagode Kawu Datti, shari’ar anyita ne shekarar 2008, kila kana nan lokacin da akayi ta ma. 

Jinjina kai Kawu Datti yayi yana fad’in tabbas ina nan, domin na fara aiki anan a shekarar 2005, duk wata shari’a da akayi a bayan wannan shekara babu wadda ban sani ba sai dai na manta, matuk’ar na zauna na saurareta kuwa to nasanta, kuma duk wasu kundi suna cikin d’akin nan nida abokin aikina muke kula dasu dan yau ma na amshe shi aiki. 

Ra’eez yace amma naji dad’i nasan kila kasan shari’ar, dama ina so na samu wanda yasan shari’ar saboda ban tsaya na fahimci abinda suke nufi ba, sunce nayi kok’ari na duba kundin zan fahimci komai. 

Kawu Datti yace akan me akayi shari’ar? Ra’eez yace akan tsohon shugaban Kwastam Alhaji Hamza Maiwada wadda aka mik’a direbansa Malan Sani gidan yari akan laifin shine ya kashe shi kuma yayi yunkurin yima matar Alhajin fyad’e silar haka ta samu tab’in hankali. 

Girgiza kai Kawu Datti yayi yana fad’in kace azzalumar shari’a, ai bazan tab’a mantawa da wannan shari’ar ba, domin tunda na fara aiki ban tab’a cin karo da shari’ar da na zubar ma kwalla kamar k’aramin yaro ba irin wannan, kai Ra’eez wata shari’ar sai a lahira, amma Allah bazai bar azzalumai ba, domin wallahi tun a lokacin kawai naji ban yarda da shari’ar ba, dan dai an gabatar da shedu masu kyau, amma tabbas nasan akwai munakisa a shari’ar. 

Kwalla ne ya ciko ma Ra’eez yayi saurin kauda kai yana kok’arin maidasu. Kawu Datti yace kayi hak’uri yanzu mutane sun fara zuwa, bana son kowa yasan abinda zakayi, domin naji ajikina zaka taimake su, ka bani lambarka zanyi kok’arin nemo maka kundin na kawo maka shi a b’oye ba tare da kowa ya sani ba, idan yaso sai ka kwafeshi ka maido amayar gudun matsala. 

Murmushin jin dad’i Ra’eez yayi yana masa godiya. Lambarsa ya bashi shima ya bashi kafin yayi masa sallama ya tafi, sosai yaji dad’i da Allah yasa Kawu Datti ya iske dan yafi Malan Salisu fuskar kamala. 

Wajen k’arfe da’ya Sameer yazo ofis d’in su Ra’eez, waya yayi masa ya fita suka had’u, shine yayi masa jagora ya gama cike komai na shedar biyan kud’in tarar da kotu tayi masa, bayan sun gama yace ma Ra’eez maganar zuwa gidan su Halima. 

Kallon agogo Ra’eez yayi yana fad’in yanzu lokacin cin abinci ne, ina ganin muyi amfani da wannan damar muje mu dawo. Murmushi Sameer yayi yace nagode Ra’eez, Allah yasa Halima ta yafe mani. Ra’eez yace amin. Jabeer yayima magana yazo suka wuce. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

3⃣1⃣

Jinjina kai Baba Haruna yayi yana goge idonshi yayin da Sameer yake tsugunne akusa dashi shima kukan yake da alamu neman gafara yakeyi. 

Kallonshi Baba Haruna yayi yana fad’in shikenan Sameer, k’addara ta riga fata, haka Allah ya tsaro ma Halimatu dole sai ta faru kuma, tabbas nasan da ace alokacin da abun ya faru nazo gidan ku na sanar maku bazaku saurare ni ba, da ace kamar yanda kazo ka rok’i yafiya irin hakan ne zai kasance alokacin da zanje gidan ku da farko wallahi bazan tab’a fitar da maganar duniya ta sani ba, amma sanin halin masu kud’i yasa dole sai da kowa yaji wannan maganar, a hakan ma badan wannan bawan Allah Ra’eez ya tsaya mana ba da shikenan ahaka zamu shigar da k’ara amma a tozar tamu kuma a sake b’atama Halima suna, amma duk da haka mungode ma Allah, bakomai, Allah ma muna masa laifi murokesa yafiya kuma ya gafarta mana, ni kama na yafe maka, bara na kira Mahaifiyarta da ita kuyi magana. 

Bayan sunzo Sameer ya d’ora guiwarsa k’asa ya had’e hannuwansa biyu yana rokon su yafiya. Cikin kuka Maman Halima tace ta yafe masa. Kallon Halima yayi yana sake rok’onta. 

Jinjina kai tayi tana share hawayen idonta tace na yafe maka, koba komai ta silata Allah ya ganar da kai gaskiya, kuma bazan bijirema Allah ba naki yafe maka ba, ina fatan kamar yanda ka cutar dani kuma ka rokeni yafiya na yafe maka Allah ya d’aukaka rayuwata, yasa ko nan gaba kada na wulak’anta daga ni har zuri’ata. 

Gaba d’aya suka amsa da amin. Ra’eez yace gaskiya Halima kinyi matuk’ar burge ni, domin kalamanki masu tsada ne sai mai zurfin ilimi ne zai iya amfani dasu, gasu sun fito daga bakin mai k’ananun shekaru, ubangiji Allah ya amsa addu’ar ki amin. 

Jabeer yace Allah ya k’ara tsare gaba, ga wannan check d’in kud’in ki ne da kotu tace abaki, Baba idan kana da asusu a banki sai muje a ciresu asaka aciki domin zasuyi mata amfani wajen karatun ta. 

Baba yace gaskiya banda wani asusu a banki, amma inaso aje a bud’e da sunan Halima sai azuba su ciki, hakika badan hakkinta bane babu abinda zaisa na amshi kud’in nan, amma sune zasu taimaka ma rayuwarta wajen inganta, domin burin ta ne karatu musamman a fannin lafiya. 

Kallonshi Sameer yayi yana fad’in ta kammala makaranta ne Baba? Kai ya d’aga masa yana fad’in sakamakonta ma yayi kyau. 

Jinjina kai yayi yana fad’in zaka iya barinta taje waje tayi karatun fanin lafiya kamar a Madina? Shiru Baba yayi yana tunani. Ra’eez yace Baba ka barta ta tafi, domin Madina k’asa ce mai kyau, kuma zatayi karatu hankalinta a kwance, sannan zata koyo abubuwa da yawa na addini, a ganina Halima tana da natsuwar da zatayi karatu a waje. 

Kai Baba ya jinjina ya kalli Halima yana fad’in zaki iya Halimatu? Saurin d’aga kai tayi tana sakin murmushi. Baba yace shikenan na amince, nasan wad’an nan kud’in zasu isheta ta kammala karatun ta. 

Sameer yace Baba zan bayar da naira million biyar nasan zasu isheta ta kammala karatunta, sannan nine zan sama mata makarantar, wannan itace babbar kyautar da zan bata bisa yafiyarta agare ni, fatana Allah yasa kada mu samu rabo a tsakanin mu. 

Baba yace nagode sosai, kuma insha Allahu babu rabon da za’a samu, domin tun a asibiti wannan malamar ta kawo mana wani magani tace abata tasha insha Allahu ciki bazai shiga jikinta ba. 

Sameer yace amma naji dad’i sosai, kuma zanje nayima sister Asabe kyauta domin ta taka rawar gani akan wannan matsala, Allah ya k’ara tsare gaba. Gaba d’aya suka amsa da amin. 

Ra’eez yace gobe idan Allah ya kaimu ko daga ofis ne zan zo na d’auki Halima muje a bud’e mata asusu a banki. Sameer yace muje na rubuta mata kud’in sai a had’a dasu. 

Godiya sukayi masu kafin suka masu sallama suka tafi. 

Bayan sun koma Sameer yace nagode sosai Ra’eez, Allah ya baka abinda kake nema duniya da lahira, ka bani account d’inka ina so nayi maka alheri. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button