ALKALI NE Page 51 to 60

Amsa tayi tana godiya. Jabeer yace ki gaishe da Momy sai mun leko, Yallab’ai sai kaje ka rakata ai. Harara Ra’eez ya aika masa.
Raheena tace haba Jabeer ya kake son bama D wahala bayan yanzu ya dawo, ka barshi ya huta, kallon Ra’eez tayi tana fad’in D kayi aiki lafiya amma kada ka matsa ma kanka dan Allah.
Murmushi yayi yana kallonta, sai kuma ta bashi tausayi ganin yadda tayi kok’arin kareshi a wajen Jabeer, tabbas yasan zuwa yanzu Raheena ta canza sosai.
Tasowa yayi yana fad’in nagode Raheena da ziyara ki gaishe da Momy idan na samu lokaci zan zo nima. Murmushi ta saki tana jin wani dad’i.
Iyaka bakin k’ofa ya tsaya dan baya son kowa ya ganshi da ita. Sai da ta tafi kana yashigo ciki. Dariya Jabeer yasa yana fad’in Allah ya shiryeka abokina.
Tsaki Ra’eez yayi ya zauna yana fad’in zaka fara ko? Jabeer yace kai d’in ne sai a hankali wallahi kana wahalar da Raheena sosai.
Ra’eez yace ai sai ka rama mata. Jabeer yace ni na isa, kawai tausayinta nakeyi, saboda kai duk ta canza, kalli yanayin shigarta komai ya canza, wallahi tausayi take bani, irin su Raheena zasu iya yin komai akan abinda suke so, kuma ko aurensu kayi baka tab’a samun matsala dasu.
Tab’e baki Ra’eez yayi yana fad’in kaga malan ina da aiki gara kaje kayi hidimar gabanka. Rik’e baki Jabeer yayi yana fad’in lallai kam, ya Allah ka nuna mani ranar da Ra’eez ze fad’a son Raheena.
Tofar ta miyau Ra’eez yayi yana fad’in har abada wallahi, nan take idanuwansa suka canza kala yana b’ata fuska. Shiru Jabeer yayi cikin mutuwar jiki yake kallon Ra’eez.
Kasa rubuta komai yayi haka ya rufe takardun da k’arfi yayi saurin barin ofis d’in yana jin wani b’acin rai. Sosai jikin Jabeer yayi sanyi akan abinda ya faru, bai tab’a ganin Ra’eez a irin wannan yanayin ba,daga wannan maganar har zai iya fushi haka, ya d’auka yana son Raheena amma yau ya tabbatar da zahiri, sai dai dole akwai dalili. Ajiyar zuciya ya saki tare da barin ofis d’in.
***
Bayan an tashi ya fito ya hangi Jabeer a jikin motarsa yana kok’arin shiga, da sauri ya k’arasa wajensa. Dafashi yayi yana fad’in yau guduwa zakayi babu sallama.
Murmushi Jabeer yayi yana fad’in haba Ra’eez, meyasa har yanzu baka d’auke ni kamar yanda na d’auke ka ba? Kasan kuwa yanda na d’auke ka? Wallahi kamar d’an uwana da muka fito ciki d’aya haka nake jinka, amma na lura akwai abubuwan da kake b’oye mani naka, ban gama tabbatarwa ba amma ka sani duk ranar dana tabbatar da hakan aranar zan san matsayina awajenka, domin ni ban b’oye maka komai nawa ba, tun ranar had’uwar mu na sanar da kai komai nawa, amma babu komai bance dole sai ka sanar dani labarin ka ba.
Ajiyar zuciya Ra’eez ya saki idanuwansa suka ciko da kwalla, tabbas ya aminta da Jabeer, amma alk’awarin Abbah ne bazai fad’ama kowa labarinsa ba yanzu.
Jin motsin Jabeer yashiga mota yasashi saurin shiga yana goge idonshi. Da kallon mamaki Jabeer ya bishi. Hannunsa Ra’eez ya kamo yana fad’in kayi hakuri Jabeer, zanje kano cikin satin nan nayi maka alk’awarin zan sanar da kai labarina idan na dawo.
Murmushi Jabeer yayi ya rik’o hannunsa yana fad’in kada kadamu abokina, bana son kana zubar da kwalla, na dad’e da sanin kana da ciwo aranka sai dai bansan komeye ba, amma nasha ganin ka cikin damuwa wani lokacin, dan haka kayi hak’uri da abinda nace maka bazan sake tada maka maganar ba.
Murmushi yayi yana fad’in nagode da ka fahimce ni. Jabeer yace bakomai zo mu tafi. Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in ka gaishe da Mamy. Jabeer yace zataji agaida Rumaisa.
**** ***
A ranar alhamis ya lek’a gidan su Raheena saboda damunshi da tayi yazo siyi sallama zasuji Dubai ranar asabar.
Bayan sun gaisa da Momy Raheena ta shige kicin domin d’auko masa kayan motsa baki. Kallonshi Momy tayi tana fad’in yau dai Raheena hankali zai kwanta kazo, kullum cikin damuwana take kaki zuwa, nace mata ai aikin ku haka yake, shine yau tace zaka zo kuyi sallama.
Kai a duk’e Ra’eez yace wallahi kuwa. Momy tace ai gara muje a fara rago siyayyar kayan d’aki dan Alhaji yace baya son bikin yawuce wata guda, shine zamuje Dubai jibi musiyo kayan d’aki, naji tace kaima zaka je kano ko? Kai Ra’eez ya d’aga yana mamakin wannan lamari.
Momy tace idan kaje ka gaishe su, ai gara kaje a kammala komai, muma kwana biyu zamuyo kada suzo bamu dawo ba. K’ara duk’ar da kai Ra’eez yayi yana sakin murmushi.
Tashi Momy tayi tana fad’in Raheena kuje falon baki nan kada ayita gitta maku. Raheena tace to Momy. Kallon Ra’eez tayi tana fad’in D muje can.
Kallonta yayi yana sakin murmushi mai kama da dariya yace ai wucewa zanyi akwai abinda zanyi. Zama tayi tana fad’in kai D zamuyi sallama bazaka tsaya muyi fira ba kuma.
Hannu ya mik’a mata alamun ta zuba mashi ruwa. Saurin zuba masa tayi ta mik’a masa tana fad’in yi hakuri ina wuni. Lafiya lau sarkin mantuwa, ya amsa. Murmushi tayi tana rufe fuska.
Tashi yayi yana fad’in Allah ya kiyaye hanya zance ko? Murmushi tayi tace nagode kaima ka dawo lafiya, me kake so nasiyo maka? Ra’eez yace dama tambaya akeyi? Girgiza kai tayi tana fad’in shikenan zan kawo maka zab’ina.
Kai ya jinjina yana fad’in ki gaida Momy zan wuce. Biyoshi tayi tana fad’in wallahi kamar kada ka tafi. Ra’eez yace dole ko na tafi. Har bakin mota ta rakasa, sai da ya tafi kana ta wuce gida.
Daga wajenta wajen Kawu ya wuce, sun dad’e suna tattaunawa kuma ya sanar masa duk kok’arin da yakeyi kana ya fad’a masa zaije kano gobe. Kawu yace agaishe mani da Alhajin kuma insha Allahu zan cigaba da addu’a Allah yashige mana gaba. Ra’eez yace amin, zasuji.
Sai da ya fara biyawa wajen Ummunsa kafin yawuce gidansu Rumaisa, daga can bayan ya gama yawuce gida dan yagaji sosai.
*** ***
Washe gari be tsaya aka tashi dashi wajen aiki ba, bayan yayi ma Alhaji Barau sallama Jabeer ya kaishi filin jirgi dan ta jirgi zai bi. Sun dad’e suna fira kafin lokacin tafiyarsu yayi, haka sukayi sallama ya tafi.
***
Jinjina kai kawai Abbah Mansur yake yana kallon takardar da Ra’eez ya kawo mashi hawaye suna fita a idonshi. ‘Dago kai yayi yana kallon Ra’eez wanda shima kukan yakeyi bayan ya gama fad’a masa abinda ya faru da kuma wanda ya gani awajen Rafeek da Sameer wanda suka fad’a masa.
Hannu Abbah yasa ya goge idonshi yana fad’in tabbas a wannan karon Ra’eez kaine zakayi nasara a kotu, hakika Malan Datti yana da matuk’ar mutunci, sannan na amince maka daka fad’ama Jabeer da Rafeek sirrinka, domin inaji ajikina sune bangon da zaka jingina dasu, sune tsaninka wanda zaka taka zuwa matakin da nakeso kaje, domin na fahimci Jabeer aboki ne nagari, dan haka ka sanar dashi komai saboda duk lokacin daya fahimta da kanshi abotar ku zata iya samun matsala.
Ra’eez yace shikenan Abbah zan fad’a masu, dama umarninka nazo nema dan bana so nayi abinda ya kaucema umarnin ka. Murmushi Abbah yayi yana fad’in na sani Ra’eez, nasan bazaka tab’a tsallake umarni na ba, Allah yayi maka albarka.
Ra’eez yace amin Abbah. Murmushi yayi yana fad’in zuwa gobe sai ka lek’a wajen Labiba ku gaisa dama tana korafin rashin zuwanka. Ra’eez yace tunda nazo dole naje mu wuni muyi fira.
Abbah yace maganar motar fa? Sosa kai Ra’eez yayi yana fad’in Abbah kaga gobe zanje gidan Mamyn Sultan bansan lokacin da zan dawo ba, kuma jibi da wuri nake son tafiya inaga abar motar zan dawo ko nan da wata d’aya sai na kaita gyara.