ALKALI NE Page 61 to 70

Matsowa Rafeek yayi yana had’a hannu, magiya zai fara mata ta daka masa tsawa dole tasa yayi shiru. Girgiza kai Baffa yayi yana fad’in shiyasa jikina be bani ba kaji nayi maka wannan tambayar, yanzu Rafeek so kake kaima mu rasaka kamar yanda muka rasa Naseer? Allah ya fimu sanin wad’an da suka aikata masa haka ka barsu dashi zeyi maganinsu, idan ma ka shigar da k’ara inaso kaje ka soketa, domin babu wanda zai sani shiga kotu, ko kai babu inda zakaje.
Hawaye ne suka zuboma Rafeek, kai yashiga girgizawa yana fad’in dan Allah Baffa ku saurare ni, wallahi ba saboda Naseer zanyi wannan abun ba, inaso a tabbatar da gaskiya shiyasa na fara sako maganarshi amma…. Tashi kabar gidan nan Rafeek, kuma kada ka sake shigowa matuk’ar da wannan maganar zaka zo. Umma ta fad’a cikin dakiya.
Kallon Baffa yayi yana hawaye. Kai ya jinjina masa hakan yasa ya fice yana share hawayen idonshi, yanzu ya zeyi dasu Ra’eez, duk wani sa ransu akanshi ne, sai da komai yazo k’arshe za’a hanashi.
Wayarsa ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Ra’eez, saurin seta kanshi yayi kafin ya d’auka. Bayan sun gaisa Ra’eez yace Yaya mun gama rubuta k’arar da za’a shigar, zan kawo maka kagani zuwa gobe juma’a sai ashigar da ita zuwa litinin ashiga kotu.
Runtse ido yayi cikin k’arfin hali yace Ra’eez kai da Jabeer ina so anjima kuzo inaso muje wajen su Baffa ne. Ra’eez yace Yaya kamar akwai matsala ko? Murmushi yayi yana fad’in bakomai kawai kuzo. Jiki a sanyaye Ra’eez yace Allah ya kaimu.
Kashe wayar yayi yana goge hawayen idonshi, dole ya sako su Ra’eez a wannan maganar idan ba haka ba Umma bazata tab’a amincewa ayi shari’ar ba, shi kuma yana so kowa yasan cewar ba Abbun Ra’eez kad’ai suka kashe ba, yafiso kowa yasan yanda suka aikata mugayen abubuwa. Motarshi ya nufa ya bar gidan.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣9⃣
Guiwa biyu Ra’eez yasa a k’asa ya had’e hannuwansa biyu yayin da hawaye suke ambaliya a idonshi, matsawa kusa da Baffa yayi bayan daya gama basu labarinshi, cikin kuka mai tab’a zuciya da raunanniyar murya yake fad’in Baffa na roke ku da girman Allah ku bar Yaya ya tayani wannan yakin, zuciyata tana da rauni, Allah shine yasan hakan shiyasa ya had’ani da Yaya tare da Jabeer, tabbas Yaya jigo ne agareni, shid’in tsani ne wanda zai taimaka mani zuwa ga kai matakin da nake fatan kaiwa da dad’ewa, matuk’ar kuka janyeshi acikin wannan shari’ar nasan zuciyata zata raunana, duk wani sa rai da nake dashi zan rasa shi, na amince a janye shari’ar Naseer amma dan Allah ku bar Yaya ya tayani kwatoma Ummu na hakkinta ko hakan zai zamo silar samun lafiyarta.
Shiru yayi yana wani irin kuka mai ban tausayi. Gaba d’aya falon shiru yayi babu wanda baya kuka, duk dauriya irin ta Baffa sai da ya zubar da kwalla.
Umma ce tayi saurin kamo hannun Ra’eez tana share masa hawaye yayin da nata suke zubowa. Girgiza kai tayi tana fad’in ban tab’a jin labarin daya tab’a zuciyata irin naka ba, ya isa kadena kuka, daga yau ka zama ‘Dah na, haka zalika ga Baffansu nan ya zam mahaifinka. Kallon Rafeek tayi tana fad’in na amince maka ka tayashi tabbatar da gaskiya, shari’ar Naseer kuma baza’a fasata ba, kushigar da k’aran aranar litinin za’ayita.
Tabbas ayanzu bazan yafema kaina ba idan naki amincewa ayi wannan shari’ar, dan haka na amince maka. Runtse ido Rafeek yayi hawayen farin ciki suna zubo masa.
Murmushi Jabeer ya saki yana rungume Rafeek. Hannu Baffa yasa yana goge idonshi yace tabbas duniya babu gaskiya, ashe dama wad’an nan azzaluman sune sukayi silar mutuwar Mahaifinka? Tabbas nasan mahaifinka mutum ne mai gaskiya, duk da bani da alak’a dashi amma zuwanshi ya samar mana kwanciyar hankali, duk wasu masu shigo da haramtattun kaya sai da yayi maganin su, lallai barin irin su Alhaji Barau a duniya babbar illa ne, dan haka nima na amince a tabbar da wannan shari’a.
Gaba d’ayansu farin ciki ya rufeso haka suka shiga yi masu godiya. Umma tace babu komai Allah yayi maku albarka, kuma yayi maku jagora akan wannan aiki da zaku fara, insha Allahu sai naga yanda k’arshen azzalumai zai kasance.
Bayan sun fito Rafeek ya kallesu yana fad’in yanzu kam hankalina ya kawanta, shiyasa dama nace kuzo nasan zuwan ku ne kad’ai zaisa su Baffa su amince dani, dan haka Ra’eez akai wannan takardar kotu, nasan kana da basira ina so kasan yanda zakayi magana.
Ra’eez yace insha Allahu. Sallama sukayi mashi suka wuce cike da farin ciki. Kai tsaye gidan su Jabeer suka wuce, acan suka ci abinci, sai da suka zauna suka huta kafin suka wuce gidan su Rumaisa.
*** ****
*Liberty Radio*
‘Yallab’ai barka da zuwa. Kwamishna yace yauwa sannu Rafeek, amun afuwa aiki yamun yawa shiyasa ban samu zuwa da wuri ba hakan yasa na kira ka nace sai da dare zan samu shigowa.
Murmushi Rafeek yayi yana fad’in har na cire ran zaka zo, dama aikin dare nakeyi yau shiyasa tunda nashigo da safe naga baka zo ba kawai na fita sai kuma ga kiranka.
Gyara zama yayi yana fad’in ai bana son karya alk’awari, shiyasa nace maka sai zuwa dare nasan lokacin na samu saukin aikin. Rafeek yace barka da zuwa, ruwa ya aje masa tare da zubawa.
Amsa yayi yana fad’in nagode. Bayan ya shanye ya kalli Rafeek yana fad’in sai mu fara kada na samu wani kiran. Murmushi Rafeek yayi ya tashi yana fad’in bismilla dama kafin kazo mun shirya komai.
‘Yallab’ai gidan redion mu yana maka barka da zuwa.
Murmushi Kwamishna yayi yana fad’in yauwa barka dai.
Rafeek.. Jama masu sauraron mu barkan mu da sake had’uwa a wannan gidan redion namu mai albarka, ayau muna da babban bako wanda ya kawo mana ziyara kuma zamuyi fira dashi, mai sauraro idan kana biye damu zakuji sunan bakon namu da kuma yanda firar tamu zata kasance, kubiyomu a cikin shirin namu.
To ‘Yallab’ai mutane zasu so suji cikekken sunan ka da kuma irin matakin da kake ayanzu saboda kowa ya sheda ka.
E to, ni dai sunana Bello Kabir, kuma nine kwamishnan ‘yan sanda a garin lagos.
‘Yallab’ai nasan kafin ka kawo wannan matsayin kasha gwagwarmaya har zuwa lokacin da Allah ya kawo ka wannan matsayin, ko zaka fad’ama masu sauraron mu irin gwagwarmayar daka sha?
Kwarai kuwa nasha gwagwarmaya kafin nazo wannan matsayi, kuma dama kowa yasani kafin aji dad’i dole sai ansha wuya, kamar yanda kowa ya sani aikin ‘Dansanda aiki ne na jihadi, aiki ne wanda dole sai ka bada k’arfin ka, dukiyar ka da kuma lokacin ka, duk wani d’an sanda yana fuskantar kalubale arayuwarsa, wasu ma suna rasa rayukansu akan wannan aikin, kamar yanda na bada misali da dukiya, tabbas akwai wani abun idan yazo maka dole sai kayi amfani da dukiyar ka kafin kaci nasara akanshi, haka ma lokaci, duk wani d’an sanda beda lokacin kanshi matuk’ar yasa aranshi k’asarshi yakema aiki, wani lokacin koda kana hutu zaka iya samun kira daga sama kuma dole kaje, shiyasa nace maka aikin d’an sanda aiki ne na sadaukarwa, d’an sanda beda lokacin kanshi sai lokacin al’umma domin su yake ma aiki, hakki ne ya rataya akanshi dole ne ya bama kowa tsaro, to da haka dai mukayi ta fafatawa da dad’i ba dad’i har Allah ya kawo ni wannan matsayi.