ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 61 to 70

Murmushi Alhaji Barau yayi yana gyara zaman glass d’inshi yace wannan haka yake, nagode daka tunatar dani, shiyasa nake jin dad’in kasancewar ka akusa dani, domin wani lokacin nakan so na kwafsa amma sai ka maidoni hanya, gaskiya Ra’eez kai d’in na daban ne, shikenan kashirya tsaya masu zuwa litinin za’a fara shari’ar, kuma insha Allahu zan sama masu adalci kodan ta silarka. 

Turo k’ofar ofis d’in akayi had’e da sallama, amsawa sukayi kafin ya shigo. Alhaji Barau yace Malan Jamilu yau ka makara ko? Wanda aka kira da Malan Jamilu yace wallahi iyalina ne basuji dad’i ba sai da mukaje asibiti amma da sauki. 

Alhaji Barau yace Allah ya basu lafiya, ai bazaka zauna ba dama yau juma’a sa hannu kawai ka tafi. Mik’a masa takarda yayi yana fad’in jiya aka kawota lokacin ka tafi shiyasa na ajeta, takardar… Katseshi yayi yana fad’in Ra’eez yayi mani bayani, amsa yayi yana fad’in zaka iya tafiya. 

Godiya yayi mashi Ra’eez ya gaishe shi yana masa ya mai jiki. Kud’i Alhaji Barau ya bashi yana fad’in ga wannan ka siya mata magani. Godiya yayi mashi ya fita yana mamakin yau Alhaji Barau yayi masa kyauta. (Niko nace agaban suriki ai dole yayi gwaninta????) 

Tashi Ra’eez yayi yana fad’in zan koma nagode Alhaji. Murmushi yayi yana fad’in babu damuwa Allah ya bada sa’a, idan kana da wata matsala kazo ka fad’a mani, domin bazan bari ka fad’i ba. Godiya yayi masa ya fice. 

****

Dariya sosai Jabeer yayi jin yanda Ra’eez yayi da Alhaji Barau. Tsaki Ra’eez yayi yana fad’in wallahi wannan mutumin beda kunya, amma ka kyaleshi na kusa koya masa yanda akejin kunya. 

Jabeer yace gashi kuwa hada maka addu’ar neman sa’a besan akanshi zata k’are ba. Ra’eez yace ai d’azu munyi waya da Yaya yace ayau zai sanar da shari’ar dan yana so tayi mutane. 

Jabeer yace kasan kuwa duk wanda yaji za’ayi shari’ar shekaru da yawa dole yazo yaji yanda zata kaya, ni kaina ina so litinin tayi kawai naji yanda za’a fafata. 

Ra’eez yace wallahi ni kaina nakosa akammala komai kona samu natsuwa, gaba d’aya bani da lokacin kaina, Pretty hak’uri kawai take dani damma muna d’an waya. 

Jabeer yace ai komai ya kusa zuwa k’arshe da izinin Allah. Waya Ra’eez ya d’auka yana fad’in bara naji muryarta ko naji kwarin yin aikin dan gaskiya yau dole na tsaya fira. 

Murmushi Jabeer yayi ya mik’e yana fad’in nayi nan kada naji kayan haushi. Ra’eez yace idan kaji haushi gobe na ganka da budurwa. Jabeer yace kai dai kasa ido Allah ya kusa kawota. 

Maganar da yaji yasa ya maida hankalinsa ga wayar. Jabeer kuwa ficewa yayi yana masu dariya. Bayan ta gaishe shi yace Prettyna ki k’ara hakuri kinji, ni kaina ina kewar ki da yawa. 

Murmushi tayi tana fad’in haba bakomai, ai wannan aikin da kakeyi mu kake mawa, dan haka ina nan ina jiranka kuma ina maka addu’a nasan zakayi nasara. Ra’eez yace nagode sosai ina so yau kimun kwalliya kamar zakije party dan yau fira zamuyi. 

Murmushi tayi tace shikenan yanda kace, sai kazo. Ra’eez yace me zan taho maki dashi? Duk abinda yayi maka ta fad’a cike da farin ciki dan tayi kewarsa, kwana biyu koya zo baya dad’ewa shima da Mama kawai suke gaisawa. 

Ra’eez yace shikenan sai nazo ki gaishe da Abdallah da Mama. Zasuji ta fad’a. Kiss yayi mata yana fad’in miss u, da sauri ta kashe wayar. Dariya yayi yana fad’in zan kamaki ne. 

**** ***

Tsaki Fawwaz yaja a karo na ba adadi, zaune yake a cikin lambun gidansu, yau kwana biyu kenan ya kasa samun nutsuwa, tunda Adnan yayi masa maganar Farouk shikenan hankalinsa yaki kwanciya, duk yanda yaso ya cire abun aranshi ya kasa, gashi baya so ya fad’ama Dad d’insa hankalinshi ya tashi, gara kawai yayi shiru ya magance matsalar da kanshi. 

Kashe sigarin daya gama sha yayi yana kurb’ar giyar da ya zuba a kofi, a ‘yan kwanakin nan ko wajen abokansa baya zuwa saboda damuwa, shaye-shayenshi ya k’aru ko zai samu sauki amma abanza. 

Waya ya d’auka ya kira babban abokinsa, yana d’agawa yace *Milo* mu had’u a gidan shakatawa ta akwai maganar da zamuyi, amma kazo kai d’aya. Shikenan sai kazo

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

4⃣0⃣

What? Dude kasan abinda kake fad’a kuwa? Kai Fawwaz ya jinjina yana zuk’ar sigari. Gyara zama Milo yayi yana fad’in lallai kai babba ne Dude, haba shiyasa baka da tsoro ashe tuni tsoron ya bar zuciyar ka, ai duk mutumin da zai iya aikata kisan kai bana tunanin yana da tsoro a ranshi, ka ganni nan ko fad’a bana so saboda nasan yanda halin maza yake akwai bak’ar zuciya, da an fara fad’a yanzu zakaji an yanki wani ko an fitar masa da jini, wannan dalilin ne yasa bana son zama a club. 

Tsaki Fawwaz yayi yana fad’in kada ka bani kunya mana Milo, ina tunanin na kawo kuka gidan mutuwa sai kazo mani da wannan banzar maganar. 

Gaskiya na fad’a maka ai, Milo ya fad’a yana kunna sigari. Ajiyar zuciya Fawwaz yayi yana fad’in wallahi tsoro nakeji kada Adnan ya tona abinda ya faru. 

Murmushi Milo yayi yana fad’in haba kada ka bani kunya, kada kamanta Dadyn ka shine tsohon Alkalin babbar kotu, duk da ya aje aiki har yanzu yana fad’a kuma anaji, sannan kace abun ya faru tun kuna secondary banga dalilin da zaisa ka damu kan ka ba, shima Adnan d’in cewa yayi kawai ya tuna maka ne bawai zai tona asiri yake nufi ba, kaga idan har zaka saka damuwa aranka ina tabbatar maka kaine zaka tona kan ka, kawai ka share kacigaba da chilling. 

Dariya Fawwaz yasa yana fad’in shiyasa nake sonka abokina, amma wallahi kwana biyu bana baccin kirki. Hannu Milo yasa aljihu yana fad’in ina zuwa, ai nine mai bada maganin bacci, ina tabbatar maka daga yau ka dena rashin bacci. 

Mik’a masa yayi yana fad’in kaga wannan kwayar ita ake kira da ‘yar hutu, nima wani abokina ne ya bani ita d’an gidan Alhaji Marusa. 

Fawwaz yace ba dai Marwan ba? Shifa, ai kasan Gayen yasan ta kan kayan hutu, shiyasa fa kaga muna d’asawa dashi dan baya harka da kayan Nija dan basu da inganci, jiya mukayi waya dashi yake fad’a mani ranar monday zai koma india kasan baya son zama a Nija. 

Amsa Fawwaz yayi yana fad’in ai gaskiya Marwan babba ne, shiyasa nima banso su Dad sukace na dawo ba, acan hankalin mu kwance sai abinda mutum yaga damaryi. 

Milo yace tashi muje Beb d’ina tana jirana d’azu tazo mani week end. Fawwaz yace ai kai kaji dad’inka tunda an ware maka gidanka, ni kuwa basa bari na kwana a wani waje duk da an mallaka mani gida. 

Tashi Milo yayi yana fad’in ba sai karik’a wuni anan ba wayasan abinda kakeyi, iyaka sai lokacin bacci yayi ka koma. Fawwaz yace ka kawo shawara haka za’ayi, nagode abokina. 

**** ****

Wai Marwan ba magana nake maka ba. Baki ya turo yana fad’in wai meyasa kike son takura mani Mom, ko dan kinga ina zuwa ganin ku, shi *Khalil* da baya zuwa ai bakiyi masa haka. 

Hannunshi ta kamo tana fad’in yi hakuri ba takura maka nakeyi ba, naji kace mun Alhaji beda lafiya kuma kana maganar zaka tafi bayan kasan yanzu ne Alhaji yake da buk’atar ka tunda kaga halin da yake ciki, ni dai mace ce bazan iya jinyarsa ba, gashi ba wani d’an uwa gareshi ba da an kirashi, dole kaine babba kai zaka tsaya ka kula dashi. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button