ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 61 to 70

Jinjina kai Rafeek yayi yana fad’in gaskiya dole na sara maka, tabbas aikin d’an sanda babban aiki ne, yakamata mutane su k’ara jinjina ma ‘yan sanda kuma su k’ara basu muhimmanci domin suna da muhimmanci arayuwar mu baki d’aya. 

Kwamishna yace nagode, amma ina ganin mutane kad’an ne suke fahimtar muhimmancin mu, domin kuwa masu zagin mu sunfi yawa. 

Murmushi Rafeek yayi yana fad’in tabbas nasan akwai masu zagin ‘yan sanda da yawa, sai dai kuma wasu suke b’ata wasu, da yawa mutane suna ma ‘yan sanda kallon masu cin hanci da rashawa, wannan bakin fentin har yanzu yaki goguwa a wajensu, kuma wasu ne suka jawo wannan abun, duk yanda kuke aiki matuk’ar ana samun masu k’arb’ar cin hanci to al’umma bazata tab’a ganin muhimmancin ku ba, shiyasa ake son arik’a kamanta gaskiya. 

Kwamishna yace wannan shine babban abinda muke yaki dashi, amma har yanzu an kasa dainawa, saboda mutane suna d’aukar cin hanci shine abinda zai rik’esu. 

Murmushi Rafeek yayi yana fad’in ‘Yallab’ai a matsayin ka na wanda yayi shekaru yana aikin d’an sanda, nasan dole akwai wani babban kalubalen daka fuskanta wanda bazaka iya mantawa dashi ba, ko zaka fad’ama masu sauraron mu irin kalubalen daka fuskanta? 

Kwarai kuwa akwai kalubale da yawa dana fuskanta, kowa yasan idan kana irin aikin mu akwai kalubale sosai akan mu, kuma nasha wahala sosai, amma juriya da jajircewa irin tawa yasa na kawo wannan matsayin. 

Jinjina kai Rafeek yayi yana fad’in duk da lokaci ya fara hararar mu amma zanso ka fad’ama masu sauraron mu a shekarun baya lokacin kana aiki a k’aramin ma’aikaci wane case ne yafi baka wahala kuma ya baka tsoro. 

E to, gaskiya nayi cases da yawa wad’an da bazan iya tunawa da wasu ba, amma ina ganin akwai wani case da na tab’ayi wanda yayi matuk’ar bani wahala da tsoro, idan ban manta ba yau kusan shekaru goma kenan, case ne wanda yake a cukurkud’e hakan yasa nasha wahala kafin na kammala lashi, zan iya cewa a wannan case d’in bayan kammalashi har k’arin matsayi na samu. 

To ‘Yallab’ai tambayata ta k’arshe a wannan shirin ko zaka fad’a mana dalilin zuwanka wannan matakin? 

Gyara zama yayi kafin ya d’auki ruwa yasha yana gyara glass d’in idonshi. Kofin ya aje yana fad’in E to, gaskiya wannan matsayi dana zo zan iya cewa dalilin taimako ne yasa nazoshi, nasan kuma mutanan da suka taimaka mani nazo wannan matsayin har yanzu suna alfahari dani, bazan iya fad’arsu ba domin ba’a son ka fad’i wanda yayi maka alkhairi tunda dan Allah yayi, amma gaskiya har in mutu bazan iya mantawa dasu ba. 

Murmushi Rafeek yayi yana fad’in ‘Yallab’ai kayi mana halin ku na ‘yan sanda, domin baka fito fili ka fad’a mana silar zuwanka wannan matsayin ba. 

Murmushi Kwamishna yayi yana fad’in wannan kuma sirri ne. Dariya sukasa gaba d’aya. Rafeek yace daga k’arshe wata shawara zaka bama sauran ‘yan sanda.

 E to inaso nayi amfani da wannan damar na k’ara bama sauran yan sanda shawara akan surike gaskiya, dan duk wanda ya rike gaskiya baya tab’ewa, kuma su sani wannan aikin da sukeyi a ciki zasu nemi duniyarsu da lahirar su, Allah yasa mudace amin. 

Juyowa Rafeek yayi yana fad’in to masu sauraron mu anan muka kawo k’arshen wannan shiri na fira da mukayi da Kwamishnan ‘Yan sanda, sai muce mungode Allah yasa aje gida lafiya. 

Kwamishna yace madallah nima nagode, masu saurare ina maku fatan Alkhairi. 

**** 

Bayan da Rafeek ya koma gida duk da dare yayi sai da ya tace shirin da ya gabatar ya adanashi dan yasan zeyi masa amfani kafin ya kwanta. 

**** ****

Alhaji ya jikin Alhaji Marusan? Jiki da sauki za’ace, amma fa yana can yana jin jiki. Momy tace bawan Allah, gaskiya asara bata da dad’i dole yashiga wannan halin, amma ai zaku taimaka masa da wani abun ko zai rage asara ko? Murmushi yayi yana fad’in Hajiya Binta kenan, baki san waye Alhaji Marusa ba, shine fa silar arzikin mu, taya kike tunanin dukiyarsa zata girgiza dan kawai yayi wannan ‘yar asarar, kawai shegen son kud’i gareshi shiyasa yashiga wannan halin, amma babu abinda zamu taimaka masa dashi sai kulawa. 

Jinjina kai tayi tana fad’in to Allah ya kyauta ya kuma tsayar akanshi. Yace amin. Kallonta yayi yana fad’in wai Ra’eez yana zuwa gidan nan kuwa? Girgiza kai tayi tana fad’in rabonsa da gidan nan tunda yazo sukayi sallama da zamuje Dubai, amma tace aiki ne yayi masa yawa shiyasa. 

Murmushi yayi yana fad’in wallahi na kosa naga Raheena a gidan miji nima ko na samu jika. Momy tace lokacin zai zo, ai anyi mewuyar tunda ta samu mijin aure, Allah dai ya bashi ikon kammala wannan aikin lafiya. Alhaji Barau yace amin ya Allah. ????

**** ****

Wajen k’arfe goma na safe Ra’eez ya kwankwasa k’ofar ofis d’in Alhaji Barau dan yaga lokacin da yazo, amsa mashi yayi tare da bashi izini hakan yasa ya tura k’ofar bakinsa d’auke da sallama. 

Amsawa yayi yana fad’in wai Ra’eez kaine shine ka tsaya kwankwasawa? Gaisheshi yayi yana fad’in wallahi kuwa. Kujera ya nuna masa yana tambayarsa k’arfin jiki. 

Ra’eez yace jiki yayi sauki babu abinda yake damuna yanzu. Alhaji Barau yace nima asibiti na biya shiyasa ban shigo da wuri ba, abokina Alhaji Marusa ne beda lafiya wata asara ce ta sameshi tunda yaji hankalinsa ya tashi ya zube shikenan sai ya samu shanyewar b’arin jiki. 

A zabure Ra’eez ya kalleshi yana fad’in Alhaji Marusan? Ido ya tsura mashi kafin ya furta kasanshi ne? Duk’ar da kai Ra’eez yayi yana fad’in a wajenka nasanshi shiyasa naji tausayinsa. 

Murmushi ya saki yana fad’in ai da sauki tunda likita yace jininsa ya sauka saboda har yanzu basu bari ya farka ba, sunfi so sai ya samu hutu zuciyarsa ta natsu sannan, a wajenshi ma na d’an jima saboda babu kowa a gunshi, kasan yaran zamani, akwai babban d’anshi amma saboda be damu dashi ba ko kuma ince shi Alhajin be jawosu ajikinshi suka saba ba shiyasa basu damu dashi ba, ga matarsa taje Dubai sai gobe zata dawo. 

Ra’eez yace Allah ya kyauta. Alhaji Barau yace amin. Kallonshi yayi yana fad’in kamar akwai magana a bakin ka ko? Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in dama jiya bayan mun tashi daga aiki wani yazo ya shigar da k’ara, to case d’in kisa ne, kuma nine suka d’auka amatsayin wanda zai tsaya masu, shine nazo inji ko an kawo maka takardar? 

Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad’in yanzu na shigo gaskiya ban iske takardar komai ba, kila dai ko zuwa anjima, amma case d’in waye? Ra’eez yace e to, gaskiya tsohon case ne, dan abun ya dad’e za’ayi kusan shekaru sha biyu da faruwar abun, to alokacin basu da shedar da zasu gabatar ma kotu shiyasa sukayi hak’uri, amma ayanzu sun samu duk wata sheda shiyasa suke so ayi shari’ar. 

Tsaki Alhaji Barau yayi yana fad’in kaji wani shirme, ko sababbin cases nawa muke dasu duk basu ishemu ba sai an koma shekarun baya an d’auko mana wata tsohuwar shari’a saboda kawai an maida kotu wajen wasan yara, yanzu haka ko anyi shari’ar bance shedarsu zata wadatar ba, saboda na tabbata da wuya a samu wanda yayi kisan araye, idan ko an sameshi to wasu shedun basa nan, gaskiya banji dad’i daka amshi wannan case d’in ba, kawai ka turasu k’aramar kotu. 

Gyara zama Ra’eez yayi yana fad’in Alhaji a taimaka masu, kasan kowa yana alfahari da wannan kotun, ba kowa bane kuma yake jawo mata farin jini sai kai, yau idan babu kai a wajennan nasan ba kowa ne zaiso ya kawo shari’arsa nan ba, domin kaine hasken da yake haske kotun, duk wasu mutane da suke zarya nan saboda kai suke zuwa, idan sukaji kayi fatali da case d’insu zaka sare masu sa ran da suke dashi, domin idan basu samu adalci a wajen ka ba sun san babu inda zasuje a amshe su. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button