ALKALI NE Page 61 to 70

Saurin kallonta yayi yana fad’in wallahi Mom bazai yuwu ba, shikenan abubuwan da nake dasu acan sai na hakura dasu, Dad fa yana da kud’i, idan kana da kud’i babu abinda zai gagareka, shi kanshi likitan yace zasu kula dashi tunda akwai kud’inshi da yawa a account d’insu, dan haka ni bazan iya jinya ba.
Kai ta jinjina tana fad’in shikenan dena fushin, tunda akwai kud’in za’a samu masu kula dashi, nima ba zama zanje inyi ba saboda kasuwancina, amma zan rik’a lek’awa, kaga yanzu asara ta sameshi idan ban tsaya na kula da tawa dukiyar ba sai nima nabi sahunsa dan shi tsufa ya taho masa ga mutuwar b’arin jiki ai kaga beda sauran amfanuwa matuk’ar be warke ba, yanzu haka kayan dana saro suna hanya jiransu ma nakeyi kafin na lek’a asibitin tunda kace allurar bacci sukayi masa.
Tashi yayi yana fad’in zan fita ni. Kallonshi tayi tana fad’in amma Marwan akwatin da naga ka d’auko a d’akin Alhaji na meye? Fuska ya d’aure yana fad’in amma ai ina da gadonshi ko? Kai ta d’aga, kauda kai yayi yana fad’in amfani zanyi dasu to.
Be jira amsarta ba yayi waje. Murmushi tayi tana fad’in Marwan manya, da Alhajin yana nan zai baka wad’an da sukafi haka ma. Wayarta ce tayi k’ara hakan yasa tayi saurin d’auka ganin wanda ya kira.
A zabure ta mik’e tana fad’in ban gane ba, ka bincinka jirgin da akace ya nutse kuwa? Shiru tayi tana sauraronshi. Salati tasa hawaye suka fara wanke mata fuska, hakuri ya bata ya kashe wayar.
Zaman ‘yan bori tayi tana kwara ihu, da sauri masu aikin gidan suka fito jin Hajiya na ihu. Kuka suka isketa tanayi kamar k’aramar yarinya, nan suka shiga bata hakuri amma kamar izata sukeyi.
**** ****
Ido kawai Alhaji Marusa ya tsura ma Matarsa da take zaune a gefenshi tana share hawaye, Alhaji Barau da Mr. Kallah sai hakuri suke bata jin asarar data sameta.
Alhaji Barau yace Hajiya hakuri zakiyi, kinga yanayin da yake ciki be kamata arik’a tada masa hankali ba, addu’a zakiyi Allah ya maido maki da wasu kud’in. Goge idonta tayi tana fad’in dole nayi kuka, wannan bala’i kamar wad’anda aka sama hannu, so akeyi asirin mu ya tonu.
Mr. Kallah yace Hajiya sai hakuri, yanzu Alhaji kulawa yake buk’ata dole ki daure ki kula dashi hakan zaisa ya samu k’arfin jikinshi tunda likita yace abun beyi yawa ba za’a iya shawo kan matsalar dan yanzu haka zasu fara mashi gashi kinga idan kina kwantar masa da hankali zaifi saurin warkewa.
Alhaji Barau yace to Allah ya kyauta, Mr. Kallah muje ko. Tashi sukayi suna fad’in Alhaji Allah ya k’ara sauki. Kai ya jinjina masu yana binsu da kallo har suka fita.
Zaune suke a mota suna kwasar dariya. Mr. Kallah yace gaskiya na tausaya masu, ga Hajiya itama asara ta sameta, gashi a kwance ko magana baya iyawa, gaskiya da munsan haka zata faru dashi da bamu aikata masa haka ba.
Alhaji Barau yace bamuda laifi, son kud’inshi ne ya jawo masa haka, ita kuma Hajiya kila zakkace aka fitar mata, itama son kud’in gareta ai, kasan kuwa yanda take cin kud’in Alhaji ita da ‘Ya’Yanta, ga satar da suke masa, ai alhakinsa ne ya kamata.
Mr. Kallah yace duk da haka ya kamata mu tausaya mashi a fitar dashi waje sai kaga cikin kwana ukku ya tashi amma zafin zeyi masa yawa, gaskiya ko bazaka taimaka ba ni zansa afitar dashi. Ganin yanda Mr. Kallah ya dage yasa Alhaji Barau ya amince.
Fita sukayi zuwa ofis d’in likita, anan suka masa bayani, nan take ya kira wani abokinsa a America, babu b’ata lokaci suka gama komai, inda za’a tafi dashi gobe saboda litinin a fara masa magani.
Sallama sukayi masa suka wuce domin nema masa Visa, dole da Mr. Kallah zasu tafi tunda Marwan yace bazeyi jinya ba. Kasancewarsu manya nan take suka samu jirgin safe na gobe, haka suka rabu.
**** ****
Washe gari tunda safe jirginsu ya d’aga, Hajiya taso ta bisu dan bata jin dad’in zaman gidan, wayar data samu daga Yaronta zai zo yasa ta fasa binsu asalima taji dad’in tafiyar tunda zata sake wannan karon a gida zasuyi sha’aninsu ba sai taje gidanta da suka saba had’uwa ba tunda Marwan ma yau ya tafi.
**** ***
Duk wani shirin shiga kotu sun kammalashi, duk inda kaje zakaji ana maganar shari’ar da za’ayi gobe, mutane da yawa suna son suje suji wace irin shari’ace haka bayan shekaru masu yawa kuma za’a maidota baya.
Wajen k’arfe sha biyu su Alhaji Mansur da Matarsa suka sauka lagos, Ra’eez da Jabeer suka d’aukosu, kai tsaye gidan Mama suka kaisu inda Alhaji Mansur zai zauna a gidan Ra’eez.
Sosai Mama tayi farin ciki da zuwan su, Rumaisa ta kawo masu abincin da zob’o. Zama sukayi aka gama gaisawa kafin suka ci abinci, haka suka cigaba da tattaunawa.
Da yamma Alhaji Mansur da su Ra’eez suka nufi wajen Kawu tare dasu Jabeer. Sosai Kawu yayi farin cikin ganinsu. Haka suka zauna suna ta fira. Alhaji Mansur yace sunyi waya da Abubakar yace da zaran za’a fara gabatar da shari’ar su Malan Sani zai zo.
Murmushi Kawu yayi yana fad’in wallahi jinake kamar mafarki, bani da abun roko daya wuce Allah ya nuna mani ranar da zan fita daga wajen nan, ranar da zanga lokacin da za’a tona asirin munafukai.
Ra’eez yace ai Alhaji Marusa da Mr. Kallah suna America. Alhaji Mansur yace akan ciwon Alhaji Marusan ne? Ra’eez yace wallahi kuwa, nima d’azu Alhaji Barau yake fad’a mani.
Alhaji Mansur yace ina rokon Allah ya bashi lafiya domin ya amshi hukuncinsa, bakomai nasan bazasu dad’e ba tunda kace jikin da sauki, kafin a kammala wannan shari’ar zasu dawo da izinin Allah.
Wayar Ra’eez ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Dr. Saddek ne, d’agawa yayi, bayan sun gaisa Dr,
yace masa yazo yana son ganinshi. Ra’eez yace gani nan zuwa.
Kashe wayar yayi yana fad’a masu abinda Dr, yace. Alhaji Mansur yace ai sai kutashi muje kila wani abunne. Kawu yace aduba mani Hajiyar.
**** ***
Zaune suke a ofis d’in Dr. Saddek, bayan sun gama gaisawa Dr, yace dama akan maganar shari’ar da naji za’a gabatar gobe ne, tunda har shari’ar zata kai zuwa gano abinda ya shafi abinda yayi silar jefa Hajiya wannan halin ina ganin zaku tafi da ita, ina so na gwada wani abu ko Allah zaisa a dace, shiyasa nace bara nakira ka.
Alhaji Mansur yace likita kana ganin babu matsala atafi da ita? Bana so fa Alhaji Barau ya gano wani abu, sannan kada aje garin gyara ayi b’arna, kana gani kwanaki daga fad’in sunanshi yanda tayi, inaga ace ta ganshi kuma ta san shine Brr. Barau d’in.
Likita yace Alhaji jikina yana bani wani abu shiyasa kaji nace aje da ita, kasanfa da yawa irin wannan haukan yana warkewa ne ta silar faruwar wani abu, musamman idan mutum yaga abinda ya tsaya masa arai, ina rokon ka amince aje da ita, idan Allah besa zata warke ba shikenan sai adawo da ita.
Hawaye ne suka zubo ma Ra’eez, kallon likitan yayi yana fad’in koda ace Ummu bazata warke ba ana kammala wannan shari’ar zan tafi da ita, tunda dai haukarta bata duka bace ni zan cigaba da zama da ita ahaka.
Dafashi Alhaji Mansur yayi yana fad’in insha Allahu Ummunka zata warke, bakomai likita zamuyi yanda kace, amma akwai maganin da zaka bata ko? Kai likita ya jinjina yana fad’in zan bata magani, kuma nima zan halarci wajen tare da wasu daga cikin ma’aikatan mu, kuma zamu kula babu abinda zai faru.