ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in ka barshi, badan kud’i nayi maka ba, ko a iya abinda kamun ka biyani. Sameer yace nagode sosai, Jabeer nagode Allah ya huta gajiya. 

Jabeer yace amin Allah ya k’ara tsare gaba, sai a daure a nemo mata kafin muma muzo mu wuce ka. Dariya suka sa gaba d’aya. Sameer yace insha Allahu zanyi kok’arin haka nima nasan na kusa tsufa damma bani da jikin kiba dan nayi arba’in idan ban wuce ba. 

Ra’eez yace to Allah ya kawo ta gari. Murmushi Sameer yayi kwalla ta cika idonshi yana fad’in bazan ce maka komai ba domin kace Allah, amma bana tunanin zan samu mace tagari tunda ban kasance nagari ba. 

Ra’eez yace kada kayi saurin yanke hukunci domin Allah baya duba da haka, abinda yake so ka tsarkake zuciyarka. Sameer yace insha Allahu nagode. 

Suna shirin sallama wata mota ta tsaya a kusa dasu, kid’an da yake tashi ne a ciki yasa hankalin su ya koma kanta. 

Wani gaye ne ya fito sanye da k’ananun kaya masu matuk’ar tsada a jikinsa fuskarsa sanye da wani bakin glass mai tsadar gaske. Rufe motar yayi yana taunar cingam. 

Saurin cire glass d’in yayi yana fad’in Yaya Sameer, saurin k’arasowa yayi yana shafa kai. Murmushi Sameer yayi yana fad’in Fawwaz dama ka dawo k’asar nan? Risnawa yayi yana gaishe shi. 

Hannu Sameer ya mik’a mashi suka gaisa, juyawa yayi yabama su Ra’eez hannu. Sameer yace lallai Fawwaz ka zama babban yaro da yawa ga abokin ka can hada yara biyu. 

Fawwaz yace ai bansan meya shiga kan Adnan ba Yaya, ko kai bakayi aure ba sai shi, lokacin muna secondary kamar wayayye amma muna rabuwa shikenan yanemi zama ustaz, bansani ba ko jami’ar da yayi a Nija ne ya sashi komawa haka, shiyasa naji dad’i lokacin da Dad yace waje zai kaini karatu, koda na gama kawai nayi zama na acan sai wancan watan ne na dawo shima Mom ce ta matsa na dawo ta gaji. 

Sameer yace ai gashi ya zama Baba ya bar ka, ina d’ayan abokin naku? Fawwaz yace Allah sarki Sufwan, har ka tuna mani dashi, ina can Adnan yake fad’a mani mutuwar sa domin kowa yasan mu three stars ne a Kings college amma mutuwa ta rabamu dashi daga zazzab’i na kwana biyu, gaskiya naji mutuwarsa sosai. 

Sameer yace Allah yajik’ansa, lafiya kazo kotu? Fawwaz yace Dad ne ya aiko ni wajen Abba Barau. Kai Sameer ya jinjina yana fad’in ai kotun taku ce. 

Murmushi Fawwaz yayi yace kai Yaya. Sameer yace emana, ai na d’auka kaima zaka biyo Dadyn ka ko lauya ka karanta ai yayi. Fawwaz yace Yaya wannan karatun ba irin namu bane. 

Sameer yace to Allah ya taimaka, ka gaishe da mutanan gidan. Fawwaz yace zasuji agaishe da Adnan amma zanje naga Yaranshi. Sameer yace zasuji. 

Sallama yayi masu ya wuce yana tafiyar ‘yan gayu. Murmushi Sameer yayi yana girgiza kai. Jabeer yace dama wannan shine Fawwaz d’an tsohon Alkalin kotun nan? Sameer yace shine fa, kai duniya babu gaskiya, idan kana da iko da kud’i baka da matsala. 

Ra’eez yace ai shiyasa mutane suke son kud’i. Sameer yace yaron nan fa alokacin suna makaranta har kisan kai ya tab’ayi amma da yake Mahaifinsa babba ne ko maganar ba’a tada ba, agaban su Adnan yayi kisan sai dai kasancewar su aminan juna ne yasa suka rufa masa asiri, kuma Mahaifinsa ya basu kud’i masu yawa shikenan sukayi shiru alokacin Adnan yana Niga, uhm shikenan maganar ta mutu, yaron ma da sukace ya gansu shima babu labarinsa sai gawarsa aka tsinta, silar haka aka tura Fawwaz waje karatu. 

 Shiru Ra’eez yayi yana tunani, da sauri ya kalli Sameer yana fad’in a wace shekara akayi abun? Sameer yace lokacin dai suna aji shidda dan har sun fara jarabawar fita, ina ganin kamar 2008 ne, E a lokacin Adnan ya kammala makarantarsa. 

Jikin Ra’eez ne yayi sanyi, tabbas wannan labarin yana da had’aka da yaron da Kawu ya bashi labari, amma zaibi komai a hankali zai had’a kan zaren da sannu. 

Sameer yace bara na wuce na tsaya ina cinye maku lokaci. Jabeer yace shikenan mungode sai munyi waya. Hannu ya basu yawuce. 

Dafa Ra’eez Jabeer yayi yana fad’in lafiya kuwa Ra’eez? Ajiyar zuciya Ra’eez yayi yana fad’in me ka gani? Jabeer yace tun lokacin da naji an fad’i mutuwar wannan yaron ka tambayi shekarar da akayi abun naga kamar ka canza. 

Murmushi Ra’eez yayi yace kawai abun ne ya bani tsoro, dalilin tambayar shekarar ina so nasan shekarunsu har suka iya aikata haka. 

Jabeer yace to yaran masu kud’i meye basa aikatawa, kai dai kawai ayi sha’ani. Ra’eez yace Allah ya kyauta. Wayarsa ce tayi k’ara, yana dubawa yaga ansa Journalist, murmushi yayi dan ya gane Rafeek ne. 

Bayan sun gaisa Rafeek yace ko anjima bayan isha’i kana da lokaci na kawo maka ziyara? Ra’eez yace ina nan kuwa, zan turo maka da kwatencen. Rafeek yace to nagode. 

Kallonshi Jabeer yayi yana fad’in kai da wa? Ra’eez yace wani d’an jarida ne yake son mu had’u bayan isha’i. Jabeer yace sarakan tambaya, sai ka kula kada su saka fad’ar wani abun kasan su da wayon tsiya ga dabara. 

Ra’eez yace ai tsakanin su da ‘Yan sanda da kuma mu ana fafatawa, domin kowa yana da ilimin fasaha da ‘yan dabaru, dan haka kada ka damu zan iya bi dashi. Jabeer yace ai nasanka. 

****

Bayan sun tashi daga aiki sukayi sallama da Jabeer kowa ya shiga motarsa ya tafi. Har Ra’eez ya d’auki hanya wayarsa tayi k’ara, yana dubawa yaga Kawu Datti, saurin tsayawa yayi ya kashe wayar sannan ya kirashi. 

Cike da farin ciki yace gani nan waje Kawu bara na matso. To shikenan bara na jiraka anan sai ka zo. Kashe wayar yayi cike da farin ciki. 

Kwankwasa k’ofar da akayi yasa yayi saurin bud’ewa. Shigowa Kawu Datti yayi ya zauna ya rufe k’ofar. Kallon Ra’eez yayi kafin ya d’age rigarsa ya zaro kundu ya mik’a ma Ra’eez yana fad’in ban tsaya dubawa ba kawai na d’auko maka shi kaje ka duba amma ka maidoshi da wuri, Allah yasa kana da abun photo copy dan bana son kaje wani waje ayi maka idan baka dashi gara ka kwafeshi kawai. 

Ra’eez yace nagode Kawu Datti, kuma babu wanda zai san dashi ina da komai a gidana zanyi na maido maka shi gobe. Kawu Datti yace ina maka fatan nasara. 

Kud’i Ra’eez ya ciro ya mika masa yana fad’in amin. Girgiza kai Kawu Datti yayi yana fad’in idan na amsa tamkar cin hanci ka bani. 

Ra’eez yace wallahi Kawu ba cin hanci bane, ai tsakanin mu babu wannan, ka d’auke ni tamkar d’anka dan Allah Kawu. 

Murmushi yayi ya amsa yana fad’in nagode sosai. Ra’eez yace nima nagode. Sallama yayi masa ya fice daga motar ya koma ofis. Hamdala Ra’eez yayi yawuce gida cike da murna. 

****

Sai da suga gama firar soyayya da Rumaisar sa kafin yayi masu sallama dan yasan Rafeek ya kusa zuwa. Har bakin mota ta rakashi sai shagwab’a take masa bata so ya tafi. Ra’eez yace kiyi hak’uri ai kullum muna tare, kicigaba damun addu’a domin nakusa fara bincike, dan haka dole ki aramun lokacinki. 

Rumaisa tace bakomai in dai lokaci nane na baka domin naka ne, kuma ina maka fatan nasara, addu’a kuma kullum ina maka. Murmushi yayi yace nagode Pretty na. Sallama sukayi yawuce. 

A hanya Raheena ta kirasa, kin d’auka yayi dan baya son damu yasan kuma daya d’auka zata tsaidashi da surutu. Ganin ta cigaba da kira yasa ya d’auka, ko magana batayi ba yace mata yana hanya ta bari wajen 11 zasuyi waya. Kashe wayar yayi yana tsaki ya k’ara gudun motar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button