ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 51 to 60

Abbah yace da alamu nakusa sayar da motar nan. Zaro ido Ra’eez yayi yana fad’in kai Abbah, shikenan ko ina can sai ka bama mai gyaranka sai ya duba mani ita kaga ina dawowa sai na tafi da abuna. 

Murmushi Abbah yayi yana fad’in shikenan zan bashi ya duba maka ita amma yanzu yayi tafiya ni kuma nafi aminta dashi idan ya dawo zan kirashi yazo ya tafi da ita, amma ka sani bazaka je Lagos da ita ba, ko an gyara ta anan za’a barta domin ana kammala wannan shari’ar Kano zaku dawo gaba d’aya sai kacigaba da aikin ka anan. 

Ra’eez yace haka ne Abbah, nima bani da buk’atar zama a Lagos, muna kammala shari’ar har gidan zan sayar domin nasan Ummu bazata iya komawa gidan nan ba. Abbah yace to Allah yashige mana gaba. Ra’eez yace amin. 

**** ***

Yaji dad’in zuwanshi Kano har yaji kamar kada ya tafi, haka Abbah ya kaishi ya hau jirgi ya tafi cike da kewar juna. 

Tun kafin ya taso ya sanar ma Jabeer, aikuwa suna sauka ya iskeshi yana jiranshi. Rungume juna sukayi kafin suka shiga mota suka tafi. 

Jabeer yace wallahi abokina ka canza kwana biyu. Ra’eez yace ba dole ba ina can ana shagwab’ani. Dariya Jabeer yayi yana fad’in naga alama ai. 

Waya Ra’eez ya ciro ya kira Rafeek. Bayan sun gaisa Ra’eez yace Yaya ko kana wani abu zuwa dare? E dama inaso kazo gida akwai maganar da zamuyi ne. Toshikenan sai kazo nagode. 

Jabeer yace ina ka samu Yaya kuma? Murmushi Ra’eez yayi yace wannan d’an jaridar da nake fad’a maka ne. Jabeer yace lallai kayi Yaya kuwa. Ra’eez yace idan yazo zan fad’a maku wata magana, dan haka yau muna tare. Jinjina kai Jabeer yayi yace Allah ya kaimu. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

3⃣3⃣

Lokacin da Ra’eez ya kammala basu labarinshi babu abinda akeji sai sautin kuka, gaba d’ayansu an rasa mai lallashin wani. A hankali Ra’eez ya zame ya kwanta yana jin wani iri a zuciyarsa, kasancewar shine aka bama labarin da farko shiyasa beji abinda yakeji yanzu ba, dan ayanzu da yake bada labarin abinda ya faru da kanshi sai yakejin wani irin d’aci a ranshi. 

Sun dad’e a haka kafin Rafeek ya kamo hannun Ra’eez yana fad’in tabbas Yaron da Abbunka ya rage ma hanya Naseer ne k’anina, domin a ranar shima aka tsinci gawarsa, duk da bani da masaniyar haka amma zuciyata ta bani hakan, domin kace Kawunka ya fad’a maka yaron da suka d’auko yace abokinsa ne yaron da suke magana alokacin an kashe a kings college, tabbas ina zargin mutane iri d’aya ne suka aikata kisan Abbunka da Naseer, banbancin shi Abbunka bayan an kashe shi anyi amfani da allura, amma da wuya idan allurar aka fara masa, domin ance akwai sahun hannu na shaka, haka shima Naseer shakeshi akayi har ya rasu. 

Ajiyar zuciya yayi yana fad’in dole akwai abinda Naseer ya sani agame da mutuwar abokinsu wanda Sameer yace Fawwaz ne ya kashe shi, tabbas wannan yaron da Adanan k’anin Sameer yace ya gansu shima ankashe shi Naseer ne, amma zamu zauna mu zana yanda komai yakasance, dole akwai abinda yake faruwa, 

 Abbunka – Naseer

             ⬇

 *Fawwaz, – tsohon Alkali mahaifin Fawwaz,- Alhaji Barau,- Alhaji Marusa, – Mr. Kallah*. 

 Wad’annan mutanan suna da alak’a da mutuwar Abbunka, idan ko haka ne Alhaji Barau shine abokin tsohon Alkali a wancan lokacin, kunga Fawwaz yaron Alkali yayi kisa dole su san yanda suka shafe maganar, domin wannan dalilin ne yasa aka tura Fawwaz waje karatu. 

Saurin gyara zama Jabeer yayi yana fad’in, amma ya akayi Naseer yaje wajen aikin Abbun Ra’eez? Domin a cikin labarin Kawu yace sunzo fitowa suka had’u dashi hakan yasa suka taimaka masa, bayan kuma kace aranar yace ma Hajiyar ku zaije wajen abokinsa Mannir, kuma kace ba wajen unguwarsu bane, to meya kaishi wajen aikinsu Abbunka? 

Rafeek yace yes! Wannan maganar taka tana kan hanya, a yanzu muna cikin damuwa dan haka mu bari bayan kwana biyu muzo anan domin mu bama kanmu tambaya kuma mu nemo amsa, kafin nan dole sai Sameer yashigo, domin ya had’amu da K’aninsa, sai dai bazamu fad’a masu case d’in Abbunka ba, iya abinda ya shafesu kawai zamu sani, case d’in Abbunka ya tsaya iya mu har zuwa lokacin da komai zai kammala, sannan bayan mun fara wannan aikin dole muna buk’atar ganin Uncle d’in ka Jabeer, domin shine lauyen daya tsaya ma Kawu a wancan lokacin, kaga yanzu yana abuja babbar kotu komai zai zo mana da sauki. 

Jabeer yace babu damuwa, naji Dady yana maganar zasuyi wani taro k’arshen satin nan na family ne kuma maza kad’ai ne zasu zauna, nasan dole Uncle zaizo dan irin wannan taron baya wuceshi, abinda nake gani mu bari yazo zanyi masa maganar, idan yana buk’atar ganin ku sai muje gaba d’aya. 

Rafeek yace yauwa komai ma zaizo da sauki, insha Allahu wannan shari’ar da zafi zamu d’auketa, a wannan karon zasu gane kuskurensu, domin zasu had’u da ‘yan zamani, kamar yanda sukayi amfani da basira haka zamuyi muma, kuma a hankali zan nemo duk mutanan da suka bada gudummuwa wajen aikata laifi, zan amshi sunayen likitocin da suka kula da gawar Abbu, hatta da wanda ya duba Ummunka inaso na ganshi, sai kuma ‘yan sandan da suka kula da case d’in dan nasan yanzu duk sun zama manya, amma komin girman mutum bazai ja da shari’a ba, insha Allahu zamu gudanar da komai, Ra’eez kasa aranka tare zamuyi wannan yaki, kuma insha Allahu zamuyi nasara, sai Kawu ya fito kuma sai an d’aure duk wani mai hannu a cikin wannan laifin. 

Jinjina kai Ra’eez yayi yana hawaye dan ya kasa magana saboda wani sanyi da yakeji. Kamoshi Jabeer yayi sai yaji jikinsa yayi zafi ga rawar sanyi da yakeyi. Saurin kallon Rafeek yayi yana fad’in Yaya Ra’eez fa beda lafiya. 

Tasowa Rafeek yayi yana fad’in damuwace ta haifar masa da hakan, ai yana ma kok’ari, akwai ciwo arayuwarshi amma haka yake daurewa domin ya sa burin d’aukar fansa aranshi, dole muje asibiti a aunashi saboda asan irin maganin da za’a bashi dan damuwa tayi masa yawa. 

Jabeer yace Ra’eez tashi muje asibiti. Girgiza kai yayi yana hawaye. Rafeek yace wallahi sai munje, matuk’ar kana son kammala wannan shari’ar to ka bari a duba lafiyar ka, sannan kasa jarumta aranka kamar yanda Kawu yayi, idan ba haka ba ciwo zai kwantar da kai. 

Jinjina kai yayi yana kok’arin tashi, kamoshi Jabeer yayi tare da gyara masa rigarsa suka fita waje, rufe gidan sukayi suka wuce asibiti. 

***

Cire glass likitan yayi yana fad’in Rafeek ya akayi Brr, yake barin damuwa aranshi har haka? Jininsa fa ya hau ga zuciyarsa tana samun damuwa saboda yana yauwan tunani, gaskiya dole akula dashi idan ba haka ba zai iya kamuwa da ciwon zuciya. 

Jinjina kai Rafeek yayi yana fad’in insha Allahu za’a kiyaye likita, kasan yanayin aikinsu, ga rashin hutu gashi dole sai mutum yana zurfafa tunani, amma duk da haka za’a kula insha Allah. 

Likita yace dama kana da alak’a da hazikin lauyan nan? Murmushi Rafeek yayi yana fad’in cousin d’ina ne a Kano suke da zama. Likita yace lallai kunyi dace da samun hazikin lauya, dan haka ku kula dashi kada al’umma ta rasa mutum mai gaskiya. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button