ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

*** 

Lemu da ruwa ya aje masa yana fad’in sannu da zuwa Yaya. Murmushi Rafeek yayi yana fad’in yauwa sannu Ra’eez, yau dai bani da aikin dare nace zan zo mu gaisa sosai. 

Ra’eez yace ai naji dad’i sosai, naso na fara kai maka ziyara gashi har ka rigani. Rafeek yace ai bakomai, na fad’a maka babu babba a abota. 

Jinjina kai Ra’eez yayi ya mik’a masa ruwan daya zuba yana fad’in gidan gauro ne babu abinci. Dariya Rafeek yayi yace haba ai babu komai, wata rana idan kayi auren zan zo naci. 

Kallon Ra’eez yayi yana fad’in gaskiya ka burge ni a shari’ar da kukayi jiya, kuma nayi mamaki da kayi masu haka, sai nake tambayar kaina dama kasan gaskiya ne yasa kace kaine zaka tsaya masu? Girgiza kai Ra’eez yayi yana fad’in Mahaifin yarinyar da ya fad’a mani abinda ya faru yasa nace zan taimaka masu, duk da alokacin na riga na amshi tayin su Sameer. 

Rafeek yace ai ka kyauta sosai Allah ya biyaka, shima Mahaifin Halima ya burge ni, duk da yana talaka amma ya iya neman hakkinsa, wallahi ina son naga an zalunci mutum ya tsaya akan neman hakkinsa. 

Ra’eez yace nima ina son irin mutane masu dakakkiyar zuciya haka, shiyasa nace zan taimaka masu sosai. 

Rafeek yace shiyasa a shekarun baya da aka kashe K’ani na naso mushigar da k’ara amma Baffa yace baya so dole muka hakura, duk da alokacin ina makaranta amma naso ashigar da k’ara. 

Ra’eez yace Allah sarki, ashe kaima an kashe maka wani, to Allah yaji k’ansa. Rafeek yace amin, har yanzu inajin d’acin mutuwar Naseer, yaro yana shirin kammala secondary d’insa amma aka samu wasu suka kashe shi, kamar marar gata haka aka wurgar da gawarsa. 

Ra’eez yace wayyo Allah ya saka masa, yana gab da fara sabuwar rayuwa suka katse mashi ita, domin duk wanda ya gama secondary alokacin yake fara shirya burinsa. 

Rafeek yace wallahi kuwa, a Kings college yake har sun fara jarabawa aka kashe shi, a shekarar su biyu aka kashe a makarantar kuma duk ajinsu d’aya. 

Saurin kallonshi Ra’eez yayi yana fad’in a wace shekara ne Yaya? Kallonshi Rafeek yayi yace shekarar 2008 ne, ai bazan iya mantawa da wannan shekara ba, alokacin ina jami’a. 

Shiru Ra’eez yayi jikinsa yana tsuma, runtse ido yayi yana tasbihi ga Allah, tabbas Allah ya fara haska masa akan shari’ar da zai gabatar, domin ayau ya fara had’uwa da abubuwan da sukayi had’aka da rayuwar Abbunsa, tabbas yana buk’atar natsuwa yayi dogon nazari, dole yaje kano yayi shawara da Abbah akan Rafeek, domin yaji ajikinsa shid’in zai taimaka masa da wani abu, yana jin zai iya bari yasan wayeshi da kudirinsa, amma idan Abbah be amince ba shikenan zaiyi yakin shi kad’ai. 

Dafashi Rafeek yayi yana fad’in Ra’eez lafiya kuwa? Ajiyar zuciya ya saki yana fad’in Yaya abun ne akwai tausayi, wallahi bana so naji an kashe mutum, kawai ina hango yanda mutum zaiji alokacin da ake kashe shi, Allah yajikansu da rahma. 

Rafeek yace amin. Amma Ra’eez ba anan garin kake ba ko? Ra’eez yace a Kano nake aiki ne ya maido ni nan. Jinjina kai yayi yana shirin jefo masa wata tambayar wayarsa tayi k’ara, yana dubawa yaga Baffansa ne. 

Bayan ya gama wayar ya kalli Ra’eez yana fad’in Baffa ya katse mana fira, wai yana nemana yanzu. Ra’eez yace kai amma banji dad’i ba muna ta firar mu. Rafeek yace bakomai idan nasamu lokaci zan dawo dan bana so mu had’u a ofis d’in ku ko namu dan kowa yasan su waye mu, da an gammu tare kowa zai fara tunanin wani abu, dan haka idan ka samu lokaci idan zaka kawo mani ziyara a gidana zakaje. 

Ra’eez yace insha Allahu nagode sosai. Tashi yayi yana fad’in nima nagode. Har bakin mota ya rakashi, sai da ya tafi sannan ya rufe gidan, kundin da Kawu Datti ya bashi ya d’auka ya nufi d’akin kayan aikinsa domin ya fara gamawa da su. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

3⃣2⃣

A wannan dare Ra’eez kashe wayarshi yayi dan baya son damu, sai da ya gama copying komai kafin ya maida komai yanda yake yasa a leda dan kada ya manta, d’akinshi ya koma ya fara duba takardun. 

A hankali ya gama karanta komai, ya mai-maita yafi so ukku, hawaye ne kawai suke zuba a idonshi, yana kallon abun kamar yana wajen yake faruwa, jiyake ina ma shine lauyen da yayi shari’ar a wancan lokacin, domin ga hujjoji nan da yawa daya kamata akare Kawu dasu amma ba’ayi amfani dasu ba, tabbas yasan lauyen daya kare Kawu sarewa yayi alokacin shiyasa be kula da hujjojin ba. 

Jin kansa yana ciwo yasa ya tattara komai ya tura k’asan gado dan yasan anan ne kawai zasu b’oyu, duk da shi kad’ai ne agidan dole ya fara b’oye duk wata sheda tashi saboda ayanzu zai fara fuskantar kalubale saboda da manyan mutane zai gwabza, zesa rayuwarsa cikin had’ari, idan yana da tsawon rayuwa shikenan, idan kuma akan kwato ma Mahaifinsa hakkinsa zai rasa ransa a shirye yake daya bada ranshi. 

Bayan ya adana komai ya kwanta yana tunanin ta yanda komai zai kasance da haka har bacci yayi gaba dashi. 

**** ****

Washe gari tunda wuri ya isa ofis, sai da ya bama Kawu Datti kundin yayi ta masa godiya, sosai Kawu Datti yaji dad’i, hankali kwance yaje ya maida inda ya d’auko su. 

Bayan ya rage aikin da yake gabanshi ya samu ya fita dan yaje ya d’auko Halima su gama komai da wuri. Babu b’ata lokaci suka kammala komai cikin lokaci. 

Sai da ya maidata gida sannan ya koma ofis. Yana shiga yayi turus yana kallonta zaune a saman kujera Jabeer ya kawo mata lemu tana sha. 

Saurin tashi tayi tana sakin murmushi, matsowa tayi tana fad’in D. sannu da dawowa wallahi na kasa hakurin rashinka shiyasa nazo, tun d’azu ma naso nazo Momy tace na bari sai anjima. 

Murmushi Ra’eez yayi ya ratse ta yawuce ciki. Zama tayi tana fad’in na manta ina kwana? Ra’eez yace lafiya lau, daga shigowata ba gaisuwa kin rufeni da surutu. 

Hannu tasa abaki tana fad’in wallahi mantawa nayi kewarka ce tamun yawa shiyasa duk na rud’e. Ra’eez yace ai na fad’a maki ina da aiyuka agabana. 

Raheena tace duk da haka D ko waya ne sai ka kirani, bakasan yanda nake shiga damuwa ba idan banjika ba, dama kai ba kirana kake ba ni kuma na kira kace kana aiki. 

Ra’eez yace daga yau kada ki sake zuwa wajen aiki na, duk macen da take iya bin namiji to bata da daraja a idon kowa, kuma ni bazan iya auren macen da take bina ba, domin zan rik’a ganin kowama haka kike masa. 

Saurin tashi tayi tana fad’in Allah ban tab’a bin kowa gidanshi ba, kaima dan ina sonka shiyasa na biyoka amma kayi hakuri bazan sake ba. Kai ya d’aga ya jawo wasu takardu yana fad’in hakan zaifi maki. 

Jabeer ne yashigo hannunsa d’auke da leda da alamu wani abu ne a ciki. Tsaye yayi yana kallon Ra’eez. Jaka Raheena ta d’auka tana fad’in Jabeer zan wuce. 

Saurin kallonta yayi yana fad’in ban gane ba, keda kikace mun wuni kikazo mana taya zaki tafi kuma? Murmushi tayi tana kallon Ra’eez tace dama Momy ce tace nazo zata aike ni. 

Kallon Ra’eez Jabeer yayi yana murmushi. Kauda kai yayi yacigaba da aikinsa. Jabeer yace shikenan ga wannan sai ki tafi dashi. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button