ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 61 to 70

Godiya sukayi masa. Sallama sukayi mashi akan gobe zasu taho da ita, sai dai bazasu bari kowa ya gane daga asibiti suka fito ba. Alhaji Mansur yace shikenan mungode, akwai Maman Rumaisa da Hajiya sai su kula da ita goben. 

**** ****

Zaune suke su biyar sai Alhaji Mansur na shida a gidan Ra’eez. Rafeek ne ya kalli Adnan yana fad’in ina fatan ka shirya ma shiga kotu gobe? Jinjina kai Adnan yayi yana fad’in sosai kuwa, domin a wannan karon bazan bari a sake aikata zalunci ba. 

Rafeek yace Nabeel fa? Nabeel yace ashirye nake Yaya, domin nashirya duk yanda zan shawo kan Abbana, dalilin da yasa banyi masa maganar ba bana so yaje masu Alhaji Barau da maganar shiyasa nace sai yau da dare zanje na rokesa akan ya fad’i gaskiya. 

Ra’eez yace lallai da ka kwafsa, ai gara da baka fad’a masa ba, kabarshi idan yaje zaiji komai da kunnansa, abinda nakeso kawai kayi kok’arin sashi yazo kotun domin nasan za’a buk’aci ganinsa. 

Nabeel yace shikenan dana koma gida zansan yanda zan fad’a masa. Rafeek yace insha Allahu babu abinda zai gagara, domin kowa yasan yanda komai ya kasance, shikuwa Fawwaz ku barshi Alkali da kanshi zai bada umarnin a kawoshi. 

Alhaji Mansur yace ni narasa ma bakin magana, agaskiya nayi farin ciki da wannan had’in kan naku, domin taimako ne zakuyi kuma Allah ne kad’ai zai iya biyanku, dan haka idan kowa ya samu dama kafin ya kwanta yayi nafila ta neman nasara, sai kuga Allah ya taimake mu, Allah yayi mana jagora. Gaba d’aya suka amsa da amin. 

**** ****

Abbah ka kalli labaran jiya na Liberty radio kuwa? Abbah yace labaran da yawa ai, wanne a ciki? Gyara zama Nabeel yayi yana fad’in aikuwa agari naji ana ta maganar shari’ar da akace za’ayi gobe a babbar kotu kuma tsohuwar shari’a ce, naji mutane suna fad’in zasuje suyi kallo. 

Abbah yace wai wace irin shari’ace haka bayan shekaru kuma za’a maidota? Nabeel yace gaskiya ban sani ba, amma koma menene nasan babbar shari’arce tunda gashi an maido ta. 

Abbah yace aikuwa nima zanje kodan naji wace shari’ace haka, kasan ina son zuwa saurarar shari’a. Murmushi Nabeel yayi yana fad’in nima nace zanje ai. Abbah yace dama ku ai ba’a barin ku abaya. Murmushi Nabeel yayi yana fad’in ai bana son naga anyi zalunci Abbah. Abbah yace to Allah ya bama masu gaskiya sa’a. Nabeel yace amin. 

***** *****

*Safiyar litinin a Kotu*

Cike babbar kotu take da mutane, yayin da su Mama da Maman Labiba, Rumaisa sai Ummun Ra’eez da matar da take kula da ita suke zaune a cikin kotun, saboda dawuri sukazo dan kada su rasa wajen zama, sannan basa son sai an shiga su shiga gudun kada Ummu tayi wani abun, duk da jikinta amace yake tun maganin data sha. 

A hankali mutane suka shige ciki kowa ya zauna ana jiran zuwan Alkali. Shigowar Alkali yasa kowa ya mik’e, bayan ya zauna kowa ya zauna. 

Shiru kotun tayi ana jiran a fara. Bayan ya kammala abinda yake Magatakarda ya tashi domin ya karanto shari’ar da za’a gabatar. 

   *A yau litinin biyar ga watan december shekera ta dubu biyu da shatara wannan kotu zata saurari k’arar da Iyalan Alhaji Sambo Jarmai suka shigar akan kissan gillan da akayima ‘Dansu a shekarar dubu biyu da takwas, wanda aka tsinci gawarsa a ranar juma’a da misalin k’arfe tara da rabi na dare, suna rokon wannan kotu mai albarka data kwato masu hakkinsu.*

Mika takardar yayi ya koma ya zauna. Gyara zama Alkali yayi yana fad’in ina lauyoyin da zasu fabatar da shari’ar? Tashi Ra’eez yayi yana fad’in ya mai shari’a nine lauyen da zai k’are wad’anda suke k’ara. 

Jinjina kai Alkali yayi yana fad’in zaka iya farawa. 

Fitowa Ra’eez yayi yana fad’in Iyalan Alhaji Sambo Jarmai sun shigar da wannan k’ara ne saboda suna da yakinin a wannan kotun ne kad’ai za’a iya kwato masu hakkin su, duk da wannan case ya dad’e amma dalilin rashin kwakkwarar sheda yasa basu shigar da k’ara ba, haka zalika basu shigar da k’ara a ofishin ‘yan sanda ba, sai dai kuma alokacin da abun ya faru akwai shedar sa hannu ta ‘yansanda a wancan lokacin, wannan shine rahoton da muka samu a ofishin ‘yan sandan da suka kula dashi a wancan lokacin. 

Amsar takardar Magatakarda yayi ya mik’a ma Alkali. Ra’eez yace a shekarun baya an tsinci gawar Naseer Sambo Jarmai a wajen gari da misalin k’arfe tara da rabi na dare, kuma ‘yan sanda ne suka d’auki gawarshi suka mik’ata asibiti, a lokacin inspector Musa shine wanda ya kula da wannan gawa harya d’auketa zuwa asibiti inda ya mik’a case d’in ga abokin aikinsa Inspector Bello Kabir wato Kwamishnan ‘yan sanda na yanzu, inaso kotu ta bani dama na kira Alhaji Musa domin muji bayani daga bakinsa. Kotu tana buk’atar Alhaji Musa. 

Ra’eez…. Kotu zata so taji sunanka da kuma aikin ka. 

Sunana Alhaji Musa Adam, nayi aikin d’ansanda a shekarun baya, amma ayanzu na aje aiki tun shekaru biyar da suka wuce, ayanzu haka ina kasuwanci ne. 

Ra’eez… Alhaji Musa ko zaka iya tuna abinda ya faru a shekarar dubu biyu da takwas akan gawar da kuka tsinta ta Naseer Sambo Jarmai? Muna so kayima kotu cikekken bayani. 

Alhaji Musa…. Kwarai kuwa zan iya tuna wannan case d’in, domin bashi kad’ai muka samu a wannan dare ba, kuma wannan lokacin yana d’aya daga cikin abinda bazan iya mantawa ba, domin a wannan shekarar a wannan kotun anyi zazzafar shari’a, wanda d’aya daga cikin gawar da muka tsinta had’e data Naseer ce akayi shari’a akanta, sai dai ita ta Naseer Iyayenshi basu buk’aci yin shari’a ba, saboda babu wata sheda da muka samu a lokacin da muka tsinceshi. 

A wannan dare na juma’a mun samu waya cewar an samu gawar tsohon shugaban kwastam wato Alhaji Maiwada, bayan da ‘Yallab’ai Bello ya tura mu wajen, da muka d’auko gawarsa mun taho muka sake samun labarin gawar da wasu suka gani, haka muka wuce muka d’auko gawar Naseer, kai tsaye asibiti muka nufa dasu, daga can kuma case d’in ya koma hannun Ogana wato ‘Yallab’ai Bello Kabir, iya abinda na sani kenan akan gawar Naseer, sai rahoton dana baka wanda nine na rubutashi da hannuna. 

Ra’eez… Mungode Alhaji Musa zaka iya tafiya. Ya mai shari’a wannan shine d’an sandan daya d’auki gawar Naseer, ga rahoton mutuwarsa nan, sai dai a binciken da mukayi mungano Naseer yana aji shidda ne a makarantar Kings college a wancan lokacin, kafin mutuwarsa akwai abinda ya faru a makarantar su wanda akan idonshi abun ya faru, yayi kok’arin ya tabbatar da gaskiya sai dai silar wannan abun ya jawo mashi mutuwar wulakanci. 

A binciken da mukayi akwai abokinshi *Fawwaz Muhammad Sanda* wanda shima d’alibi ne a makarantarsu, bincike ya nuna mana akwai rigima da akayi tsakanin Fawwaz da d’an ajinsu mai suna Farouk, wanda Adnan da Sufwan duk sun san da wannan rigima domin su ukku suke tare abokai ne sosai, kuma bincike ya nuna cewar bayan rigimar Farouk da Fawwaz a ranar aka tsinci gawar Farouk a wajen gari, komenene ya faru alokacin Fawwaz ne zai fad’a mana saboda yasan Naseer, ina neman alfarmar wannan kotu data bada umarnin a kawo Fawwaz Muhammad Sanda domin muji komai daga bakinsa. Nagode. 

Tashin hankali wanda ba’a samasa rana. Gaba d’aya zufa ce ta lullube Alkali da Abban Nabeel, da wani zaije kusa da Alhaji Barau zaiji yanda zuciyarsa take bugawa, jarumta ya tattaro ya kalli Ra’eez, cikin k’arfin hali yace an d’age wannan shari’ar zuwa gobe, kafin nan kotu tana umartar akawo mata Fawwaz Muhammad Sanda zuwa gobe. Kotttt!!!  

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button