ALKALI NE Page 61 to 70

A hankali muka zama manya amakarantar, ajin mu d’aya da Naseer, ganin yana da kok’ari yasa muke kulashi, munso mu jawoshi cikin mu amma yaki amincewa domin yanayin mu da nashi ba d’aya bane, abokinsa d’aya Munnir. Ganin yaki bamu had’in kai yasa muka kyaleshi amma duk da haka muna gaisawa.
Zuwan mu aji shidda Fawwaz ya k’ara zama tantiri, wani abun ma muna tsawatar masa amma duk da haka sai abinda yaga dama, akwai wata yarinya *Minal* aji biyar take alokacin, Fawwaz yana matuk’ar sonta, sai dai ita bashi take so ba, wani d’an ajin mu take so *Farouk*, Fawwaz ya dad’e yana jama Farouk kunne akan ya rabu da Minal amma yayi banza dashi, saboda shima akwai zuciya.
Ganin abun ya fara koma masu fad’a yasa muka fara bama Fawwaz hakuri akan ya rabu da ita ya nemi wata, amma yace bazai hakura ba.
Wata rana da yamma zamu tafi gida yaga Minal da Farouk suna zaune suna shan lemu, takawa yayi har inda suke, yana zuwa ya kwashe Farouk da mari, cikin zafin nama Farouk ya rama, yana marinsa Minal ta k’ara masa hada juye masa lemu a jiki.
Saurin rik’e Fawwaz mukayi gudun kada abun yayi tsamari, duk yanda yaso mu sakeshi kiyawa mukayi, haka muka turashi mota naja muka tafi gida.
Washe gari koda mukazo makaranta muna zaune sai dai mukaga Fawwaz yana murmushi yana sakin kwafa, da muka tambayeshi lafiya yace bakomai.
Aranar mun tsaya lesson har yamma, bayan mun tashi mukaga Fawwaz ya mik’e ya fita da sauri, juyawar da mukayi sai mukaga ashe Farouk ne ya fita zuwa bayan aji da alama band’aki zaije, har mun zauna sai kuma muka tashi muka bi bayansu.
Kafin mu k’arasa muka hangosu suna fad’a, kasancewar wajen babu mutane yasa babu wanda yagansu, da sauri muka nufesu, sai dai kafin mu isa Fawwaz ya zaro wuk’a ya yankar masa wuya nan take ya zube.
Cike da firgici muka isa tare da rik’e Fawwaz, muna dubawa mukaga Farouk baya numfashi, cike da tashin hankali na fige wuk’ar naje na sata cikin wani k’aton rami da ake kona bola, dawowa nayi mukaja Fawwaz muka wuce, sai dai alokacin naga Naseer ya juya baya da gudu ya bar wajen yana kok’arin maida wayarsa aljihu, tabbas ko ba’a fad’a ba nasan ya d’auki abinda ya faru.
Sai alokacin shima hankalinsa ya tashi. Kuka yasa yana fad’in shima kashe shi za’ayi, lallashinsa muka farayi muna fad’in bazamu bari kowa yasan shine ya kashe shi ba, saboda muna son junan mu.
Kai tsaye gidansu muka nufa, wajen Dadynshi mukaje, bayan daya gama jin abinda ya faru na d’auka zai shiga tashin hankali ko kuma yayi ma Fawwaz fad’a amma sai naga cikin ko in kula ya kamo kafad’ar Fawwaz yana shafa kanshi yana fad’in Auta ka kwantar da hankalin ka, meye zaka tashi hankalin ka dan d’an wannan abun, ka d’auka kwananshi ne ya k’are, dan haka ba kaine ka kashe shi ba tsautsayi ne ya kai wuk’ar hannunka wuyanshi, amma babu mai kashe wani sai Allah, dan haka ka kwantar da hankalin ka kacigaba da hidimar ka tamkar yau aka haife ka, bana so ka nuna damuwa, ina fatan babu wanda ya ganku? Suka amsa mashi da babu. Saurin kallonshi nayi nace masa naga wani abokin mu Naseer ina tunanin ya d’auki abinda ya faru kuma ya gani da idonshi dan naganshi yana maida waya aljihu.
Jinjina kai yayi yana fad’in nine Alkalin babbar kotu, kome na fad’a ya zauna, ko case d’in yaron baza’a kaishi kotu ba bare aje afara bincike, zakuce na fad’a maku babu wanda zai tada maganar kawai gawar yaron za’a d’auka a rufe Iyayenshi suyi hakuri, dan haka kuje kawai, shima waccan yaron zansan yanda zanyi dashi.
Kud’i ya bamu masu yawa yana fad’in kuje kusayi wani abu. Anan take Fawwaz ya warware, ni kuwa jikina ne yayi sanyi sosai, ba dan ina son Fawwaz ba babu abinda zai hana na rabu dashi, amma amintakar mu daban take. Haka na wuce gida jiki a sanyaye, aranar da zazzab’i na kwana.
Washe gari haka mukaje makaranta abun mamaki babu wanda yaje da sunan bincike, sai nake jin labarin wai an tsinci gawar Farouk a bayan gari an yankashi, koda na tambaya a ina nayi tunanin za’ace a makaranta amma babu wanda yace haka, abun ya bani mamaki, nan Fawwaz yake rad’a mana ai Dadynshi ne yayi komai, muna tafiya yayi magana da shugaban makarantar akaje inda gawar take aka fita da ita ba tare da kowa ya sani ba, wannan dalilin ne yasa babu wanda yasan a cikin makarantar aka kashe shi, sai dai aka buga ajarida amma Iyayenshi basu tada maganar ba saboda basu san wanda zasu tuhuma ba.
A ranar mun dawo daga yawo mukazo gidansu Fawwaz kawai muka iske Dadyn Fawwaz yayi bak’i, anan aka kiramu, Brr. Barau shine wanda ya tambaye mu kwatancen gidan su Naseer tare da hotonshi, bayan mun bashi ya sake ja mana kunne akan kada mu fadama kowa, nan muka jaddada masu babu wanda zamu fad’amawa.
Kafin mu wuce naji yana waya da wasu yana fad’a masu kada su bar Naseer, su amso abinda ya d’auka kuma su kashe shi. A lokacin nashiga firgici jin za’a kashe Naseer, tun daga lokacin naji Fawwaz ya fice mun arai, nayi danasanin tarayyar mu, haka na wuce gida.
Washe gari sai labarin mutuwar Naseer naji, tun daga lokacin zuciyata ta tsinke, haka kuma tarayyata da Fawwaz tayi baya, Allah yaso zamu fara jarabawa babu sauran zama amakaranta, hakan yasa ban cika shiga cikinsu ba, bayan mun kammala jarabawa aka fitar da Fawwaz waje, tun daga nan muka rabu sai dai waya.
Shigata makaranta a hankali halayyata ta canza, a hankali na rika shiga damuwa saboda abubuwan da suka faru sun kasa barin zuciyata, shiyasa har yanzu ban mance abinda ya faru ba, duk da an d’auki shekaru na kasa manta koda kalma d’aya ce, wani lokacin inajin kamar ina da laifi, domin nayi tarayya wajen b’oye mai laifi, kuma nine silar tona Naseer, domin nine na fad’a ya gammu.
Abinda ya faru da Yaya Sameer da kammala komai har zuwanshi wajena ya fad’a mun Fawwaz ya dawo da abinda yakeso nayi yasa hankalina ya sake tashi, kuma nayi alk’awarin a wannan karon zan tsaya na bada kowace irin sheda ake buk’ata domin a tabbatar da gaskiya, duk abinda ya faru yana nan a zuciyata be goge ba, dan haka ashirye nake domin bada sheda.
Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in tabbas wannan ‘Yallab’ai d’in da muke nema ina kyautata zaton tsohon Alkali ne wato mahaifin Fawwaz, domin alokacin da sukaje gidansu Fawwaz su ukku sun had’u, kunga kenan shine na hud’unsu.
Rafeek yace babu tantama shine na cikon hud’unsu, kuma dole zamu tabbatar da abinda zai tona asirinsu, ayanzu mu kad’ai ne mukasan gaskiya, kuma mu dukan mu babu wanda yake da tsinken da zai iya rik’ewa a matsayin hujja, kotu bata amfani da hujjar baki, ko shari’ar muka dawo da ita baya sune zasu sake nasara domin sune masu hujja mai kwari, dan haka ba yanzu zamu tado da maganar ba.