ALKALI NE Page 61 to 70

Gaba d’aya kotun ta d’auki hayaniya, Abban Nabeel kuwa kasa tashi yayi daga inda yake, gaba d’aya hankalinsa ya tashi, abinda ya guda shekarun baya gashi zai faru, Allah ya sani tun bayan daya aikata wannan laifin yayi nadama, bayan da Nabeel yazo masa da maganar kuma be sake samun kwanciyar hankali ba, haka kawai yake jin kamar wani abu zai faru ashe kuwa lokacin jin kunyarsu ne yazo.
Cira ido kawai Ummu takeyi saboda gaba d’aya hayaniyar tayi mata yawa, jin kanta tayi yana sara mata. Wasu mutane da suke bayansu taji suna fad’in…. Ai wannan shari’ar da akayi ta shugaban kwastam Alhaji Maiwada a wancan lokacin Brr. Barau ne yayita, gashi kuma yanzu shine Alkali, amma kuma Fawwaz da ake magana ai d’an gidan tsohon Alkali ne, lallai wannan shari’ar akwai lauje cikin nad’i, ga mutuwar Farouk ana magana kuma duk ‘yan makaranta d’aya ne, tabbas za’ayi tone-tone a yanda na fuskanci wannan shari’ar babban al’mari ne.
Zumbur sukaga Ummu ta mik’e, saurin tashi Mama tayi tana kok’arin kamota amma ina tuni Ummu ta zube k’asa yayin da kanta ya bugu da kujera.
Da sauri ma’aikatan da sukazo tare sukayo kanta, hankali tashe Ra’eez ya nufo wajenta, sai dai kafin ya iso Alhaji Mansur yayi saurin rik’eshi yana girgiza mashi kai, dole ya tsaya. Jabeer ne ya jashi sukayi waje.
Haka hankalin mutane yayo kanta, sai dai kafin a taru tuni anyi waje da ita ansata mota sun wuce. Da sauri su Alhaji Mansur sukabi bayansu shida Rafeek.
Share this
[ad_2]